Editor

9513 Posts
A wata uku ‘yan bindiga sun kashe mutum 3,000 a Nijeriya – Bincike

A wata uku ‘yan bindiga sun kashe mutum 3,000 a Nijeriya – Bincike

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wani rahoton binciken da aka gudanar a Nijeriya ya ce mutane 2,968 'yan bindiga suka kashe a jihohin Neja da Kaduna da Zamfara a cikin watanni 3, yayin da aka yi garkuwa da wasu 1,484. Binciken da ƙungiyar sanya ido akan harkokin tsaron Nijeriya ta gudanar da ake kira ‘Nigeria Security Tracker’ ya ce mutanen da ake kashewa a yankin Arewa maso Yamma ya zarce wanda ake yi a kowanne sashe. Rahotan binciken ya ce 'yankin Arewa ta tsakiya ita ce ta biyu wajen kashe-kashen, inda ta yi asarar mutane 984, sai kuma Arewa maso…
Read More
Caji ba bisa ƙa’ida ba: fiye da masu ajiya 2000 sun koka da bankuna

Caji ba bisa ƙa’ida ba: fiye da masu ajiya 2000 sun koka da bankuna

Daga AMINA YUSUF ALI Fiye da masu ajiya 2,256 ne suka shigar da koken su zuwa ga ƙungiyar Ma'aikatan bankuna(CIBN), game da yadda bankuna suke cirar musu kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba. Kuɗaɗen da ake zargin an cirar wa kwastomomi masu ƙorafin sun kama har Naira biliyan 368.9 da Dala miliyan $428.7 wato dai-dai da Naira 177.05. Waɗannan bayanai suna ƙunshe a cikin rahoton shekarar 2021 da ƙungiyar ta  saki a ranar Asabar ɗin da ta gabata, jim kaɗan bayan kammala babban taronta na shekara-shekara a jihar Legas.  Shugaban ƙungiyar ta CIBN, Dakta. Bayo Olugbemi shi ne ya jagoranci taron wanda ya…
Read More

Kare ’yan Nijeriya daga ’yan ta’adda

Duk da cewa batun tsaro shi ne babban abin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta sa a gaba, amma ’yan Najeriya masu bin doka da oda a yanzu suna rayuwa cikin fargaba fiye da kowane lokaci a tarihin ƙasar. Mutanenmu sun dogara sosai kan tafiye-tafiye don samun abin rayuwa, amma abubuwan da suka faru a cikin makonnin da suka gabata sun nuna cewa tafiye-tafiyen ya zama wani abu mai hatsarin gaske a halin yanzu. Ta'addancin ’yan bindiga na neman zarce na ƙungiyar Boko Haram/ISWAP a matsayin babban hatsarin da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin ’yan Nijeriya. A cikin makonnin…
Read More
Ashe Osinbajo ba ɗan Tinubu ba ne?

Ashe Osinbajo ba ɗan Tinubu ba ne?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Mazauna Legas dai sun san sunan mataimakin shugaban Nijeriya mai ci Yemi Osinbajo gabanin zaven 2015 amma a gaskiya yawancin mutanen Nijeriya sai lokacin da shugaba Buhari ya canko shi ya zama ma sa mataimakin ɗan takara sannan ne sunan sa ya fito a ka san shi. Hakanan wasu musamman ’yan Arewa ba sa iya ambatar sunan sa sosai sai ka ji sun ce OSIBANJO maimakon OSINBAJO. In ka ɗebe tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, a dimokuraɗiyyar Nijeriya ba wani mataimakin shugaba da ya daɗe kan kujera irin Osinbajo. Gabanin zaman sa mataimakin shugaban Nijeriya,…
Read More
Tashar ruwan ciniki cikin ‘yanci ta Hainan ta shaida ƙaruwar buɗe ƙofa ta ƙasar Sin ga ƙasashen waje

Tashar ruwan ciniki cikin ‘yanci ta Hainan ta shaida ƙaruwar buɗe ƙofa ta ƙasar Sin ga ƙasashen waje

Daga CMG HAUSA “Ba za a rufe ƙofar da aka buɗe ba, maimakon haka za a kara buɗewa”, wannan shi ne babban alƙawarin da ƙasar Sin ta ɗauka ga duniya. Ci gaban da aka samu na gina tashar ruwan ciniki cikin 'yanci ta Hainan a cikin shekaru huɗu da suka gabata, ya zama wani misali na ƙudurin ƙasar Sin na cika alƙawuran da ta dauka. A ranar 12 ga watan Afrilu, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, wanda ke ziyarar aiki a lardin Hainan, ya ziyarci yankin raya tattalin arziki na Yangpu, don fahimtar yadda yankin ke samun bunƙasuwa, inda aka…
Read More
Li Keqiang: Sin za ta rungumi salon cigaba bisa daidaito a fannin cinikayyar waje

Li Keqiang: Sin za ta rungumi salon cigaba bisa daidaito a fannin cinikayyar waje

Daga CMG HAUSA Firaministan ƙasar Sin Li Keqiang ya ce, gwamnatin Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofin bunƙasa cinikayyar waje, a matsayin ɗaya daga ginshikan daidaitawa, da inganta rayuwar alummar ƙasar. Hakan dai sakamako ne na taron majalissar gudanarwar ƙasar Sin, wanda firaminista Li Keqiang ya jagoranta a jiya Laraba. Kaza lika taron ya amince da buƙatar aiwatar da manufar tallafawa hada-hadar fitar da hajoji zuwa ƙetare, domin bunƙasa cinikayyar waje ta Sin. Har ila yau, an amince da aiwatar da matakan daƙile tasirin annobar COVID-19, da bunkasa farfadowa da ci gaban sayayyar hajojin waje. Taron ya…
Read More
Bai kamata manyan ƙasashe su yi ƙasa a gwiwa kan batun kare muhalli ba

Bai kamata manyan ƙasashe su yi ƙasa a gwiwa kan batun kare muhalli ba

Daga SAMINU ALHASSAN Yayin da ƙasashe masu raunin tattalin arziki a sassan duniya daban daban ke ɗanɗana raɗaɗin tasirin sauyin yanayi, wata matsalar dake tunkaro duniya ita ce yadda wasu manyan ƙasashe ke jan kafa wajen sauke nauyin dake kan su na ba da tallafin kare muhalli. A wasu yankunan karkarar ƙasar Kenya ga misali, mutane na fuskantar mummunan yanayin fari. Wasu yankunan ma sun shafe shekaru 2 ba tare da samun ruwan sama ba, sakamakon haka tsirrai da dabbobi sun mutu kana al’ummu da yawansu ya kai miliyan 4 za su buƙaci agajin abinci cikin watanni masu zuwa. Baya…
Read More
Harin Filato: Tilas maharan su fuskanci hukunci – Buhari

Harin Filato: Tilas maharan su fuskanci hukunci – Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce wajibi ne maharan da suka kai mummunan hari a ƙauyukan Kanam da Wase a jihar Filato su fuskanci hukuncin abin da suka aikata, tare da bayyana harin a matsayin ƙololuwar ƙeta ga jama'a. Mai Magana da Yawun Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya bayar a ranar Talata. Shehu ya ce, Buhari ya bada umarnin “Kada a sassauta musu, kuma babu yafiya." KARANTA: INEC ta gano rijistar katin zaɓe mara kyau sama da miliyan 1.3 Ya ƙara da cewa, Buhari ya umurci hukumomin da lamarin ya shafa…
Read More
Gidauniyar IDDEF ta aza harsashin gina kwalejin ilimi a Kano

Gidauniyar IDDEF ta aza harsashin gina kwalejin ilimi a Kano

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano A ƙoƙarin da ta ke yi na samar da ilimi da bunƙasarsa a ƙasashen Musulmi na duniya, Gidauniyar ‘Insana Deger Veren Demekler Foundation’ wato IDDEF a ƙarƙashin Cibiyar Bincike da Samar da Ilimi ta Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, wato ‘Sheikh Muhammad Nasiru Kabara Research Center’, ta ƙaddamar da bikin aza harsashin gina kwalejin ilimi mai suna ‘Sheikh Muhammad Ifandi International College’ domin samar da ingantaccen ilimin addini da na zamani a tsakanin al'ummar Musulmi da ke Jihar Kano da sauran wasu yankuna da ke kusa da ita. Taron wanda aka gudanar a ranar Asabar ɗin…
Read More
Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga BBC Hausa

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga BBC Hausa

Daga ABDULAZIZ TIJJANI (PHD) A duk yayin da ya kasance mutum ko wata kafar sadarwa tana da mabiya da yawa, to ya zama wajibi wannan mutumin ko kafar sadarwar su yi taka tsan-tsan wurin isar da saƙwanninsu. Tashar BBC Hausa tasha ce mai matuƙar tasiri ga rayuwar al’ummar Hausawa a faɗin Duniya ta fuskar ilimantarwa da yaɗa labarai da al’adun da suka shafi ƙabilar Hausawa. Amma ko shakka babu a waɗannan kwanakin alamu sun nuna cewa tashar tana buƙatar gyara al’amuranta ta yadda shirye-shiryenta zasu riƙa kawo gyara, ba lalacewar al’umma ba. A kwanakin baya ne dai BBC Hausa a…
Read More