14
May
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a inuwar Jam’iyyar PDP, Hon. Isah Ashiru Kudan, ya bayyana cewa babban abin da zai fi maida hankali a kai idan ya zama Gwamnan Kaduna shi ne magance matsalar tsaro a jihar. Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya ƙaddamar da kwamitin kamfen ɗin sa a garin Kaduna, Ashiru ya ce dalilin matsalar rashin tsaro da rarrabuwar kai a Jihar Kaduna ya sa an samu koma baya a wajen cigaba da raya jihar. ”Ina da ƙwarewa a harkar sanin yadda ake hulɗa da jama’a da kuma…
