Osinbanjo da Tinubu sun yi musabiha a taron fitar da ɗan takarar APC a yankin Yarabawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Karon farko tun bayan ayyana aniyar taka takarar kujeran Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi ido huɗu da jagoran Jam’iyyar APC kuma maigidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jihar Legas.

Jiga-jigan Jam’iyyar APCn biyu sun haɗu ne yayin wani taron zaman haɗin kai tsakanin ‘yan takarar kujerar shugaban ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar APC daga yankin ƙabilar Yoruba.

Dattawan yankin Kudu maso Yamma ne suka shirya zaman don ganin yadda za a haɗa kai da juna don tsayar da mutum guda cikinsu.

Dattawan sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande, da tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba.

Waɗanda ke hallare a zaman sun haxa da Jigon APC Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi, da Ministar harkokin cikin gida Rauf Aregbesola.

Sauran su ne Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo Olu, Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu, da Gwamnan Jihar Osun Gboyega Oyetola.

Hakazalika akwai Ministan Ayyuka da Gidaje, Babajide Raji Fashola; Sanata Ibikunle Amosun; Sakataren APC Iyiola Omisore, Gwamnan Ogun Dapo Abiodun da sauransu.