Editor

9513 Posts
Buhari ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Nda-Isaiah

Buhari ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Nda-Isaiah

Daga BASHIR ISAH A ranar Alhamis da ta gabata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya kai wa iyalan marigayi Nda-Isaiah ziyarar ta'aziyya dangane da rasuwar Mrs Eunice Ndanusa Nda-Isaiah wadda ta rasu a ranar 8 ga Afrilu. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa, Marigayiya Eunice, ita ce mahaifiyar wanda ya kafa kamfanin Jaridar Leadership, wato marigayi Sam Nda-Isaiah. Buhari wanda Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya wakilta ya ce, Gwamnatin Tarayya ta yi matuƙar alhini da rasuwar Mama Eunice. Yadda kifewar kwale-kwale ya yi ajalin mutane 26 a Sakkwato Ya ce, a zahiri ana ganin kyawawan ayyukan…
Read More
Yadda kifewar kwale-kwale ya yi ajalin mutane 26 a Sakkwato

Yadda kifewar kwale-kwale ya yi ajalin mutane 26 a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mutane 26 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da ake ci gaba da neman wasu, bayan kifewar kwale-kwale a kogin Shagari da ke Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato. Shugaban Ƙaramar Hukumar Shagari, Aliyu Ɗantani, wanda ya shaida haɗarin ga Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN, a Laraba a Sakkwato, ya ce lamarin ya faru ne a yammacin Talata. An cafke Ba’amurke ɗauke da bindigogi da alburusai a filin jirgin Nijeriya Ɗantani ya ce daga cikin gawarwakin 26 da aka gano, 21 mata ne yayin da biyar kuma ƙananan yara, ya ƙara da cewa…
Read More
An cafke Ba’amurke ɗauke da bindigogi da alburusai a filin jirgin Nijeriya

An cafke Ba’amurke ɗauke da bindigogi da alburusai a filin jirgin Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Wani Ba'amurke da ya shigo Nijeriya ɗauke da muggan bindogogi ya shiga hannun jami'an kula da bodar Nijeriya a filin sauka da tashin jirage na Murtala Muhammed dake jihar Legas. Shi dai wannan fasinja ya shigo ƙasar Nijeriya ne ta cikin wani jirgi wanda ya taho daga garin Houston na Amurka, inda jirginsu ya sauka a Nijeriya ƙarfe 10 da mintuna goma na safiya.  Makaman da ya shigo da su sun haɗa da, muggan bindigogi guda biyu (babba da ƙarama) da tulin albirusai waɗanda ya vioye cikin hikima a  kayansa.  A wata uku ‘yan bindiga sun…
Read More
Ya zuwa yanzu Amurka ta kau da kai daga abin baƙin ciki da ke faruwa a cikin gidanta

Ya zuwa yanzu Amurka ta kau da kai daga abin baƙin ciki da ke faruwa a cikin gidanta

Daga CMG HAUSA Kwanan baya, shehun malama a fannin ilmin doka Amy Wax daga jami’ar Pennsylvania ta ƙasar Amurka, ta soki Amurkawa ‘yan asalin Indiya a cikin wani shirin gidan telibijin na Fox News, inda ta ce, ƙasarsu ta kasance abin kunya. Kalamanta sun girgiza mutane sosai, kuma wani misali ne na yadda ake nuna bambanci ga Amurkawa ‘yan asalin ƙasashen Asiya a ƙasar Amurka. Sin kullum Amurka ba ta kan yi shelar nuna daidaito a tsakanin kowa da kowa ba? Me ya sa Wax ta nuna wariyar launin fata a fili? Yau Jumma’a hukumar nazarin haƙƙin dan Adam ta…
Read More
Rahoto ya nuna yadda ake samun ƙaruwar nuna wariya ga ’yan Asiya a Amurka

Rahoto ya nuna yadda ake samun ƙaruwar nuna wariya ga ’yan Asiya a Amurka

Daga CMG HAUSA Ƙungiyar nazarin haƙƙin bil adama ta ƙasar Sin ta fidda rahoto a yau Juma’a, wanda ke nuna cewa, ana samun ƙaruwar nuna wariya ga al’ummu ’yan asalin Asiya a ƙasar Amurka. A cewar rahoton, har yanzu Amurka tana tinkaho da matsayinta na ƙasa mai hallayar nuna fifiko a tsakanin Amurkawa farar fata mafiya rinjaye, da sauran kananan ƙalibun ƙasar. An buɗe baje kolin Canton Fair ta yanar gizo cikin yanayi na yaƙi da annobar COVID-19 Rahoton ya ce, Amurkawa ’yan asalin Asiya, da Amurkawa ’yan asalin Afrika, da ’yan Latino da kuma Amurkawa ’yan asalin Indiya, suna…
Read More
An buɗe baje kolin Canton Fair ta yanar gizo cikin yanayi na yaƙi da annobar COVID-19

An buɗe baje kolin Canton Fair ta yanar gizo cikin yanayi na yaƙi da annobar COVID-19

Daga CMG HAUSA An bude baje kolin hajojin da ake shigowa da wadanda ake fitarwa daga ƙasar Sin ko “Canton Fair” a yau Juma’a ta yanar gizo, cikin yanayi na yaki da annobar COVID-19. Baje koli na kwanaki 10, a bana ya hallara sama da masu baje hajoji na cikin ƙasar Sin da na waje har 25,500. Masu baje kolin za su samu hidimomin yanar gizo daban daban, kamar nuna hajoji ta yanar gizo, da musayar damar kasuwanci, da kuma ƙaddamar da hajoji. Rahoto ya nuna yadda ake samun ƙaruwar nuna wariya ga ’yan Asiya a Amurka A cewar kakakin…
Read More
Izala ta ƙaddamar da gidauniyar neman taimakon Naira miliyan 30 a Kano

Izala ta ƙaddamar da gidauniyar neman taimakon Naira miliyan 30 a Kano

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano Ƙungiyar Jama'atu Izatul Bid'a wa Iƙamatus Sunnah mai helkwata a garin Jos, wadda kuma Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ke jagoranta, ta buɗe gidauniyar neman taimakon kuɗi Naira miliyan 30 a Kano don gudanar da ayyukan ƙungiyar. Shugaban Majalisar Malamai na Izalar Jos, Sheik Sani Sharif Umar Bichi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi wurin taron ƙaddamar da gidauniyar neman taimakon kuɗin don taimakon addinin Musulunci wanda ya haɗa da samar da hedikwatar ƙungiyar mai haɗe da masallaci da makaranta a Kano. Sai kuma ciyarwa da hidimar tafsirin azumin Ramadan don faɗakar da…
Read More
Ganduje ya ƙara kasafin kuɗin Jihar Kano don kula da lafiyar mata da yara

Ganduje ya ƙara kasafin kuɗin Jihar Kano don kula da lafiyar mata da yara

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin jihar Kano ta ƙara kasafin kuɗin zuwa miliyan 100 ga ɓangaren mace-macen mata masu haihuwa, domin inganta lafiyar mata da ƙananan yara. Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Aminu Tsanyawa ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai a bikin  ranar kula da lafiyar mata ta duniya da ake gudanarwa duk ranar  11 ga Afrilu, da aka yi a Litinin da ta gabata,Kwamishina ya ce gwamnati ta ƙara kasafin  ne domin amfanin mata da ƙananan yara daga miliyan 20 a 2015 zuwa Miliyan 100 a 2022. Ganduje ya ƙi amincewa da buƙatar shugaban…
Read More
Nijeriya ta naɗa Salisu Yusuf sabon kociyan Super Eagles

Nijeriya ta naɗa Salisu Yusuf sabon kociyan Super Eagles

Daga WAKILINMU Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF), ta sanar da naɗa Salisu Yusuf a matakin sabon kociyan Super Eagles ta gida da ke buga gasar CHAN. Haka kuma zai ja ragamar tawagar matasan ƙasar ta 'yan ƙasa da ke buga wasannin Olympics. Yusuf ya taɓa jan ragamar Super Eagles B a gasar kofin Afirka ta 'yan wasa da ke taka leda a gida a Morocco, inda Nijeriya ta yi ta biyu a 2018. Kamar yadda NFF ta sanar a shafinta a Intanet ranar Alhamis ta ce zai yi aiki tare da Kennedy Boboye da Fatai Osho da Abubakar Bala…
Read More
Sabbin shugabannin APC za su yi taronsu na farko a Afrilu

Sabbin shugabannin APC za su yi taronsu na farko a Afrilu

Daga BASHIR ISAH Kwamitin Shugabanni na Ƙasa na jam'iyyar APC, ya tsayar da ranar 20 ga Afrilu a matsayin ranar da zai yi taro don tsara jadawali da kuma shiryen-shiryen fid da gwani na zaɓen 2023. Sakataren yaɗa bayanai na jam'iyyar na ƙasa, Mr Felix Morka ne ya sanar da hakan ranar Juma'a a Abuja. Ya ce taron zai gudana ne a zauren taro na otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja, tare da cewa a wajen taron ne jam'iyyar za ta yi nazarin 'yan takaran da za su tsaya zaɓe a 2023 ƙarƙashin APC. Morka ya ce, “La'akari da…
Read More