10
May
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shirin naɗa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC ya yi ƙaurin suna a ranar Litinin da ta gabata, inda sa'o'i kaɗan bayan faruwar hakan Jonathan ya ziyarci ofishin shugaban jam’iyyar, Abdullahi Adamu, domin nisanta kansa ga wannan mataki. An buga hotunan ziyarar ta yanar gizo a daren Litinin. Rahotanni sun ce Jonathan ya ziyarci Adamu a gidansa. An ɗauki hoton 'yan siyasar biyu suna tare da juna suna murmushi. Ziyarar na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan ƙungiyar 'Miyetti Allah Cattle Rearers', wata ƙungiyar Fulani ta sayi fom ɗin tsayawa takara da…
