17
Apr
*Siyasar ‘uba’ da ‘ɗa’ ta kunno kai a cikin jam’iyyar*Tinubu ya ‘sheganta’ Osinbajo*Yaro ya yi wa maigidansa ƙirmisisi Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A daidai lokacin da manyan zaɓukan 2023 ke ƙara tunkarowa, masu sha'awar taka takarar kujerar shugabancin Nijeriya a ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar sai ƙara bayyana kansu suke yi ga al'umma tare da tuntuvar masu ruwa da tsaki, don neman shawarwari da goyon bayansu. Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jagoran Jam'iyyar APC na Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakin Shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbanjo, su ma kamar sauran manema, sun fito sun nuna kwaɗayinsu…
