08
May
Daga CMG HAUSA Reshen kamfanin sarrafa ƙarafa na ƙasar Sin dake ƙasar Kamaru da ma’aikatar kula da haƙar ma’adinai, da masana’antu, da nazarin fasahohi ta ƙasar Kamaru sun daddale yarjejeniyar haƙar ma’adinan ƙarfe a ƙasar Kamaru da jarin da aka zuba a fannin wanda ya kai fiye da dalar Amurka miliyan 700. Ministan kula da haƙar ma’adinai, da masana’antu, da nazarin fasahohi na ƙasar Kamaru Gabriel Dodo Ndoke, da manajan reshen kamfanin Zheng Zhenghao sun daddale yarjejeniyar. Bisa bayanin da kamfanin sarrafa ƙarafa na ƙasar Sin ya yi, yarjejeniyar ta hada da aikin haƙar ma’adinan karfe dake birnin Kribi na kudancin ƙasar…
