Editor

9513 Posts
Kotu ta yi fatali da hukuncin soke Sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe

Kotu ta yi fatali da hukuncin soke Sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe

Daga BASHIR ISAH Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jingine hukuncin da Babbar Kotun Umuahia a Jihar Abia, ta yanke na soke tanade-tanaden Sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe ta 2022. A hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce, Babbar Kotun ba ta da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar a gabanta, saboda a cewarta tun farko, wanda ya shigar da ƙarar, Nduka Edede ba shi da cancantar yin hakan Kwamitin Alƙalai mai mambobi guda uku ƙarƙashin Alƙali Hamma Akawu Barka ne ya soke wannan hukuncin. Alƙalan sun ce Edede ya gaza bai wa kotu ƙwaƙƙwarar hujjar…
Read More
Sin ta bada gudunmawar rigakafin Sinovac da kayayyakin lafiya ga Benin

Sin ta bada gudunmawar rigakafin Sinovac da kayayyakin lafiya ga Benin

Daga CMG HAUSA A jiya Talata jamhuriyar Benin ta karɓi rukunin alluran riga-kafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinovac, da kayayyakin kiwon lafiya waɗanda gwamnatin kasar Sin ta bayar a matsayin gudunmawa. Babban jami’in ofishin jakadancin Sin dake ƙasar Benin, Yan Yan, ya jagoranci bikin mika tallafin da yammacin ranar Talata, tare da babban darakta a ma’aikatar lafiyar jamhuriyar Benin, Petas Akogbeto, wanda aka gudanar a Cotonou, birnin tashar ruwan jamhuriyar Benin. Gudunmawar dai ta kunshi kwalaben alluran riga-kafi na kamfanin Sinovac, da sirinji, da na’urar ɗaukar hoton jiki, da manyan na’urorin binciken yanayin lafiyar jiki, da famfunan sirinji masu aiki…
Read More
Kamfanin Huawei ya bai wa matasan da suka kammala karatun jami’a a Habasha damarmaki a fannin fasahohin zamani na ICT

Kamfanin Huawei ya bai wa matasan da suka kammala karatun jami’a a Habasha damarmaki a fannin fasahohin zamani na ICT

Daga CMG HAUSA Sashen kamfanin Huawei na ƙasar Sin dake ƙasar Habasha ya shirya taron dandali da nufin bai wa sabbin daliban da suka kammala karatun jami’a damammakin samun horo a fannin fasahar sadarwa ta zamani. Tamire Dawud, manajan sashen bunkasa fasahar ICT a kamfanin fasahar sadarwa na Huawei dake Habasha, ya ce kafa dandali, wani ɓangare ne na burin kamfanin Huawei na ci gaba da bada horo, da samar da ilmi, ga sabbin matasan da suka kammala karatun jami’a domin horar da su game da sabbin dabarun zamani na kamfanin, da suka hada da fannonin yada bayanai, da fasahar…
Read More
Gidauniyar tallafawa Dimokuraɗiyya ko tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasashe?

Gidauniyar tallafawa Dimokuraɗiyya ko tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasashe?

Daga IBRAHIM YAYA A duk lokacin da aka ambaci asusu ko gidauniya, abin da zai fadowa mutum shi ne, aikin taimako ko inganta rayuwar al’umma a fannoni daban-daban, kamar lafiya, Ilimi, muhalli, mata har ma a wasu lokuta da kananan yara da sauransu. Sai dai sabanin irin asusu ko gidauniyar da al’umma suka sani, har ma suka ci moriyarsu, gidauniyar NED ta Amurka, wata gidauniya ce da Amurkar ta ƙirƙiro da nufin tayar da hargitsi da neman tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran ƙasashe da sunan raya demokiraɗiyya. A kwanakin nan ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta fitar da…
Read More
Adabin zamanin da na Sin

Adabin zamanin da na Sin

Daga AMINA XU Taƙaitaccen bayaniAdabi, wani kashi ne mai kuzari sosai a cikin al’adun ƙasar Sin. A cikin dogon tarihi, adabin gargajiyar ƙasar Sin ya hada da manyan ra’ayoyin al’adun ƙasar Sin, ya bayyana burin jama’ar ƙasar na neman gaskiya, da alamun ƙasar na musamman. Akwai nau’o’i daban daban na adabin ƙasar Sin, kamar tatsuniyoyi na zamanin da da can, da waƙoƙin daular Tang da ta Song, da labaran daular Ming da na Qing da dai sauransu. A cikin shekaru sama da dubu ɗaya da suka gabata, an samu shahararrun marubuta da bayanai masu dimbin yawa. A cikin bayanin da…
Read More
2023: APC ta yaba wa Adamu kan yadda ya warware rikicin jam’iyyar a Zamfara

2023: APC ta yaba wa Adamu kan yadda ya warware rikicin jam’iyyar a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta yaba wa shugabannin jam’iyyar na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu kan yadda suka warware rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a jihar. A wata sanarwa a ranar Talata a Gusau ta hannun Yusuf Idris, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na jihar, jam’iyyar ta yaba wa duk waɗanda suka halarci yarjejeniyar zaman lafiya. Idris ya ce, an warware rashin jituwar da ke tsakanin Gwamna Bello Matawalle da tsohon Gwamna Abdulaziz Yari a hedikwatar APC ta ƙasa da ke Abuja. Ya ƙara da cewa, yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin Matawalle da tsohon…
Read More
Saka murmushi a fuskar mabuƙata ke ba ni ƙwarin gwiwa – Maryam Yaro

Saka murmushi a fuskar mabuƙata ke ba ni ƙwarin gwiwa – Maryam Yaro

“Babban burina shine inganta rayuwar al’ummar Zamfara da sana'o'i" Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna A kullum iyaye mata ba su bari a bar su a baya, musamman a wannan zamanin su ne sahun gaba wurin taimakon al’umma a kowane yanki. Hajiya Maryam Shehu Yaro (Zarar Maru) ’yar asalin Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara ita ce mace ta farko da aka ba wa sarautar Zarar Maru a masarautar Maru da ke Ƙaramar Hukumar Muru, Jihar Zamfara. Allah Ya albakarkaci Hajiya Maryam da ‘ya’ya biyu mata, Hauwa da Amira. Hajiya Maryam gogaggiyar ‘yar boko ce, kuma ta na da ilimin addini,…
Read More
Mu kawar da bara, domin bara ba addini ba ce

Mu kawar da bara, domin bara ba addini ba ce

Daga MUHAMMAD BALA GARBA a Maiduguri                        A duk lokacin da aka ambaci kawar da Bara, sai wasu su ɗauki hakan a matsayin wani yunƙuri na hana karatun allo ko kuma Alƙur’ani mai girma. Wasu rashin sanin ma’anar Baran ne ya sa suke ɗauka karatun allo ake son hanawa. Wasu kuma suna sane da abin da ake nufi, amma saboda wasu ɓoyayyun manufofinsu da ke ƙarƙashin ƙasa ya sa suke sauya ma’anar maganar zuwa hana karatun allo ko kuma Alƙur’ani mai girma.  Da farko dai yana da kyau mu san cewa,…
Read More
Yadda cigaban fasahar sadarwa ke barazana ga aikin jarida

Yadda cigaban fasahar sadarwa ke barazana ga aikin jarida

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ba da jimawa ba a ranar 3 ga Mayu aka gudanar da bukin ranar bayyana ’yancin 'yan jarida na gudanar da bincike da samar da bayanai ga jama'a, da nufin faɗakar da al'umma, musamman hukumomi da jami'an tsaro da sauran su muhimmancin tsare hƙƙoƙin ɗan jarida da masu neman labarai, da mutunta su. Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ware kowacce wannan rana a kowacce shekara ta zama ranar da za a riƙa haɗuwa ana tattauna muhimman batutuwan da suka shafi rayuwar manema labarai a fagen samar da bayanai.  An fara gudanar da bukin wannan rana ne…
Read More
Zaɓen 2023: Zan yi aiki tuƙuru wajen ƙarfafa nagartar Jihar Neja – Malagi

Zaɓen 2023: Zan yi aiki tuƙuru wajen ƙarfafa nagartar Jihar Neja – Malagi

Daga WAKILIN MU Ɗaya daga cikin manyan masu neman tsaya wa jam'iyyar APC takarar zama gwamna a Jihar Neja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya sha alwashin zai fara aiki daga sa'ar farko da ya kama aiki a matsayin gwamna domin cimma burin sa na gina sabuwar nagartacciyar Jihar Neja idan har aka ba shi damar zama ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen fidda gwani mai zuwa. Malagi, wanda shi ne Shugaban kamfanin buga jaridun Blueprint da Manhaja, ya faɗi haka ne a ranar Talata a lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan ya miƙa fom ɗin sa…
Read More