08
May
Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Mai neman tsaya wa takarar kujerar Gwamnan Jihar Bauchi a zaɓen shekara ta 2023, Dokta Musa Babayo ya bayyana cewar, yana neman zama gwamna ne domin ya saka wa jiha bisa nauyi data ɗauka na karatun bokon sa tun daga makarantar firmare, sakandare, har ya zuwa jami’a. Dokta Musa Babayo yace nauyin karatun sa tun daga ɗarnukan 60 zuwa 70 karamar hukumar en’e da Sarkin yanka ke jagoranci ne ta ɗauki nauyi, sa’annan gwamnatin jiha ta karɓa, yana mai cewar, karatun digirin sa ne na biyu ya samu tallafin ƙasar waje. Babayo, wanda yake yin…
