Ko kamfanin NNPC zai iya magance matsalar tsadar mai a Nijeriya?

Shugaban babban kamfanin man fetur na Nijeriya tare da na babban bankin ƙasar sun bayyana wa majalisar dokokin ƙasar da kuma kamfanonin jiragen sama cewar ba za su iya ba da tabbacin magance matsalar tashin farashin man jiragen da aka fuskanta a ƙasar ba.

kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya nuna amannar sa wajen samar da Man jirage ga ‘yan kasuwa waɗanda kamfanonin sufurin jiragen saman Nijeriya wato AON suka aminta a baiwa.

Sannan ƙungiyar za ta miƙa buƙatar ta, ta neman lasisin shigo da man daga ƙasashen waje, a cewar kakakin majalisar wakilan ƙasar Femi Gbajamiala.

A yayin da babban jami’in kamfanin man fetur (NNPC), Mele Kyari ya bayyana cewar baza su iya magance matsalar tsadar farashin man fetur ɗin ba, hanya kaɗai da zasu bi wajen samar da sassaucin ita ce a sanya tallafi.

Sannan shugaban Babban bankin na Nijariya Godwin Emefiel wanda ke ƙoƙarin tsaya wa takarar neman shugabancin ƙasar shi ma ya ƙara da cewa, ba zai iya ba wa kamfanonin sufurin jiragen saman tsayayyen farashi bisa musayar kuɗaɗen ƙasashen waje da zai taimaka wajen shigo da man daga ƙasashen ƙetare ba.

Shugaban babban bankin ya cigaba da cewar indai har kamfanonin na da buƙatar hakan, to za su tuntuɓi bankunan ƙasar dangane da yiwuwar magance matsalar.

Za mu iya cewa, wannan matsalar dai ba a san ranar magance ta ba.

Daga AHMAD MUSA, 09070905293.