Editor

9513 Posts
Ƙasashen Afirka sun yi shiru don nuna ƙin amincewa ga ƙasashen Yamma

Ƙasashen Afirka sun yi shiru don nuna ƙin amincewa ga ƙasashen Yamma

Daga CMG HAUSA Bayan ɓarkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine, Amurka da wasu ƙasashen yamma na ƙoƙarin mai da ƙasar Rasha saniyar ware, inda suke matsawa sauran ƙasashe lamba, domin su goyi bayansu. Hakan ya sa wasu jami’an ƙasar Amurka ke daga murya ga ƙasashen Afirka, don su yi watsi da matsayinsu na ‘yan ba ruwanmu. Duk da haka, yayin da ake jefa kuri’a a Majalisar Ɗinkin Duniya don tabbatar da cewa ko za a yi Allah wadai da ƙasar Rasha, akwai ƙasashe 25 dake nahiyar Afirka da suka jefa ƙuri’ar janyewa daga batun, ko kuma kin jefa ƙuri’ar. To,…
Read More
Amurka ba ta da izinin zargin jama’ar Afirka kan zaɓin yin haɗin gwiwa tare da Sin

Amurka ba ta da izinin zargin jama’ar Afirka kan zaɓin yin haɗin gwiwa tare da Sin

Daga CMG HAUSA A yayin ziyarar da mataimakiyar sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka Wendy Sherman ta yi a nahiyar Afirka, ta bayyana cewa, wasu ƙasashen Afirka sun zabi kamfanin Huawei na ƙasar Sin a matsayin kamfanin dake samar da hidimar sadarwa, wai wadannan ƙasashe sun yi watsi da ikon mulkin kasa. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, zargin da jami’ar Amurka ta yi kan ƙasar Sin ba shi da tushe. Ya rage ga ƙasashen Afirka da jama'ar su zabi waɗanda za…
Read More
Amurka ta aikata assha da sunan asusun NED

Amurka ta aikata assha da sunan asusun NED

Daga CMG HAUSA Ƙila wasu sun san asusun demokuraɗiyya na ƙasar Amurka, saboda sunan asusun ya ambato demokuraɗiyya wato NED. Amma mene ne gaskiyar asusun? Kwanan baya, ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta fitar da wasu jerin shaidu a shafinta na Internet, inda ta bankaɗo asirin asusun. Haƙiƙa asusun NED ya ƙulla maƙarƙashiya da yawa a sassan duniya, kamar ta da rikicin kawo ɓaraka, yin juya juyin mulki, rikicin siyasa, yin ƙarya da yaɗa jita-jita da dai sauransu. Ba za a iya lissafa laifuffukan da asusun na NED ya aikata ba. Ƙila ayyukan assha da ya aikata za su wuce…
Read More
APC za ta samar da daidaito ga duk masu son tsayawa takara – Adamu

APC za ta samar da daidaito ga duk masu son tsayawa takara – Adamu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya tabbatar wa duk masu neman muƙamai daban-daban a faɗin ƙasar nan cewa, jam'iyyar za ta yi gaskiya da samar da daidaito a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar mai zuwa. Adamu ya bayar da wannan tabbacin ne a ƙaramar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a shiyyar sanata ta Yamma suka gudanar da wani taro na nuna ɓangaranci da karrama shi. Ya kuma yaba wa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar bisa wannan…
Read More
Dalilan ASUU na sake tsawaita wa’adin yajin aikinta da watanni uku

Dalilan ASUU na sake tsawaita wa’adin yajin aikinta da watanni uku

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) ta bayyana cewa, ta tsawaita wa'adin yajin aikin da take tsaka da gudanar da makonni 12 saboda rashin yin abin da ya kamata daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya. Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana tsawaita wa'adin yajin aikin a ranar Litinin, yana mai cewa sun ɗauki wannan mataki ne domin bai wa Gwamnati isasshen lokaci wajen warware matsalolin da suka gabatar mata. Ya ƙara da cewa, tsawaita wa'adin yajin aikin ya fara aiki ne daga kan ƙarfe 12:01am na ranar 9 ga Mayun 2022. Haka nan, ya ce sun yanke shawarar tsawaita wa'adin…
Read More
Wani sirri da ya kamata mata su sani game da kwalliya

Wani sirri da ya kamata mata su sani game da kwalliya

Daga QURRATUL-AYN SALIS  Mata da dama na son sanin sirrin da ke sanya kowacce kyau. A gaskiya zamani ya kaimu lokacin da babu mace mummuna sai dai in ta ga damar zama mummuna. Akwai sirrin kwalliya da dama, ta yadda duk munin mace idan har tana kulawa da su, zai yi wuya a ga muninta. Shi ya sa wasu mazan ke bai wa junansu shawarar gane kyakyawar mace, domin ka da a zo a yi zaɓen tumun dare. Idan mace ta zama mummuna ita ta so. Akwai ababe da dama da ake gyarawa daga yanayin shafa hoda da jan-baki da…
Read More
An sake garzayawa da Sarki Salman na Saudiyya asibiti

An sake garzayawa da Sarki Salman na Saudiyya asibiti

Daga BASHIR ISAH An garzaya da Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya zuwa asibitin Jidda domin ci gaba da duba lafiyarsa. A ranar Lahadi Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya ba da sanarwar garzayawar da aka yi da basaraken mai shekaru 86 zuwa a asibiti. Rahoton Masarautar Saudiyya ya nuna a ranar Asabar ne Sarki Salman ya tafi Asibitin Ƙwararru na Sarki Faisal don bincika lafiyarsa. A shekarar 2015 ne Sarki Salman bn Abdulaziz ya ɗare kujerar sarauta a matsayin sarkin Saudiyya na bakwai biyo bayan rasuwar Sarki Abdullah bin Abdulaziz. Kafin wannan lokaci, Sarki Salman ya tafi asibiti a…
Read More
Shugaba Buhari ya tafi taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Shugaba Buhari ya tafi taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya keta hazo zuwa Abidjan a Ƙasar Cote d’Ivoire domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya. Taron zai maida hankali ne kan abin da ya shafi lalubo hanyoyin magance matsalolin zezayar ƙasa, fari, gushewar dazuzzuka da sauransu da kuma tasirinsu ga tattalin arzikin duniya. Wannan shi ne karo na goma sha biyar da MƊƊ ke shirya irin wannan taro wanda zai gudana daga ranar 9 zuwa 10 na watan Mayun 2022. Sanarwar da ta fito ta hannun Kakin Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ta nuna babban taron zai tattauna a kan matakan da suka…
Read More
Akwai ƙoƙarin da muke yi na inganta tsarin makarantun tsangaya – Gwani Jibrin

Akwai ƙoƙarin da muke yi na inganta tsarin makarantun tsangaya – Gwani Jibrin

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Tun bayan sake ci gaba da muhawarar da ta taso a zaurukan sada zumunta dangane da zargin da wata jarumar finafinan Hausa, Nafisatu Abdullahi ta yi game da gararambar yara ƙanana suna yawon bara a titi, babu kulawar iyaye, 'yan Nijeriya ke ta tofa albarkacin bakinsu game da illar tura yara ƙanana almajiranci da samar da sabon tsari ga makarantun tsangaya, yadda za su dace da zamani. Shugaban Ƙungiyar Inganta Ilimin Tsangaya na ƙasa wato Tsangaya Education Development Initiative, ƙarƙashin gamayyar wasu manyan alarammomin Nijeriya, GWANI JIBRIN YAHAYA ALQASIM, ya gana da wakilin Blueprint Manhaja ABBA…
Read More