Editor

9513 Posts
Sin na adawa da yadda NATO ke ta ƙiyayya tsakanin manyan rukunoni a faɗin duniya

Sin na adawa da yadda NATO ke ta ƙiyayya tsakanin manyan rukunoni a faɗin duniya

Daga CMG HAUSA Kwamitin sulhu na MDD ya kira taro kan batun Ukraine a jiya Alhamis, inda zaunannen wakilin ƙasar Sin dake majalisar Zhang Jun, ya yi kira ga ƙasa da ƙasa da su rubanya ƙoƙarinsu wajen sa kaimi ga tsagaita buɗe wuta a tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa. Ya kuma bayyana cewa, akwai darasi a cikin matsalar Ukraine, don haka ya kamata a yi tunani a kansa sosai. Ban da wannan kuma Zhang ya nuna cewa, ƙungiyar NATO na habaka zuwa gabas bayan yaƙin cacar baki. Ya ce NATO ƙungiyar tsaro ce, amma tana ta tada yaƙe-yaƙe a…
Read More
Shugaban Bankin CBN ya shiga jerin masu zawarcin shugabancin Nijeriya

Shugaban Bankin CBN ya shiga jerin masu zawarcin shugabancin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Tuni Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emiefele ya shigo sahun masu zawarcin kujerar Shugaban Ƙasa ƙarkashin tutar APC bayan da shi ma ya yanki takardar bayyana aniyar takara kan miliyan N100. A ranar Juma'a Emiefele ya yankin fom ɗin nasa Tun a 2014 tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya naɗa Emiefele Gwamnan Babban Bankin Nijeriya bayan da ya sauke Sunusi Lamido Sunusi.
Read More
2023: Babu zaɓen fidda gwani bayan 3 ga watan Yuni, INEC ta gargaɗi jam’iyyu

2023: Babu zaɓen fidda gwani bayan 3 ga watan Yuni, INEC ta gargaɗi jam’iyyu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta gargaɗi jam’iyyun siyasar Nijeriya cewa, ranar Juma’a 3 ga watan Yuni 2022 ya rage wa’adin gudanar da zaɓen fidda gwanin zaɓukan 2023. Hukumar zaɓen ƙasar ta fitar da wannan sanarwa ne a ranar Alhamis ta hannun shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, Festus Okoye. A cewar Festus Okoye, dukkanin jam’iyyun siyasa na da wata guda daga yau su kammala zaɓen fidda gwani. Ya jaddada cewa, ya kamata a gabatar da sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya tsakanin ranakun…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Rikicin APC a Kano, Shekarau ya sha kaye a hannun Ganduje a kotu

Da ɗumi-ɗumi: Rikicin APC a Kano, Shekarau ya sha kaye a hannun Ganduje a kotu

A ranar Juma'a Kotun Ƙoli ta kori ƙarar da tsagin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya shigar yana mai neman kotu ta tabbatar da shi a matsayin halastaccen APC na jihar Kano bisa ga tsagin Gwamna Abdullahi Ganduje. Kotun ta ce ƙarar da ɓangaren Shekarau ya shigar ba ta da hurumin da kotu za ta saurare ta, don haka ta kori ƙarar sannan ta tabbatar da tsagin Gwamna Ganduje a matsayin halastaccen APC a Kano. Cikkaken labari na nan tafe....
Read More
Zan iya cigaba da zama kocin Madrid shekaru 10 – Ancelotti

Zan iya cigaba da zama kocin Madrid shekaru 10 – Ancelotti

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana cewa, wataƙila ya yi ritaya idan ya bar ƙungiyar da ta zama zakarar gasar La Liga a bana, sai dai ya ce, a shirye ya ke ya cigaba da zama tare da qungiyar Madrid ɗin tsawon shekaru masu yawa a nan gaba. Ancelotti ɗan ƙasar Italiya mai shekaru 62 a duniya, ya zama koci na farko a tarihi da ya lashe kofunan manyan lig-lig guda biyar na Turai, nasarar da ya cimma a wannan kakar tare da Real Madrid bayan lashe gasar La Liga, inda kuma ya jagoranci karawa da Manchester City ranar…
Read More
Saƙon sallah: Mun kusa yin nasara a yaƙi da ‘yan ta’adda – Buhari

Saƙon sallah: Mun kusa yin nasara a yaƙi da ‘yan ta’adda – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce za su "tabbatar ba a samu ƙarancin kuɗi ba" a gwamnatinsa wajen samar da tsaro a faɗin ƙasar kuma "saura qiris a samu nasara a yaƙi da 'yan ta'addan Boko Haram masu fakewa da Musulunci". Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake taya al'ummar Musulmi murnar bikin Ƙaramar Sallah a ranar Lahadi, yana mai cewa "muna da dalilin da ya sa za mu yi bikin (Sallah) cikin ƙwarin gwiwa". "Yaƙin da ake yi da 'yan ta'adda da suke fakewa da Musulunci ya kusa zuwa ƙarshe," in ji…
Read More
Saƙon sallah: Mu na ƙoƙarin rage ƙarin farashin aikin Hajjin bana – NAHCON

Saƙon sallah: Mu na ƙoƙarin rage ƙarin farashin aikin Hajjin bana – NAHCON

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan, ya bayyana cewa hukumar na nan na iya bakin ƙoƙarinta na ganin cewa an rage farashin aikin Hajji na bana, duk da cewa ba makawa sai an ƙara farashin. Kunle ya bayyana haka ne a saƙon sallah da ya fitar, wanda ya sanya hannu da kansa ranar Litinin. A cewarsa, NAHCON na bin hanyoyin da su ka dace don ganin cewa an an bi hanyoyin da su ka dace domin ganin cewa ƙarin farashin aikin Hajjin bai yi yawan da har za a koka…
Read More
Harin jirgin qasa: Muna aiki domin ceto mutanen da aka sace – Buhari

Harin jirgin qasa: Muna aiki domin ceto mutanen da aka sace – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar wa iyalai da 'yan uwan mutanen da aka sace daga jirgin qasan Abuja zuwa Kaduna cewa za a dawo da 'yan uwansu gida ba tare da matsala ba. Ya bayyana haka ne a yayin da wasu al'ummar Abuja suka kai masa gaisuwar Sallah ranar Litinin a fadarsa ta Aso Villa. Wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaba Buhari ya fitar ta ambato shugaban ƙasar yana cewa 'yan bindigar suna amfani da mutanen da suka kama ne a matsayin wata garkuwa. "A yayin da muke murnar…
Read More
Buhari ya bayyana wanda zai miƙa wa ragamar mulki a 2023

Buhari ya bayyana wanda zai miƙa wa ragamar mulki a 2023

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, wanda zai miƙa wa mulki a 2023, mutum ne wanda 'yan Nijeriya suka zaɓa. Shugaba Buhari ya faɗi haka ne da yake zantawa da manema labarai a Aso Rock bayan an sauka sallar Idi. Ɗan jarida ya tambayi Shugaba Buhari cewa ”'yan takarar Shugaban Ƙasa na ta zuwa wurinka neman yarda, kuma wasu sun ce ka ce muce su je su fito takara, wa za ka miƙa wa mulki a 2023? Sai Buhari ya ce, ”duk wanda 'yan Nijeriya suka zaɓa shi ne zan miƙa wa mulki.…
Read More
Yaqi da taaddanci na buƙatar haɗin gwiwar dukkanin sassa

Yaqi da taaddanci na buƙatar haɗin gwiwar dukkanin sassa

Daga CMG HAUSA Ta’addanci da dukkanin nau’o’insa na cikin manyan ƙalubalolin da ƙasashen duniya da dama ke fuskanta, tun daga sassan Turai zuwa Asiya da gabas ta tsakiya da nahiyar Afirka, kusan ba inda wannan matsala ba ta shafa ba. Masharhanta na ta bayyana hanyoyi, da dabarun da suke ganin wajibi a bi su, idan har ana fatan shawo kan wannan ƙalubale da ya zamewa duniya ƙadangaren bakin tulo. Yayin ziyarar babban magatakardar MDD Antonio Guterres, a ƙasashen Senegal da jamhuriyar Nijar da Najeriya, babban jami’in ya yi tsokaci game da muhimmancin haɗa ƙarfi da ƙarfi tsakanin dukkanin ƙasashen duniya,…
Read More