Editor

9513 Posts
Sanarwar ministocin ƙungiyar G7 ta keta ƙa’idar ƙasa da ƙasa ce dake neman rura wutar rikici

Sanarwar ministocin ƙungiyar G7 ta keta ƙa’idar ƙasa da ƙasa ce dake neman rura wutar rikici

Daga FAEZA MUSTAPHA A baya-bayan nan ne, ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar G7 suka fitar da wata sanarwa bayan taron da suka yi, inda a cikinta suka bayyana wasu buƙatu ga ƙasar Sin, waɗanda suka yi su bisa son zuciya da zarge-zarge marasa tushe, da gazawa wajen mutunta cikakken ’yancin kan ƙasar. Cikin sanarwar, sun ce sun damu da yanayin kwanciyar hankali a tsibirin Taiwan. Amma sam ƙasashen yamma ba su damu da hakan kamar yadda suke furtawa ba. Sanin kansu ne cewa, zaman lafiyar yankin ya dogara ne da janyewarsu daga yi wa harkokin gidan Sin katsalandan da kuma…
Read More
An cimma nasarar kawar da ƙwayoyin cutar COVID-19 baki ɗaya a ƙananan hukumomi 16 na birnin Shanghai

An cimma nasarar kawar da ƙwayoyin cutar COVID-19 baki ɗaya a ƙananan hukumomi 16 na birnin Shanghai

Daga CMG HAUSA A yayin taron ganawa da manema labarai game da aikin kandagarkin annobar COVID-19 da aka shirya yau Talata da safe, an bayyana cewa, a halin yanzu, an cimma nasarar kawar da ƙwayoyin cutar COVID-19 baki ɗaya a yankunan ƙananan hukumomi 16 dake birnin Shanghai na ƙasar Sin. A jiya Litinin 16 ga wata, an tabbatar da sabbin mutane 77 da suka kamu da cutar, sannan wasu mutane 746 da suka kamu da cutar, amma ba tare da nuna alamun cutar ba a birnin Shanghai. Kuma, dukkansu suna zaune ne a cikin yankunan da aka kilace. Bugu da…
Read More
Wa zai yarda Amurka ta goyi bayan yankin Taiwan don halartar babban taron lafiya na duniya?

Wa zai yarda Amurka ta goyi bayan yankin Taiwan don halartar babban taron lafiya na duniya?

Daga CMG HAUSA A gabannin babban taron ƙasa da ƙasa kan harkokin kiwon lafiya karo na 75, wasu ‘yan siyasar Amurka sun sake ƙulla makirci, na nunawa yankin Taiwan goyon baya don halartar taron. Kwanan nan ne, shugaban Amurka ya sa hannu kan wani shirin doka, inda ya buƙaci sakataren harkokin wajen ƙasar, da ya taimaki yankin Taiwan, don sake dawo da matsayinsa na dan kallo a hukumar WHO, ta yadda zai samu damar halartar taron. Irin wannan abu, shisshigi ne da aka yi cikin harkokin cikin gidan ƙasar Sin, wanda kuma ya sabawa babbar manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya…
Read More
2023: Sarkin Illori ya juya baya ga Saraki, ya yi mubaya’a ga Tinubu

2023: Sarkin Illori ya juya baya ga Saraki, ya yi mubaya’a ga Tinubu

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Litinin ne dai Sarkin Illori Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana mubaya'arsa ga ɗan takarar shugabancin Nijeriya a APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Basaraken ya bayyana haka ne yayin amsar baƙuncin mambobin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Tinubu mai suna, South West Agenda for Asiwaju 2023 a fadarsa dake Ilorin. Inda ya bayyana cewa: "Tinubu ya cancanci zama shugaban ƙasar Nijeriya na gaba". Amma abinda ya fi ɗaukar hankali ga wannan mubaya'a da basaraken ya yi ga Tinubu shi ne mubaya'ar ta zo ne a dai-dai lokacin da ɗan asalin jiharsa kuma Mariƙin ɗaya daga cikin…
Read More
Ku manta baya mu haɗa kai – Gidan Dabino ga ’yan Kannywood

Ku manta baya mu haɗa kai – Gidan Dabino ga ’yan Kannywood

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Sabon shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) reshen Jihar Kano, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), ya ce, duk da rigingimu da Kannywood ta ke ciki zai yi iya yinsa ya ga ya ɗinke duk wata ɓaraka a matsayinsa na shugaba. Ya ce, "Wannan masana’anta da muka gina ta tun da jajayen sawunmu (mu na matasa) yau sama da shekaru 25, ya zama wajibi a gare mu da sauran ‘yan uwa da muke ta faɗi-tashi don ganin kada wannan masana’anta ta wargaje, mu haɗa hannu don mu daɗa samar mata da inganci…
Read More
BIDIYO: Tashin bom a Kano

BIDIYO: Tashin bom a Kano

Mazauna yankin Sabon Gari a birnin Kano sun kiɗeme sakamakon tashin bom da ya auku a yankin a safiyar Talata. Yazuwa wallafa wannan bidiyon ba a tantance adadin mutanen da fashewar ta rutsa da su ba.
Read More
Harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna: Mahara sun sako mai juna-biyu

Harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna: Mahara sun sako mai juna-biyu

Daga BASHIR ISAH 'yan bindiga sun sako wata mata mai juna-biyu tare da wasu daga mutanen da suka yi garkuwa da su a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna wanda ya auku lokutana baya. Manhaja ta gano cewa maharan sun sako matar ne bisa ganin damarsu. Hoton bidiyon matar da lamarin ya shafa ya yi ta karakaina a soshiyal midiya inda aka ga matar sanye baƙin hijabi da baƙin abin rufe baki da hanci. Tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da daidaita da maharan domin a sakon ragowar mutanen da ke hannunsu. Ta ce lamarin abin damuwa ne matuƙa saboda…
Read More
Almundahana: Akanta-Janar, Ahmed Idris ya faɗa a komar EFCC

Almundahana: Akanta-Janar, Ahmed Idris ya faɗa a komar EFCC

Daga BASHIR ISAH Hukumar EFCC ta cika hannu da Akanta-Janar na Ƙasa, Ahmed Idris bisa zargin almundahana da karkatar da biliyan N80 mallakar gwamnati. Majiyarmu ta nuna Idris ya faɗa a komar jami'an EFCC ne da yammacin Litinin a Kano sannan suka ɗauke shi zuwa Abuja don ya amsa musu tambayoyi. Majiyar ta ce kafin wannan lokaci da ma EFCC na bincike kan batun karkatar da biliyan N80 mallakar gwamnati da aka zargi Idris da aikatawa ta hanyar amfani da wasu kwantiragi. Sakamakon bincike ya nuna kamfanonin da aka yi amfani da su wajen aiwatar da kwantiragin na da nasaba…
Read More
Bayan wani mahaukacin ɗan bindiga sai mahaukaciyar ƙasa

Bayan wani mahaukacin ɗan bindiga sai mahaukaciyar ƙasa

Daga CMG HAUSA A yayin da mutane suka je kasuwa don sayen kayayyaki a ƙarshen mako, ba su san hawa ba balle sauke, sai kawai aka harbe su da bindiga. Wannan harin da ya abku ba gaira ba dalili shi ne abin da ake kira “hauka”. Wani saurayi farar fata mai shekaru 18 a duniya ne, ya ƙaddamar da wannan hari a ranar Asabar da ta wuce, a wata kasuwar zamani dake garin Buffalo na jihar New York ta ƙasar Amurka. Inda ya rika watsa hotunan bidiyon yadda yake kashe mutane kai tsaye a shafin yanar gizo. Cikin ‘yan mintuna…
Read More
Idan amarya ba ta hau doki ba, bai kamata a ɗora mata kaya ba

Idan amarya ba ta hau doki ba, bai kamata a ɗora mata kaya ba

Daga AHMAD FAGAM Ko shakka babu, duniyar bil adama tana fama da tarin ƙalubaloli waɗanda ke zama barazana ga zaman lafiya, da tsaro, da walwala, har ma da ci gaban duniyarmu baki ɗaya. Musamman idan muka yi la’akari da yadda duniyarmu ke fuskantar tarin matsaloli, kamar matsalar karayar tattalin arzkin sassa daban-daban na duniya, da matsalar sauyin yanayi wanda ke kara jefa rayuwar dan adam da sauran halittu gami da shi kansa muhallin halittun cikin garari, ga kuma matsalar annobar COVID-19 da ake fama da ita, sannan uwa uba ga matsalar yawaitar tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na duniya. Sai…
Read More