13
May
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Abdulmalik Tanko, malamin makarantar da a ke zargi da kashe Hanifa Abubakar, ya ce shi da sauran mutane biyu da ake tuhuma ba su san yadda a ka yi yarinyar 'yar shekara 5 da haihuwa ta rasu ba. Tanko ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin da yake kare kansa a gaban babbar kotu a Jihar Kano. Ana tuhumar Tanko mai shekara 34 tare da Hashimu ɗan shekara 37 da kuma Fatima Musa mai shekara 26, dukkan su mazauna Tudun Murtala a gaban babbar kotun. Ana tuhumar su da laifuka 5 da suka haɗa…
