Ba zan manta da halaccin Sanata Lawan a rayuwata ba – Hon. Kaitafi

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu 

Tsohon hadimin shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya (SA Protocol) kuma dan takarar kujerar malajisar wakilai a kananan hukumomin Bade da Jakusko, Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya ce ba zai taba mantawa da halascin da maigidan sa kuma shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya- Sanata Ahmed Ibrahim Lawan ya yi masa ba a rayuwa ba, ya kara da cewa har abada zai ci gaba da tuna abubuwan alherin da ya shuka a rayuwarsa tare da ci gaba da mutunta shi a matsayin wanda shi ne sanadin duk wani ci gaban da ya samu a rayuwa, tare da ɗaukarsa a matsayin uba. 

Haka kuma, ya ƙara da cewa, tun bayan shigarsa harkokin siyasa a hannun Alhaji Tijjani Musa Tumsa a 2006, Sanata Ahmed Lawan da Gwamna Mai Mala Buni, wanda tun daga wancan lokaci ya kasance ƙarƙashin Sanata Lawan, wanda ya riƙe shi a matsayin ‘da’ tare da ɗora shi bisa ingantacciyar turbar da ta kai shi ga dukan ci gaban da ya samu a rayuwarsa. Har wala yau ya ce zai ci gaba da yi wa musa gidan nasa biyayya, girmama wa tare da bin turbar da suka ɗora shi.

Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya bayyana hakan a sa’ilin da yake karvar fom ɗin da al’ummar ƙananan hukumomin Bade da Jakusko suka saya masa domin yin takarar kujerar majalisar wakilai a gidansa dake Abuja a ƙarshen mako.

Yayin da ya nuna matuƙar godiya dangane da wannan karimcin da jama’a suka nuna masa tare da shaidar da cewa, “Babu wata kalma da zan yi amfani da ita wadda za ta yi daidai da wannan ƙauna da karammawa da kuka nuna min face kawai na miqa godiya ga Allah, da godiya gare ku. Saboda duk da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki amma kuka sadaukar da taro da kwabon da ya dace ku yi cefane da shi wajen saya mini fom ɗin takara.

“Ko shakka babu kun yi haka ne domin imanin da kuke da shi cewa wannan sadaukarwa ba za ta tafi a banza ba. Kuna da tabbacin cewa zan riqe amarnar da za ku ɗora min, tare da burin samun wakilci na gari ga al’ummar yankinmu.” 

Hon. Kaitafi ya shaidar da cewa, “na shiga harkokin siyasa a 2006 kuma ba domin na yi takarar wata kujera ba, kawai na shigeta ne domin na koya na amfana, kuma jama’ar da nake tare da su su ci gajiyar dimukuraɗiyya, wanda yanzu kwatsam mun zo wata gaba wadda muna yi wa Allah godiya, tare da matuƙar alfahari da goyon baya da jama’a suke bamu, abu ne daga Allah, saboda ba mu da wani girma ko yanayin da zai saka mu samu tagomashin face kawai Allah ne ya tsara haka.” 

Ya ƙara da cewa, “sannan a cikin yardar Allah; tunda jama’a suka tara kuɗinsu wajen bani wannan damar (suka saya min fim), In Sha Allah ba zan saka su kunya ba, zan bai wa maras ɗa kunya.

Kuma kafin wannan lokaci ban taba furta zan yi takara ba, amma daga yau; ina mai bai wa al’ummar Bade/Jakusko tabbacin cewa zan tsaya takarar kujerar majalisar wakilai domin wakiltar ƙananan hukumomin Bade da Jakusko a zaɓen 2023 mai zuwa, a karkashin jam’iyyar APC.” 

“Saboda haka, ina baran addu’a da goyon bayan manyanmu daga waɗannan qananan hukumomi, Arewacin Yobe dama jiharmu baki ɗaya. Don Allah ku dubeni a matsayin ɗanku, tare da bani dama a wannan kuduri da muka sanya a gaba.

“Kamar yadda kuke da kyakkyawan fata gareni, in sha Allah zan yi duk abin da ya dace wajen ganin an samu gagarumin sauyin siyasa mai ma’ana wanda ba a tava samun makamancin sa ba a wannan yanki namu.

“Saboda kuma irin yadda kullum nake biye da salon turbar da maigidana- Sanata Ahmad Lawan ya ɗorani, wanda ya kawo ci gaban da wannan yankin bai taɓa ganin makamancin sa ba,” in ji Hon. Kaitafi. 

Da yake miqa fom ɗin da al’ummar yankin suka saya masa zuwa ga Sani Kaitafi, shugaban kwamitin asusun tara kuɗin, Alhaji Bukar Dala, ya yaba dangane da sadaukarwar da jama’ar yankin suka nuna kasancewar yunƙurin shi ne na farko a tarihin siyasar jihar Yobe.

Ya ce sun yi hakan bisa cancantar ɗan takarar, a matsayin sa na mutum mai kishin jama’a kana da halayen jinƙai da dattakun da aka san shi da su.

“Bisa ga hakan muke miƙa wannan fom wanda al’ummar yankin Bade/ Jakusko suka saya maka, domin yin takarar kujerar majalisar wakilai tare da kyautata zaton samun wakilci nagari daga wajenka, saboda haka muna kira gareka ka kula da wannan nauyin da aka ɗora maka tare da tabbacin cewa za ka iya wajen bai wa maras ɗa kunya idan Allah ya baka nasara.”