Editor

9513 Posts
Amurka na cin riba, yaya kuma ƙasashen Afirka?

Amurka na cin riba, yaya kuma ƙasashen Afirka?

Daga CMG HAUSA Shugaban bankin raya Afirka na AfDB Akinwunmi Adesina, wanda tsohon ministan noma ne a Najeriya, a yayin zantawarsa da shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari a kwanan baya, ya ce rikicin Rasha da Ukraine, ya haddasa hauhawar farashin alkama da kusan kaso 60 bisa ɗari a ƙasashen nahiyar Afirka. Adesina ya ƙara da cewa, tashin hankalin ya haifarwa duniya tarin ƙalubale, musamman ma ƙasashen Afirka, masu shigo da kaso mai yawa na abincin da suke buƙata daga ƙasashen biyu. Abin haka yake, daidai kamar yadda Adesina ya ce, ɓarkewar rikici a tsakanin Rasha da Ukraine ya haddasa hauhawar…
Read More
Zhao Lijian: Amurka ta ƙware wajen kitsa ƙarairayi

Zhao Lijian: Amurka ta ƙware wajen kitsa ƙarairayi

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya musanta zargin da Amurka ta yi, cewa wai Sin na taimakawa ƙasar Rasha a fannin yaɗa bayanan bogi, yana mai cewa, irin waɗannan kalamai na Amurka, manyan ƙarairayi ne da ƙasar ke yaɗawa duniya, wanda hakan ya dada tabbatar da Amurka a matsayin wadda ta yi matuƙar ƙwarewa wajen kitsa kalaman bogi. Zhao Lijian ya kuma ce Sin na kan bakan ta, na kin amincewa da matakin Amurka, na fakewa da batun kare haƙƙin bil adama, da amfani da ƙarfin gwamnati wajen yiwa kamfanonin Sin…
Read More
Waƙa: UBANGIJINMU ALLAH (T)

Waƙa: UBANGIJINMU ALLAH (T)

Tare da ABDULHAMID Na MATAZU Da Sunan Allah na Mai Girma,Baitochi ne Zan Tsara ma.Mabuwayi Kuma Gagara Gasa,WANZAJJE tun Kan Kowa Ma.Bai Haifa Ba Ba a Haifai Ba,bai da KINI Allah mai 'AMA.Shi ne yake Da Mulkin Sammai,har ƙassai Shi sarkin Girma.Shi ne Muke Nufa Da Buƙata,duk kuma Shi ne zai yaye ma.Allah Shi ke Ba mu ISASSA,Shi ke Kawo Har MARDHUN ma.Sai dai duk CUTAR da Dawa'i,in Yaga Dama Yayyaye ma.Jallah Ya Ba mu Abincin cin mu,dats tsuntsaye Dabbobi ma.Shi yai ZAKI shi yai KURA,CINNAKA sauro Da Kunama.Mai ƊACI bauri Daz ZAQI,Har Hamami Tuni na Sallamma.Shi ya Kamata Ayi…
Read More
Tasirin azumi a jikin ɗan adam (4)

Tasirin azumi a jikin ɗan adam (4)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu, assalamu alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, mai ilmintarwa da qayatarwa na Jikin Ɗan Adam, wanda ke kawo muku bayanai game da duniyar jikin bil’adama, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, ku san yadda jikinku ke aiki a jaridarku ta Blueprint Manhaja mai farin jini.  Barkanmu da wannan lokaci na azumin watan Ramadan; fatan Allah ya karɓi ibadunmu, Aameen. Azumi ya kawo gangara; babu mamaki wannan ne rubutuna na ƙarshe game da tasirin azumi a jikin ɗan adam, sai kuma idan Mai…
Read More
Yadda ƙalubalen satar fasaha ke barazana ga cigaban adabi

Yadda ƙalubalen satar fasaha ke barazana ga cigaban adabi

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Hauwa Salisu, da ake yi wa laƙabi da Haupha, marubuciya ce daga Jihar Kaduna, yayin da ta fara aikin wani littafin ta mai suna 'Da Aurena' ba ta taɓa tunanin rubutun zai iya fuskantar tangarɗa ba, ganin irin yadda masu karatu suka karɓi littafin, saboda da salo na jan hankali da ta yi amfani da shi. Kwatsam, ran nan sai wata marubuciya daga ƙungiyarsu ta Kainuwa ta sanar da ita cewa ana ɗora labarin ta a wani zaure da ke manhajar Facebook, amma ba tare da sunan littafin ba kuma ba da irin bangon da ta…
Read More
Buhari ya karɓi baƙuncin Guterres a fadarsa

Buhari ya karɓi baƙuncin Guterres a fadarsa

Daga BASHIR ISAH A ranar Laraba Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Bayanai daga Fadar sun nuna Buhari ya yi ganawar sirri tare da baƙon nasa inda suka tattauna batutuwa da suka shafi Nijeriya, Afirka da sauransu. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Guterres ya zo ziyarar aiki ne na kwana biyu a Nijeriya, inda a ranar Talata ya ziyarci Maiduguri babban birnin Jihar Borno ya gana da waɗanda rikicin ta'addanci ya shafa da kuma mayaƙan Boko Harama da suka ajiye makaminsu.…
Read More
Musulmai a Jihar Xinjiang sun yi bikin ƙaramar Sallah

Musulmai a Jihar Xinjiang sun yi bikin ƙaramar Sallah

Daga CMG Hausa Musulmai a jihar Xinjiang ta ƙasar Sin, sun gudanar da shagulgula daban daban na bikin ƙaramar Sallah a jiya Laraba. Wasu musulmai a birnin Urumqi, sun gudanar da sallar idi ne a masallacin Yangxing mai tarihin sama da shekaru 120, ƙarƙashin matakan kariya da daƙile yaɗuwar annobar COVID-19. A harabar masallacin Etigar dake Kashigar kuwa, mazauna na ƙabilu daban-daban ne suka yi kwalliya tare da gudanar da shagulgulan bikin ranar Sallar. Ranar Sallah, rana ce da iyalai a jihar Xinjiang ke ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki, inda suke haɗuwa su yi ciye-ciyen nau’ikan abinci don murnar…
Read More
Ofishin jakadancin dake Amurka ya ƙaryata kalaman Dda Amurka ta yi kan rikicin Rasha da Ukraine

Ofishin jakadancin dake Amurka ya ƙaryata kalaman Dda Amurka ta yi kan rikicin Rasha da Ukraine

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ofishin jakadancin ƙasar Sin dake ƙasar Amurka, ya mayar da martani kan tambayoyin da manema labaru suka yi jiya Talata, inda ya musanta bayanin da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi a ranar Litinin 2 ga wata cewa, wai jami'ai da kafofin watsa labaru na ƙasar Sin suna yada farfaganda da bayanan ƙarya na Rasha, a yayin rikici tsakanin ƙasashen Rasha da Ukraine. Kakakin ya ce, matsayin ƙasar Sin kan batun Ukraine yana bisa gaskiya da adalci, kuma babu wani abin zargi a ciki. Idan ana batun yada bayanan ƙarya ne, ya kamata…
Read More
Masana kimiyyar Sin sun isa ƙolin tsaunin Qomolangma

Masana kimiyyar Sin sun isa ƙolin tsaunin Qomolangma

Daga CMG HAUSA Tawagar masana kimiyya na ƙasar Sin ta “yanayin duniya na shekarar 2022”, ta yi nasarar hawa tsaunin Qomolangma mai tsawon mita 8,848 a yau Laraba, inda kashi na farko na tawagar ta isa ƙolin da misalin karfe 12:22 na rana, yayin da sauran suka cim musu bayan awa guda. Mambobi 13 na tawagar da suka tashi da safiyar yau ne suka fara haye mita 8,000, inda 5 daga cikinsu suka kafa cibiyar tantance yanayi mai sarrafa kanta mafi tsawo a duniya da misalin ƙarfe 11:11 na safiya, a kan yankin iyakar Sin da Nepal mai tsawon mita…
Read More
Labarin likitocin Beijing da suka samar da agajin jinya ga mutanen Afirka

Labarin likitocin Beijing da suka samar da agajin jinya ga mutanen Afirka

Daga MURTALA ZHANG Tun shekaru sama da 50 da suka gabata har ya zuwa yanzu Ƙasar Sin take aiwatar da ra’ayin gina al’umma mai kaykkyawar makoma ta bai daya a fannin kiwon lafiya, don tabbatar da ƙoshin lafiyar jama’a. A shekara ta 1963, kasar Sin ta tura tawagar ma’aikatan jinya ta farko zuwa nahiyar Afirka. Kawo yanzu, akwai ma’aikatan jinyar ƙasar Sin da dama wadanda aka tura zuwa Afirka don kulawa gami da samar da magani ga mutanen Afirka, inda aka jinjina musu saboda jajircewarsu wajen kare rayukan al’ummar wurin. Har ma ana kiran likitocin ƙasar Sin da suna “mala’ikar…
Read More