Editor

9513 Posts
An yanke wa matar aure hukuncin sharar kotu kwana biyar a Kaduna

An yanke wa matar aure hukuncin sharar kotu kwana biyar a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Alƙalin Kotun Majistare, Ibrahim Emmanuel, jiya Alhamis ya umarci wata matar aure mai suna Hadiza Ahmed da ta share harabar kotun na tsawon kwanaki biyar saboda ta yi wa makwabciyar ta duka. Emmanuel, ya bada umarnin ne biyo bayan amsa laifin da Hadiza Ahmed ɗin ta yi. Kotu ta tabbatar da tuhuma bakwai kan Nnamdi Kanu “An umarce ki da ki share tare da tsaftace harabar kotun nan na tsawon kwanaki biyar a ƙarƙashin bibiyar magatakardan kotun. "Hukuncin zai zama izina ga wasu da ba sa son zaman lafiya da maƙwabta," in ji shi.…
Read More
Marafa ya ƙaryata komawarsu PDP

Marafa ya ƙaryata komawarsu PDP

Daga BASHIR ISAH Sanata Kabiru Marafa ya ƙaryata rahoton da ke nuni shi da tohon gwamnan Zamafara, Abdulaziz Yari sun sauya sheƙa sun koma jam’iyyar hamayya ta PDP. A rana Lahadi aka jiyo shugaban PDP na jihar Zamfara na cewa sun cimma jarjeniniya tare da waxanda lamarin ya shafa tare da cewa nan bada daxewa ba za su bayyana komawarsu PDP a hukumance. Yari da Marafa sun sauya sheƙa zuwa PDP A kan haka ne Sanata Marafa ya ce, “Abin da muka sani shi ne muna kan tattaunawa da jam’iyyun siyasa da dama wadanda suka buqaci mu shigo cikinsu a…
Read More
Kano 2023: Zan yi takara ba gudu ba ja da baya – Sheikh Ibrahim Khalil

Kano 2023: Zan yi takara ba gudu ba ja da baya – Sheikh Ibrahim Khalil

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Shugaban Majalisar Malamai na Kano da Arewacin Nijeriya, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce, babu gudu babu ja da baya kan batun tsaya wa takararsa wajen neman gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin tutar jam'iyyar ADC a zaɓen 2023 mai zuwa. Sheik Khalil ya bayyana haka ne lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a gidan tunawa da Malam Aminu Kano, wato Gidan Mumbayya, dake Unguwar Gwammaja a ƙaramar Hukumar Dala a Birnin Kano. Kakakin Majalisar Bauchi ya yi wa APC sakin da babu komeYari da Marafa sun sauya sheƙa zuwa PDP Shehin malamin ya bayyana…
Read More
Kakakin Majalisar Bauchi ya yi wa APC sakin da babu kome

Kakakin Majalisar Bauchi ya yi wa APC sakin da babu kome

Daga BASHIR ISAH Kakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Abubakar Y. Sulaiman ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyya mai mulki a jihar, PDP. Da yammacin Asabar da ta gabata Sulaiman ya bayyana ficewar tasa a fadar gwamnatin jihar a lokacin da suke buɗa baki tare da Gwamna Bala Mohammed da wasu ƙusoshin PDP daga yankunan ƙananan hukumomin Ningi, Toro, Warji da kuma Dass a jihar. Abubakar Sulaiman ya ce ya yanke shawarar komawa tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP ne saboda kyakkyawar fahimta da kuma jin daɗin aiki tare da Gwamna Bala, kana ya yi alƙawarin ci gaba da yin aiki…
Read More
Yari da Marafa sun sauya sheƙa zuwa PDP

Yari da Marafa sun sauya sheƙa zuwa PDP

Daga BASHIR ISAH Tsohon Gwmanan Jihar Zamfara, Abdul’azeez Yari tare da wasu jiga-jigan APC a jihar irin su Sanata Kabiru Marafa da sauransu haɗe da magoya bayansu, sun sauya sheƙa zuwa babbar jam'iyyar hamayya ta PDP. Shugaban PDP na jihar, Bala Mande ne ya bayyana hakan sa'ilin da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi. Tinubu da Osinbajo: Wa zai kai wani ƙasa a APC? Da yake jawabi Mande ya ce, “'Yan jarida, mun kira ku ne don mu shaida muku cewa tsohon Gwamnan Zamfara, Alhaji Abdul Aziz Yari da Sanata Kabiru Garba Mafara da danzon magoya bayansu sun dawo…
Read More
Sin ta fara aikin gina wuri mai sanyi don adana rigakafi a Masar

Sin ta fara aikin gina wuri mai sanyi don adana rigakafi a Masar

Daga CMG HAUSA Kamafin Sinovac na ƙasar Sin ya fara aikin gina wuri mai sanyi don adana alluran riga-kafi a wannan mako, ofishin jakadancin ƙasar Sin a Masar ya bayyana hakan cikin wata sanarwa. Liao Liqiang, jakadan ƙasar Sin a ƙasar Masar, ya bayyana a wajen bikin ƙaddamar da fara aikin a ranar Alhamis cewa, ta hanyar tallafin kamfanin hada magungunan na ƙasar Sin, manyan dakuna masu sanyin za su taimaka wa ƙasar Masar wajen inganta aikin adana riga-kafin. A cewar jakadan, wurin ajiyar mai faɗin murabbi’in mita 2,800, yana da girman da zai iya ɗaukar alluran riga-kafi miliyan 150…
Read More
Ana jigilar manyan ƙarafun gadar Cocody daga Sin zuwa Kwadibuwa

Ana jigilar manyan ƙarafun gadar Cocody daga Sin zuwa Kwadibuwa

Daga CMG HAUSA Jiya Asabar 16 ga wata, jirgin ruwa dakon kaya na farko ya kwashi manya ƙarafuna guda 37 waɗanda za a yi amfani da su domin aikin gina gadar Cocody ta ƙasar Kwadibuwa, gadar mai madaurai mafi girma a yankin yammacin Afirka, ya tashi daga tashar ruwan kogin Yangtse dake birnin Nantong na lardin Jiangsu na kasar Sin, zuwa ƙasar ta Kwadibuwa. Gadar Cocody mai tsawon mita 630, muhimmin aiki ne na haɗin gwiwa a tsakanin kasar Sin da ƙasashen Afirka, idan aikin ya kammala, wanda kamfanin ƙasar Sin ke gudanarwa, za ta kasance gada mai madaurai mafi…
Read More
Har yanzu ana keta ƙa’idojin da ƙasashen Asiya da Afirka suka gabatar

Har yanzu ana keta ƙa’idojin da ƙasashen Asiya da Afirka suka gabatar

Daga CMG HAUSA A ranar 18 ga watan Afrilun shekarar 1955, tawagogin gwamnatocin wasu ƙasashen dake nahiyoyin Asiya da Afirka 29, da suka haɗa da Afghanistan, da Sin, da Masar, da Habasha, da Laberiya, da India, da dai sauransu, sun gudanar da wani taro na musamman, a Bandung na ƙasar Indonesia, domin tattauna batun haɗin gwiwarsu, da na yaƙi da manyan ƙasashe masu mulkin danniya, inda suka gabatar da wasu ƙa’idoji guda 10, waɗanda ya kamata dukkan ƙasashe su yi ƙoƙarin binsu, don tabbatar da samun zaman lafiya a duniya, da ƙarfafa hadin kai tsakanin ƙasashe daban daban. Sai dai…
Read More
Kamfanin gandun dajin Sin zai dasa bishiyoyi Hekta 40,000 a duk ƙasar

Kamfanin gandun dajin Sin zai dasa bishiyoyi Hekta 40,000 a duk ƙasar

Daga CMG HAUSA Kamfanin kula da gandun daji na ƙasar Sin ya sanar cewa, zai shuka itatuwa da za su kai girman hekta 40,267 a faɗin ƙasar a wannan shekara ta 2022. A cewar kamfanin, zai gudanar da aikin dashen itatuwa mafi girma da sauran ayyukan dake shafar kula da itatuwa bisa dacewa da yanayin yankunan ƙasar. Ƙasar Sin na adawa da amfani da batutuwan da suka shafi haƙƙin ɗan Adam wajen matsawa wasu ƙasashe lamba A matsayinsa na wani babban kamfani mallakin gwamnatin ƙasar a fannin kula da gandun daji, kamfanin kula da gandun dajin, ya samu ribar da…
Read More
Mbappe na tantamar rattaɓa hannu a yarjejeniyarsa da Madrid

Mbappe na tantamar rattaɓa hannu a yarjejeniyarsa da Madrid

Kylian Mbappe zai zama ɗan wasan Real Madrid a kakar wasa mai zuwa, amma sai dai idan ba a samu sauyin yanayi ba, abu ne mai matuƙar wuya hakan. Sai dai har yanzu ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint-Germain tana fatan riƙe ɗan wasan na Faransa wanda ya ƙi saka hannu kan sabon kwantaragi kan ‘Los Merengues’. Kylian Mbappe da Real Madrid za su haɗu a kakar wasa mai zuwa. Komai yana nuna cewa tauraron ɗan wasan zai isa Bernabeu a matsayin kyauta. Sai dai har yanzu PSG na da kwarin gwiwar cewa za ta iya shawo kan Mbappe. A…
Read More