Editor

9513 Posts
NED—Makamin mallakar duniya

NED—Makamin mallakar duniya

Daga AMINA XU Asusun demokuraɗiyya na Amurka wato NED, ‘yan siyasar ƙasar sun yi masa laƙabin “ƙungiya mai zaman kanta dake baiwa sauran ƙasashe taimakon demokuraɗiyya”. Amma a haƙiƙa dai fadar White Housa da ma majalisar dokokin ƙasar na samar masa kuɗi, kuma asusun yana bin umurnin gwamnatin ƙasar wajen jagorantar ƙungiyoyin masu zaman kansu na ƙasa da ƙasa da su yayata manufofin Amurka da hambarar da mulkin ƙasashen ta hanyar samar musu kuɗaɗe. Hakan ya sa ya kasance wani makami mai ƙarfi na Amurka don cin moriyarta da mallakar duniya. Mai zana: Amina Xu
Read More
BBC ta kitsa ƙarairayi kan batun ta’addanci

BBC ta kitsa ƙarairayi kan batun ta’addanci

Daga CMG HAUSA Kwanaki sama da 20 da suka gabata, an kai farmakin ta’addanci kan wata mota ta kwalejin koyon harshen Sinanci, wato Confucius Institute dake jami’ar Karachi dake ƙasar Pakistan, al’amarin da ya haddasa mutuwar wasu malaman ƙasar Sin uku, tare da jikkata wani. Kwamitin tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi Allah wadai da irin wannan farmakin da kakkausar murya. Amma ita kafar yaɗa labaran BBC, ta wallafa wasu rahotanni kwanan nan, inda ta yi yunkurin wanke waɗanda suka kai farmakin daga mummunan laifin da suka aikata. A matsayinta na ɗaya daga cikin kafafen yaɗa labaran ƙasashen yammacin duniya…
Read More
Cikin shekara bakwai, APC ta yi ayyukan da suka gagari PDP

Cikin shekara bakwai, APC ta yi ayyukan da suka gagari PDP

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa jam'iyya mai mulki ta samu nasarori da dama fiye da kowace jam'iyya a Nijeriya a shekara bakwai da ta yi tana mulki. Adamu ya bayyana haka ne a wajen taron ƙaddamar a kwamitin tantance 'yan takarar majalisun jihohi a ranar Talata a Abuja. Shugaban jam'iyyar ta bakin wakilcin mataimakinsa na shiyyar Arewa, Sanata Abubakar Kyari, ya jaddada cewa ba ya kokwanto daukacin 'yan takarar da suka hadu a cibiyar tantancewa za su ci gaba da aiwatar da kyawawan manufofin jam'iyyar. Da yake yi wa 'yan kwamitin…
Read More
’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 30 a hanyar Abuja-Kaduna

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 30 a hanyar Abuja-Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla fasinjoji 30 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Talata. Wannan lamari dai ya zo ne sa'o'i 24 bayan gwamnatin tarayya ta sanar da buɗe hanyar jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna wanda wasu gungun 'yan bindiga suka daƙile shi, inda suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da mutane da dama a watan Maris ɗin 2022. A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar Kula da Jirgin Ƙasa ta Nijeriya (NRC), ta sanar da cewa, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayar da umarnin sake dawo…
Read More
An dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na Zamfara bisa zargin zagon ƙasa ga jam’iyyar

An dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na Zamfara bisa zargin zagon ƙasa ga jam’iyyar

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau An dakatar da shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), reshen jihar Zamfara, Kanar Bala Mande (rtd) bisa zargin zagon ƙasa ga jam’iyyar. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labarai na Jam’iyyar PDP na jihar, Abba Bello kuma aka miƙa wa Blueprint a Gusau ranar Laraba. A cewar sanarwar, jam’iyyar ta ƙalubalanci shugaban jam’iyyar da aka dakatar, Kanar Bala Mande Rtd, kan gudanar da harkokin jam’iyyar ba tare da sa hannun kwamitin ayyuka na jiha ba, da kuma shugabannin jam’iyyar. “Muna sanar da jama’a, da jiga-jigan…
Read More
Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga hukumomin tsaron Nijeriya

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga hukumomin tsaron Nijeriya

Daga NAFI'U SALISU Da Sunan Allah, Mai Rahama Mai Jinƙai. Sanin kowa ne cewa, ƙarfin kowacce ƙasa da tsayuwarta a kan duga-duganta, ya ta’allaƙa ne bisa jajircewa da hoɓɓasa ta jami’an tsaronta, ta fuskar tsayuwa irin ta daga wajen tabbatar da tsaron ƙasa, kare rayukan al’umma da dukiyarsu. Wanda hakan shi ne abinda yake samar da ci gaban ƙasa musamman ta fuskar yaɗuwar arzikin ƙasa da bunƙasa ƙasa ta hanyar haɓaka tattalin arziki. Babu wata ƙasa da za ta cigaba, ta ɗaukaka matuƙar wannan ƙasa ta yi sake tare da riƙon sakainar kashi wajen al’amuran da ya shafi tsaro. Domin…
Read More
Ƙalubalen iyaye kan ‘yan mata masu shaye-shaye

Ƙalubalen iyaye kan ‘yan mata masu shaye-shaye

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa ba baƙon abu ba ne, musamman ma ga 'ya'ya maza, inda ya ke da mamaki da ɗaukar hankali shi ne a ga ’ya mace budurwa, bazawara ko matar aure tana bulayi cikin maye ko a ga tana ɗaga kwalba ana shewa da ita, babu ma dai kamar yarinya ’yar musulma kuma bahaushiya ko ’yar Arewa, da ake kyautata mata zaton ta taso a gidan tarbiyya, kunya da ƙyamatar irin waɗannan halaye marasa kyau. Ba lallai ya zama abin kunya ga matan bariki ko masu zaman kansu da aka fi…
Read More
Sengbe Pieh: Bawan da ya yi wa Turawa tawaye

Sengbe Pieh: Bawan da ya yi wa Turawa tawaye

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A shekara ta 1839 an saci Sengbe Pieh, wani manomi kuma ɗan tireda daga Ƙasar Saliyo a matsayin bawa. Kan hanyar zuwa Amurka ya jagoranci tawaye a cikin jirgin ruwan jigilarsu, abin da ya kawo ƙarshen cinikin bayi a Amurka. Babu dai takamaimen lokacin da ake iya cewa shi ne lokaci da aka haifi Sengbe Pieh, sai dai masana tarihi sun yi ittifaƙin cewa, an haife shi ne a shekarar 1814 a ƙasar da a yanzu ake kira Saliyo. An yi imanin cewa, an haife shi a wani tsibiri da ke gundumar Bonthe, wajen da ya…
Read More
Maza masu duka da wulaƙanta matansu sam ba su da laifi!

Maza masu duka da wulaƙanta matansu sam ba su da laifi!

Daga AMINA YUSUF ALI Barkan mu da sake haɗuwa a wani makon a filinmu mai albarka, Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja.  Da farko dai shi duka a zaman aure da maza suke yi wa mata abu ne a al'adance da ddinance ma bai kamata ba, kuma abu ne da yake ci wa mata tuwo a ƙwarya. Duk da dai shi duka a gidan aure ba Hausawa suka fi yinsa ba. Wasu ƙabilun na Nijeriya sun fi yinsa. Sai dai shi ma Bahaushe yana nema ya ara ya yafa.  Abin tambaya, me yake jawo duka a zaman…
Read More
Matasa a siyasa

Matasa a siyasa

Daga MARYAM BATOOL Ita dai siyasa tana nufin haɗa yarjejeniya tsakanin mutane, domin su zauna tare duk da mabambantan ra’ayoyinsu, ƙabilu da addinai a birane da ƙasashe. A manyan ƙasashe mutane da dama kan dauki dogon lokaci wajen tsayar da yarjejeniyar siyasa. Waɗannan mutane su ake kira da ‘yan siyasa. ‘Yan siyasa da kuma ragowar Al’umma sukan haɗu don samar da gwamnati da tafiyar da ita. Kafin kafuwar sabuwar gwamnati akwai wasu ƙa’idoji da ake bi domin samun tsayayyun shugabanni nagari. Al’umma ƙasa da garuruwa sukan haɗu gabaɗaya domin zabar wanda suke so bayan jam’iyoyi sun fitar da ‘yan takarar…
Read More