07
May
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu 'yan uwa guda biyu a Lahadin da ta gabata sun rasa rayukansu a ƙoƙarin ɗauko wayar salula da ta faɗa cikin masai a Jihar Kano. Rahotanni sun bayyana cewa mutum na farko, mai suna Haruna Abdullahi mai shekaru 30 da haihuwa, shi ya fara shiga cikin shaddar domin ya ɗauko wayarsa da ta faɗa. Lamarin dai ya afku ne a ƙauyen Aku da ke Ƙaramar Hukumar Gaya ta jihar. Rahotanni sun bayyana cewa yayin da Marigayi Abdullahi ya shiga shaddar domin ɗauko wayar ta sa, sai ya maƙale ya kasa fitowa, lamarin da…
