09
May
Daga AISHA ASAS Na ci karo da wani rubutu da ya ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya ɗauki hankalina izuwa wannan rubutu, ba don komai ba sai don zamewarsa bulaliya ga wata ɗabi'a da mata musamman na hausawa suka maida jiki. Kafin komai, bari mu ji wannan labari da za a iya kira kukan kurciya. Wani ne ya ɗauki matarsa suka je gidan Zoo don kallon dabbobi. Karon farko suka ci karo da Biri da matarsa suna wasa irin ta masoya, cikin shaƙqi matar ta ce, kaga masoya. Gaba kaɗan suka hango zaki da zakanya suna zaune, zakin…
