Editor

9513 Posts
2023: APC ta ƙaddamar da kwamitocin tantance ’yan takara

2023: APC ta ƙaddamar da kwamitocin tantance ’yan takara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar APC za ta ƙaddamar da kwamitocin tantance ’yan takarar majalisar wakilai, dattijai da na gwamnoni da ta tantance a yau da ƙarfe 12 na rana. An bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren jam'iyyar na ƙasa, Sulaiman Argungu ya fitar. A cewar Argungu, za a ƙaddamar da kwamitin tantancewar ne a Fraser Suites, Abuja. Ya kuma bayyana cewa, daga nan ne za a fara tantance masu neman kujerar gwamna, majalisar wakilai da kuma ’yan majalisar dattawa. Argungu ya ce, za a gudanar da tantance ’yan takarar majalisar wakilai a ranar Asabar 14 ga Mayu,…
Read More
Hanyar da ASUU za ta gamsar da ɗalibai

Hanyar da ASUU za ta gamsar da ɗalibai

A duk lokacin da ƙungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki takan yi iƙirari ne da yanayin jami'o'i da kuma ɗaliban cikinsu. Haƙiƙa da yawa daga cikin ɗalibai sun rasa irin wannan kishi da ƙungiyar ASUU take yi musu. Sau da yawa wasu ɗalibai masu gajeren zangon tunani iri na, na kallon rigimar ASUU da gwamnati a matsayin rigima ce kawai irin ta 'ya'yan turaka, domin duk daga kwasfo ɗaya suka fito, rigima ce tsakanin masu wukar yanka da masu aska kawai. Sanin kowa ne a wannan ƙasa, farfesoshi ne ke yin aikin 'returning officers' na kafa irin waɗannan shugabannin da…
Read More
Birtaniya ta burge Nijeriya

Birtaniya ta burge Nijeriya

Ƙasar Birtaniya wacce ita ce ta raini Nijeriya har zuwa lokacin samun ’yancin kai a shekara ta 1960 ta faranta ma duk wani ɗan ƙasa na ƙwarai rai bisa ayyana ƙungiyar 'yan ta'adda ta IPOB a matsayin 'yan ta'adda. Kamar yadda tashar radiyon BBC Hausa ta yi hira da mai magana da umurnin shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ya yi ƙarin haske da nuna farin cikin gwamnatin ƙasarmu cewa ƙasar Birtaniya ta yi abin ƙwarai ganin yadda IPOB ta zamo annoba. Muna fatan ƙasashe kamar Amurka ita ma ta biyo bayan ƙasar Birtaniya wajen haramta waccen ƙungiya ta 'yan ina…
Read More
Ƙasashen BRICS sun yi kira a haɗa kai don tinkarar sauyin yanayi

Ƙasashen BRICS sun yi kira a haɗa kai don tinkarar sauyin yanayi

Daga CMG HAUSA Kwanan nan ne aka gudanar da babban taron ƙasashen BRICS kan tinkarar sauyin yanayi ta kafar bidiyo, inda aka yi kiran a hada kai don tinkarar matsalar sauyin yanayi, da tattaunawa kan gaggauta rage fitar da iskar dake gurbata muhalli, da lalubo hanyar samun farfaɗowa mai ɗorewa da daidaito da nuna haƙuri. Ministan kula da muhallin halittun ƙasar Sin, Huang Runqiu ya gabatar da jawabin dake cewa, ta hanyar shirya babban taron ƙasashen BRICS kan tinkarar sauyin yanayi, ƙasar Sin na fatan yin ƙoƙari tare da kasashen BRICS, don tabbatar da aiwatar da ra’ayin kasancewar bangrori daban-daban…
Read More
Amurka ba ta cimma burinta a Asiya ba

Amurka ba ta cimma burinta a Asiya ba

Daga CMG HAUSA Ranar 13 ga wata, aka rufe taron koli na musamman tsakanin ƙasar Amurka da ƙasashe mambobin ƙungiyar ASEAN a birnin Washington, babban birnin ƙasar, wanda aka dakatar da kira a baya. Sai dai babu wani abu takamaimai cikin sanarwar haɗin gwiwa da aka bayar bayan rufe taron. Manazarta sun yi nuni da cewa, lamarin bai wuce zaton mutane ba, wato Amurka ta yi shelar ƙara yin abota da ƙasashen Asiya, amma haƙiƙa dai tana yunƙurin haɗa hannu ne da waɗanda ke adawa da ƙasar Sin. Kafofin yada labaru na ƙasashen duniya sun lura da cewa, Amurka ta…
Read More
Ya kamata Sin da Amurka su ƙara haɗin gwiwa a fannin aikin noma

Ya kamata Sin da Amurka su ƙara haɗin gwiwa a fannin aikin noma

Daga CMG HAUSA An gudanar da taron tattauna bunkasa aikin noma da yankunan karkara tsakanin ƙasashen Sin da Amurka ta yanar gizo a baya bayan nan, wanda kwalejin ilmin bunkasa ƙasa da ƙasa da aikin noma ta duniya, ta jami’ar ilmin aikin noma ta ƙasar Sin ta ɗauki baƙuncinsa. Mahalartar taron na ganin cewa, ya kamata Sin da Amurka su ƙara hadin gwiwa a fannin aikin noma, suna cewa, hakan zai amfanawa ƙasashen biyu, har ma da samar da gudummawa ga tabbatar da wadatar hatsi a duniya. Bisa ƙididdigar da aka yi, yawan kuɗin cinikin aikin noma da aka samu…
Read More
Babban titin da Sin ta gina zai bunƙasa ɓangaren yawon buɗe ido a Kenya

Babban titin da Sin ta gina zai bunƙasa ɓangaren yawon buɗe ido a Kenya

Daga CMG HAUSA Ana sa ran babban titin da ƙasar Sin ta gina a ƙasar Kenya, zai bunƙasa ɓangaren yawon bude ido na ƙasar.Sakataren ma’aikatar kula da yawon buɗe ido da namun daji na ƙasar, Najib Balala ne ya sanar da hakan ga manema labarai a birnin Nairobi, babban birnin ƙasar, yana mai cewa, ana sa ran motoci za su fara gwada titin daga ran Asabar. Ya ƙara da cewa, wannan wata makoma ce mai haske ga ɓangaren yawon buɗe ido na kasar, saboda ana sa ran babban titin na Nairobi zai rage lokacin da ake ɗauka daga filin jirgin…
Read More
Kawo ƙarshen cutar maleriya a Afirka

Kawo ƙarshen cutar maleriya a Afirka

A duk shekara ɗaruruwa dubbai na yara ne ke mutuwa sakamakon zazzaɓin cizon. Sai dai yanzu wata allurar riga-kafin maleriya da aka yi gwajinta a Afirka ta ba da sakamako mai ƙarfafa gwiwa. Sama da mutane dubu 400 zazzaɓin cizon sauro ya yi ajalinsu a shekarar 2019. Sakamakon sabuwar allurar riga-kafin da aka wallafa a mujallar kimiyya ta The Lancet, kuma yanzu haka ake jiran a sake yin bincike kanta, ya nuna cewa riga-kafin samfurin R21/Matrix-M na da ingancin kashi 77 cikin 100, bayan an shafe wata 12 ana gwajinsa. Hakan ya dace da mizanin Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO,…
Read More
Ko kamfanin NNPC zai iya magance matsalar tsadar mai a Nijeriya?

Ko kamfanin NNPC zai iya magance matsalar tsadar mai a Nijeriya?

Shugaban babban kamfanin man fetur na Nijeriya tare da na babban bankin ƙasar sun bayyana wa majalisar dokokin ƙasar da kuma kamfanonin jiragen sama cewar ba za su iya ba da tabbacin magance matsalar tashin farashin man jiragen da aka fuskanta a ƙasar ba. kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya nuna amannar sa wajen samar da Man jirage ga 'yan kasuwa waɗanda kamfanonin sufurin jiragen saman Nijeriya wato AON suka aminta a baiwa. Sannan ƙungiyar za ta miƙa buƙatar ta, ta neman lasisin shigo da man daga ƙasashen waje, a cewar kakakin majalisar wakilan ƙasar Femi Gbajamiala. A yayin…
Read More
Jamhuriyar Afirka ta tsakiya (CAR) ta mayar da Bitkoyin kuɗin ƙasarta

Jamhuriyar Afirka ta tsakiya (CAR) ta mayar da Bitkoyin kuɗin ƙasarta

Daga AMINA YUSUF ALI Jamhuriyar mulki ta Afirka ta tsakiya (CAR) ita ma ta bi sahun El Salvador wajen mayar da Bitkoyin a matsayin kuɗinta na ƙasa. Jaridar Sierra Leone Telegraph ta bayyana cewa, Afirka ta Tsakiya wacce a kwanakin baya yaƙi ya yi wa raga-raga da ita, ta ƙaddamar da Bitkoyin a matsayin kuɗin ƙasarta na halaliya wanda za a iya yin dukkan wata hada-hadar ta kuɗi, kamar cinikayya, ko harkar banki da sauransu. Sai dai wannan mataki da ƙasar ta ɗauka ya jawo mata cece-ku ce, domin ana zargin ƙasar ta yi gaban kanta ne ba tare da…
Read More