Editor

9513 Posts
Rijiyoyin burtsatse da Sin ta gina sun taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar rashin ruwa mai tsafta a Rwanda

Rijiyoyin burtsatse da Sin ta gina sun taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar rashin ruwa mai tsafta a Rwanda

Daga CMG HAUSA A baya, dubban mazaunan gabashin Rwanda ne suka yi fama da rashin tsaftataccen ruwan sha saboda matsalar fari. Misali, a yankin Rwinkwavu na gundumar Kayonza dake lardin gabashi, mazauna sai sun yi tafiya mai nisa, kafin su samu ruwa mai tsafta. Sai dai yanzu, wannan matsalar ta zama tarihi, bayan ayyukan ginin rijiyoyin burtsatsai 200 da ƙasar Sin ta samar da kudin aiwatarwa, domin kawo ƙarshen matsalar rashin ruwa a lardin. A baya-bayan nan ne aka kammala aikin tare da ƙaddamar da shi, inda mutane 110,000 ke amfana. Mazauna a gundunmomi daban daban na lardin, sun shaidawa…
Read More
Ƙasar Sin: Yunƙurin Amurka na yin tasiri kan ƙasashen yankin tekun Indiya da Fasifik bai dace da muradun ƙasashen ba

Ƙasar Sin: Yunƙurin Amurka na yin tasiri kan ƙasashen yankin tekun Indiya da Fasifik bai dace da muradun ƙasashen ba

Daga CMG HAUSA Dan majalisar gudanarwar ƙasar Sin kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya ce yunƙurin Amurka na samar da ƙarin tasiri kan ƙasashen yankin tekun Indiya da Fasifik, bai dace da muradun ƙasashen dake yankin ba. Wang Yi ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa ta kafar bidiyo da Luhut Binsar Pandjatan, jami’in ƙasar Indonesia mai kula da dangantakarta da ƙasar Sin. A cewar Wang Yi, tuni yankin gabashin Asia ke da tsarinsa na haɗin gwiwa karkashin kungiyar ƙasashen kudu maso gabashin Asiya wato (ASEAN), yana mai cewa ƙungiyar ita ce jigon tabbatar da zaman lafiya…
Read More
Ba zan manta da halaccin Sanata Lawan a rayuwata ba – Hon. Kaitafi

Ba zan manta da halaccin Sanata Lawan a rayuwata ba – Hon. Kaitafi

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu  Tsohon hadimin shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya (SA Protocol) kuma dan takarar kujerar malajisar wakilai a kananan hukumomin Bade da Jakusko, Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya ce ba zai taba mantawa da halascin da maigidan sa kuma shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya- Sanata Ahmed Ibrahim Lawan ya yi masa ba a rayuwa ba, ya kara da cewa har abada zai ci gaba da tuna abubuwan alherin da ya shuka a rayuwarsa tare da ci gaba da mutunta shi a matsayin wanda shi ne sanadin duk wani ci gaban da ya samu a rayuwa, tare da ɗaukarsa a matsayin…
Read More
Mawallafin waƙar taken NYSC ya rasu yana da shekaru 74

Mawallafin waƙar taken NYSC ya rasu yana da shekaru 74

Daga AMINA YUSUF ALI Mawallallafin waƙar nan mai daɗin ji ta taken 'yan bautar ƙasa (NYSC), Dakta Oluwole Adetiran ya kwanta dama. Dakta Oluwole Adetiran, ya rasu ranar Juma'a 6 ga watan Mayun shekarar nan ta 2022. Ya rasu yana da shekaru 74 da haihuwa. An samu tabbacin labarin rasuwar Marigayin ne daga wasu mambobi na majami'ar Celestial Church of Christ (CCC), wanda shi ma marigayin mamba ne na wannan majami'ar. Shi ma shugaban tsare-tsaren na NYSC a jihar Ogun, Dakta Belinda Faniyi ita ma ta ƙara tabbatar da labarin rasuwar. A cewar ta ma, a lokacin tana ƙoƙarin sanar…
Read More
Osinbanjo da Tinubu sun yi musabiha a taron fitar da ɗan takarar APC a yankin Yarabawa

Osinbanjo da Tinubu sun yi musabiha a taron fitar da ɗan takarar APC a yankin Yarabawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Karon farko tun bayan ayyana aniyar taka takarar kujeran Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi ido huɗu da jagoran Jam'iyyar APC kuma maigidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jihar Legas. Jiga-jigan Jam'iyyar APCn biyu sun haɗu ne yayin wani taron zaman haɗin kai tsakanin 'yan takarar kujerar shugaban ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar APC daga yankin ƙabilar Yoruba. Dattawan yankin Kudu maso Yamma ne suka shirya zaman don ganin yadda za a haɗa kai da juna don tsayar da mutum guda cikinsu. Dattawan sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande, da tsohon…
Read More
Saudiyya ta cafke ‘yan Nijeriya bisa laifukan barbaza hotunan wani ɗan takara na Nijeriya

Saudiyya ta cafke ‘yan Nijeriya bisa laifukan barbaza hotunan wani ɗan takara na Nijeriya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Hukumomin Ƙasar Saudiyya sun cafke ‘yan Nijeriya guda 20 bisa laifukan ta’ammali da baza hotunan wani mai neman shiga takarar shugabancin Nijeriya a harabobin Harami dake garin Makka ta ƙasa mai tsarki. A halin da ake ciki dai, waɗannan ‘yan Nijeriya suna damƙe a hannun mahukuntan ƙasar ta Saudiyya ƙarƙashin kulawa da askarawan ƙasar kafin gurfanar da su a gaban kuliya manta-sabo, inda za a yi masu hukunce-hukunce daidai da laifukan su. Wata majiya mai tushe ta shaidar da cewar, waɗannan ‘yan Nijeriya da suka shiga cikin halayyar aikata sharo ba shanu, za su ɗanɗana…
Read More
Sheikh Gumi ya ƙaddamar da ƙungiyar kare haƙƙin Fulani makiyaya

Sheikh Gumi ya ƙaddamar da ƙungiyar kare haƙƙin Fulani makiyaya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shaharren malamin  addinin Musuluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi ya kafa ƙungiyar da za ta kare haƙƙin Fulani makiyaya. Gumi ya sanar da kafa wannan ƙungiya da ya kira Nomadic Rights Concern, NORIC a taƙaice a yayin gudanar da tafsirin watan Ramadan a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a arewacin Nijeriya. Ya ce ƙungiyar za ta janyo hankali al’umma a game da cin zarafin Fulani makiyaya da ake yi. Ya bayyan Farfesa Umar Labbo a matsayin wanda zai jagoranci ƙungiyar, yana mai cewa NORIC za ta zama wata kafa…
Read More
NRC ta gyara layin dogon Abuja-Kaduna, ta gindaya sabbin sharaɗɗan sayen tikiti

NRC ta gyara layin dogon Abuja-Kaduna, ta gindaya sabbin sharaɗɗan sayen tikiti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), ta ce, ta gyara ɓarnar da aka yi wa na’urorin layin dogon Abuja zuwa Kaduna, da kuma sanya sabbin sharuɗɗa na sayen tikiti. Har ila yau, ta tabbatar da cewa, fasinjojin da ke son shiga za su gabatar da Lambar Shaida ta Ɗan Ƙasa (NIN), a matsayin wani sharaɗi na sayen tikitin jirgin ƙasa. Rahotanni sun nuna cewa, an yi matuƙar lalata layin dogon a kwanan nan sakamakon harin da maharan suka kai. Manajan Daraktan NRC, Injiniya Fidet Okhiria ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da…
Read More
Ranar Ma’aikata: Jihar Edo za ta fara biyan Naira 40,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Ranar Ma’aikata: Jihar Edo za ta fara biyan Naira 40,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Edo da ke kudancin Nijeriya, Godwin Obaseki, ya ƙara albashi mafi ƙaranci a jihar zuwa Naira 40,000 sama da Naira 30,000 da Gwamnatin Tarayya ta saka wa ma'aikatanta. Obaseki ya sanar da ƙarin a ranar Lahadi yayin da ake bikin Ranar Ma'aikata ta Duniya. Kazalika wasu rahotanni na cewa tsoffin ma'aikatan jihar sun gudanar da zanga-zangar neman a biya su garatutinsu a ranar. "Kamar yadda muka sani, mafi ƙarancin albashi na Naira 30,000 da ƙyar zai iya riƙe iyali, rashin ɗa'a ne da tausayi mu ci gaba da basarwa cewa ba mu…
Read More
Har yanzu mata suna baya wajen samun madafun iko a Nijeriya – NBS

Har yanzu mata suna baya wajen samun madafun iko a Nijeriya – NBS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, NBS, ta bayyana cewa har yanzu an bar mata a baya a Nijeriya wajen samun madafun iko, idan aka kwatanta su da maza a ƙasar. Wannan na ƙunshe ne a wani rahoto da ya fita ranar Lahadi a Abuja daga Kundin Ƙididdigar Jinsi na Watanni uku-uku, na wata ukun farko a 2022. Kundin rahoton ya maida hankali ne a kan wasu lamura uku da su ka haɗa da, mulki, madafar iko, lafiya, ƙididdigar al'umma da kuma ilimi. A cewar rahoton, ƙididdiga ta nuna cewa kashen mata da su ke fitowa…
Read More