Editor

9513 Posts
Najeriya ce ta 8 a jerin ƙasashen da ake sayar da fetur da arha – Bincike

Najeriya ce ta 8 a jerin ƙasashen da ake sayar da fetur da arha – Bincike

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai farashin fetur a ƙasashe da dama na Duniya na yin tashin gwauron zabon da bai tava yi ba. Hakan na faruwa ne saboda rashin samun shi a wadace da ba a yi yanzu a Duniya. Jaridar Premium Times ta rawaito cewa, wani sabon rahoto da wani kamfanin binciken ƙwaƙwaf mai suna Zutobi ya fitar, ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta 8 a jerin ƙasashen da har yanzu ake sayen litar fetur arha. An dai buga wannan bincike a cikin watan Afrilu, inda farashin galan 1 ke daidai da dala 1.82. Ƙasashen…
Read More
Ceto kamfanonin jiragen sama daga rugujewa

Ceto kamfanonin jiragen sama daga rugujewa

Kamfanonin jiragen sama na Nijeriya sun fitar da wata sanarwar cewa, daga ranar Litinin 9 ga Mayu, 2022, za su rufe ayyukansu, saboda tsadar man jiragen da ake sayarwa akan Naira 700 kan kowace lita. Wata sanarwa da aka fitar tare da sanya hannun dukkan shugabannin jiragen a ƙarshen makon da ya gabata, ta shawarci jama’a masu tafiya da ke da niyyar tashi da su yi wasu shirye-shirye na daban, don guje wa maƙalewa a tashoshin jiragen saman ƙasar. A cewar ma’aikatan, bayan lokaci, farashin man jiragen sama (JetA1) ya tashi daga Naira 190 kan kowace lita zuwa Naira 700…
Read More
Sheikh Abduljabbar ya sake sallamar lauyoyinsa a Kotu

Sheikh Abduljabbar ya sake sallamar lauyoyinsa a Kotu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Malamin addinin Musuluncin nan da ke Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, ya sake sallamar lauyoynsa a karo na uku.  A zaman da kotun shari'a da ke Ƙofar Kudu a ƙarƙashin jagorancin, Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola, wanda ake ƙara bai bayyana da lauyoyinsa ba.   A zaman na jiya Alhamis, jagoran lauyoyin gwamnati, Nasiru Adamu Aliyu (SAN), ya bayyana da abokan aikinsa 13, yayin da aka ga jagoran lauyoyin wanda ake ƙara, A.O Muhammad (SAN), ya aiko da wasiƙar cire kansa daga cikin shari'ar.  Gwamnatin Kano na zargin Sheikh Abduljabbar ne da laifin yin kalaman ɓatanci…
Read More
Ina ma dai Malam Shekarau zai yi haka..!

Ina ma dai Malam Shekarau zai yi haka..!

Kowa ya san siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, siyasa ce mai dabaibaye da addini da tarbiyya. Don haka ma da dama al’umma ke kallon Malam Shekarau da ƙima kuma suke girmama ra’ayinsa, sannan suke bin sa ba don kuɗi ko mulki ba, sai don aƙida. Hatta lokacin da mulki ya suɓuce a hannunsa, akwai ’yan amanarsa da dama da suka cigaba da wannan azumin na rashin gwamnati, ba su bi wani ba, sun zauna da shi a yanayin akwai da babu. Dawowar Malam Ibrahim Shekarau cikin jam’iyyar APC bayan ya bar PDP, wacce ya yi iƙirarin rashin…
Read More
An ƙone matashiyar da ake zargi da ɓatanci ga Annabi a Sakkwato

An ƙone matashiyar da ake zargi da ɓatanci ga Annabi a Sakkwato

-A kai zuciya nesa, cewar Majalisar Sarkin Musulmi-Mun rufe kwalejin har illa masha Allahu – Gwamnati-’Yan sanda sun kama mutum biyu Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Matasa sun ƙone wata matashiya da ake zargi da yin ɓatanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (SAW), a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, lamarin da ya tilasta wa gwamnati rufe kwalejin ba tare da bayyana ranar da za a koma karatu ba. Ɗaruruwan ɗalibai da wasu mata sun gudanar da zanga-zanga tare da ciro wacce ake zargin daga maɓoyar da hukumomin makaranta suka ɓoye ta, inda suka kashe tare da ƙone…
Read More
Ba kare bin damo: Rundunar soja ta kammala biyan haƙƙin tsoffin sojoji

Ba kare bin damo: Rundunar soja ta kammala biyan haƙƙin tsoffin sojoji

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar sojojin Nijeriya ta biya dukkan haƙƙoƙin tsofaffin jami’anta da kuma na magadan sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki.  Hukumar kula da fanshon sojoji (MPB) ta kammala biyan ƙarin mafi ƙarancin albashi da kuma basussukan albashi ga tsaffin ma'aikatan da suka cancanta, wanda aka fara tun ranar 6 ga Mayu, 2022, wanda aka kammala a ranar 10 ga Mayu, 2022. Hakazalika, hukumar ta iya dukkan iyalan mamatan sojojin waɗanda suke bin bashin haƙƙoƙinsu su ma an biya su, ba sa bin ko sisi.  Don haka, hukumar fanshon sojojin ta cika alƙawuran da ta ɗaukar…
Read More
Kano ta Tsakiya: Ni na sa kaina sayen fom, ba Ganduje ba – Sanata Lado

Kano ta Tsakiya: Ni na sa kaina sayen fom, ba Ganduje ba – Sanata Lado

"Na shiga halin ɗimuwa a lokacin da na karanta wani labari a jaridun politicsdigest.ng da alfijir.com.ng da wasu kafafen yaɗa labarai wanda aka wallafa a ranar 9 ga watan Mayun shekarar 2022. A cikin labaran an rawaito Malam Ibrahim Shekarau ya ce: Mai girma Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ba ni umarnin tsayawa takarar Sanata na yankin Kano ta tsakiya. Duk da dai ban fiye fitowa fili na yi ce-ce-ku-ce a harkar siyasa ba, kuma na so na kama bakina na yi shiru don kare mutuncina, amma gudun kada shirun nawa ya sa wasu su zaci labarin gaskiya ne,…
Read More
Nijeriya ta kasa ɗaukar mataki watanni shida bayan rahoton zanga-zangar ENDSARS – HRW

Nijeriya ta kasa ɗaukar mataki watanni shida bayan rahoton zanga-zangar ENDSARS – HRW

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Rights Watch ta zargi hukumomin Nijeriya da ƙin ɗaukar matakin tabbatar da adalci ga masu zanga-zangar neman kawo ƙarshen zaluncin 'yan sanda wato #ENDSARS, a Jihar Legas a 2020, bayan wata shida da kwamitin binciken da aka kafa ya zargi jami'an tsaro da cin zarafin mutane a lokacin. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Litinin, ta buƙaci gwamnati da ta aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar a ɗauka a kan waɗanda aka zarga da aikata laifi. Ƙungiyar ta ce, ba zai yiwu a kawar…
Read More
Iyalan waɗanda aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yi zanga-zanga

Iyalan waɗanda aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yi zanga-zanga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Iyalan waɗanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga Maris, 2022 sun gudanar da zanga-zangar nuna damuwa da kuma kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi ƙoƙarin kuɓutar da iyalan nasu daga hannun 'yan ta'addar. Iyalan na cikin damuwa sosai kan kasa ceto 'yan uwan nasu.'Yan uwa da iyalan waɗanda aka sace a jirgin ƙasan sun yi zanga-zangar lumana a titunan Kaduna ranar Litinin domin nuna damuwarsu kan rashin ceto ko sakin waɗanda aka sacen. Haka kuma a Abuja ma babban birnin Nijeriya, wasu iyalai da…
Read More