Mawallafin waƙar taken NYSC ya rasu yana da shekaru 74

Daga AMINA YUSUF ALI

Mawallallafin waƙar nan mai daɗin ji ta taken ‘yan bautar ƙasa (NYSC), Dakta Oluwole Adetiran ya kwanta dama.

Dakta Oluwole Adetiran, ya rasu ranar Juma’a 6 ga watan Mayun shekarar nan ta 2022. Ya rasu yana da shekaru 74 da haihuwa.

An samu tabbacin labarin rasuwar Marigayin ne daga wasu mambobi na majami’ar Celestial Church of Christ (CCC), wanda shi ma marigayin mamba ne na wannan majami’ar.

Shi ma shugaban tsare-tsaren na NYSC a jihar Ogun, Dakta Belinda Faniyi ita ma ta ƙara tabbatar da labarin rasuwar. A cewar ta ma, a lokacin tana ƙoƙarin sanar wa da babban daraktan janar na NYSC ne labarin rasuwar marubucin. Ta bayyana hakan a yayin zantawarta da Jaridar Ingilishi ta Punch.

Rahotanni sun bayyana cewa, Darakta Janar na NYSC, Ibrahim Shu’aibu, ya ziyarci marigayin mai shekaru 74 cikin watan Yulin 2021. A gidansa dake yankin Ibafo, na ƙaramar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun.

Tun kafin rasuwarsa, marubuci wanda taken NYSC da ya rubuta shi kuma ya buga tun a shekarar 1984 ya ce yana jin nishadi matuƙa da alfahari a yadda sunansa bai ɓace ba bayan kusan shekaru 37 da yin waƙar.

Sannan ya bayyana cewa, yana fama da cututtukan hawan jini, ciwon suga, da jeji tun a shekarar 2018.

Marigayi Adetiran, ya karanci kiɗa da waƙa ne a jami’ar Nijeriya mai suna, Nsukka. Sannan ya buga waƙar taken NYSC ɗin ne a lokacin yana bautar ƙasa a jihar Oyo cikin shekarar 1984.