Editor

9513 Posts
Azumin bana: Ga talauci ga tsadar kayan masarufi

Azumin bana: Ga talauci ga tsadar kayan masarufi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Watan Ramadan dai shi ne wata na tara a lissafin watannin Musulunci kuma yana daga cikin watanni masu alfarma. Hasali ma a cikinsa ne aka saukar da Alƙur'ani mai girma, wanda ya ƙunshi dukkan hukunce-hukuncen addinin Islama. Shi dai azumi shi ne kamewa daga cin abinci ko sha da kuma jima'i, haka kuma ana son mai azumi ya ƙara kamewa daga barin duk wani zance na alfasha ko kuma aikata zunubi. A na daina cin abinci ko sha ne tun daga fitowar alfijir har faɗuwar rana. Wannan ya sanya yawaitar buƙatuwa da abin kai wa…
Read More
Gwamnati ta bayyana musabbabin rashin samun wutar lantarki a ƙasa

Gwamnati ta bayyana musabbabin rashin samun wutar lantarki a ƙasa

Daga BASHIR ISAH Gwmnatin Tarayya ta bayyana cewa matsalar ƙarancin wutar lantarki da 'yan ƙasa ke fuskanta a baya-bayan nan hakan ya faru ne saboda ayyukan wasu ɓatagari. Cikin sanarwar manema labarai da ta fitar a ranar Asabar, Ma'aikatar Lantarki ta Ƙasa ta ce lalata babban layin lantarki na Odukpani zuwa Ikot Ekpene mai karfin 330kV da wasu ɓatagari suka yi hakan ya sa ƙarfin lantarkin da ake samar wa ƙasa ya ragu da 400MW wanda hakan shi ne dalilin fuskantar matsalar rashin wutar lantarki a faɗin ƙasa a baya-bayan nan. Mai taimaka wa Ministan Lantarki kan harkokin yaɗa labarai,…
Read More
An gudanar da taron kwamitin haɗin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya

An gudanar da taron kwamitin haɗin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya

Daga CMG HAUSA An gudanar da taro karo na 7 na kwamitin haɗin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya, kan harkokin tattalin arziki da cinikayya da fasahohi, a jiya Juma’a. Kwamitin ya gudanar da taron ne ta kafar bidiyo ƙarƙashin jagorancin mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin Qian Keming da ministar kuɗi da tsare-tsare ta Nijeriya, Zainab Ahmed. Jakadan ƙasar Sin Cui Jianchun da mambobin kwamitin daga ƙasashen biyu ne suka halarci taron ta kafar intanet. Ƙasashen biyu sun waiwayi kyawawan nasarori da suka cimma a haɗin gwiwarsu da ya shafi ciniki da zuba jari da ababen more rayuwa, inda kuma…
Read More
Tawagar jami’an lafiya na ƙasar Sin ta bayar da gudunmuwar kayayyakin lafiya a ƙasar Saliyo

Tawagar jami’an lafiya na ƙasar Sin ta bayar da gudunmuwar kayayyakin lafiya a ƙasar Saliyo

Daga CMG HAUSA Tawagar jami’an lafiya na ƙasar Sin dake aiki a Saliyo, ta samar da gudunmuwar kayayyakin lafiya ga asibitin sada zumunta na Sin da Saliyo, domin bunƙasa hidimomin kiwon lafiya. Shugaban tawagar Zhou Xi, ya ce kayyakin sun haɗa da rukunoni 24 na magungunan da ake buƙata sosai da sama da nau’o’i 30 na kayayyakin aiki, waɗanda za su taimaka wajen cike gibin ƙarancin kayayyakin lafiya dake akwai a asibitin. A cewar Zhou Xi, asibitin, wanda a nan ne tawagar ta ƙasar Sin ke aiki, ya dade yana fuskantar ƙarancin kayayyaki da wutar lantarki da ruwa, wadanda ke…
Read More
An buɗe taron ministocin kuɗi da gwamnonin manyan bankunan ƙasashe mambobin BRICS karo na fatko a shekarar 2022

An buɗe taron ministocin kuɗi da gwamnonin manyan bankunan ƙasashe mambobin BRICS karo na fatko a shekarar 2022

Daga CMG HAUSA An gudanar da taron farko a bana, na ministocin kuɗi da gwamnonin manyan bankunan ƙasashe mambobin ƙungiyar BRICS ta kafar bidiyo, a jiya Jumma’a . Taron mai taken "Raya dangantakar abota mai inganci don ƙirƙirar sabon zamanin ci gaban duniya", ya tattauna kan batutuwan da suka shafi yanayin tattalin arziki da daidaita manufofi, da sabon bankin raya ƙasa, da zuba jari kan ababen more rayuwa, da cibiyoyin binciken masana a fannin kuɗi na BRICS da dai sauransu. Kana an yi musayar ra'ayi kan sakamakon da ake sa ran samu daga haɗin gwiwar hada-hadar kuɗi tsakanin ƙasashen BRICS…
Read More
Buhari bai tafi London ba – Bashir Ahmad

Buhari bai tafi London ba – Bashir Ahmad

Daga BASHIR ISAH An labarin da ke nuni da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi hutun kwana 20 a London, hakan ba gaskiya ba ne. A yau ne dai aka ga wani rahoto kan tafiyar Buhari zuwa hutun kwana ashirin a London ya karaɗe kafafen sadarwa. Sai dai a cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai taimaka wa Shugaba Buhari kan sha'anin kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad ya ƙaryata labarin. Yana mai cewa, lallai Shugaba Buhari yana Abuja bai tafi ko'ina ba, kuma babu wani shiri a kan zai tafi London.
Read More
Ƙasar Sin na adawa da amfani da batutuwan da suka shafi haƙƙin ɗan Adam wajen matsawa wasu ƙasashe lamba

Ƙasar Sin na adawa da amfani da batutuwan da suka shafi haƙƙin ɗan Adam wajen matsawa wasu ƙasashe lamba

Daga CMG HAUSA Dangane da matakin da babban taron MDD ya ɗauka, na dakatar da Rasha daga zama mamba a kwamitin kare haƙƙin bil Adama na MDD, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya jaddada matsayin ƙasarsa a taron manema labarai da aka saba gudanarwa a Jumma’ar da ta gabata, inda ya jaddada cewa, ƙasar Sin tana adawa da siyasantar da batutuwan da suka shafi haƙƙin ɗan Adam, da nuna adawa da yin zaɓe, da nuna kiyayya, kuma bisa amfani da ma’auni biyu kan batutuwan, kana da adawa da amfani da batutuwan haƙƙin dan Adam…
Read More
Elon Musk ya sama wa Tiwita ribar shekara huɗu cikin kwana ɗaya da sayen hannun jarinsa

Elon Musk ya sama wa Tiwita ribar shekara huɗu cikin kwana ɗaya da sayen hannun jarinsa

Daga AMIN YUSUF ALI Mutumin da ya fi kowa arziki a Duniya, Biloniya Elon Musk ya ƙara samar da riba mai yawa ga kamfanin Tiwita jim kaɗan bayan sayen hannun jari a kamfanin na  Tiwita. Attajiri Elon Musk ya samar da gwaggwaɓar riba har ta dalar Amurka guda Kwatankwacin Naira Biliyan 580 bayan awanni ashirin da huɗu da sayen hannun jarin Kamfanin Tiwita na kaso 9.2%. A cewar ƙididdigar Jaridar Ingilishi ta kasuwanci, Bloomberg Mutumin da ya fi kowa arziki ya samu ribar dalar Amurka guda bayan samun shiga da zama ɗaya daga cikin mamallakan Kamfanin nan na sada zumunta…
Read More
Matsalar tsaro ta fi ƙarfin Buhari – Obasanjo

Matsalar tsaro ta fi ƙarfin Buhari – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana rashin tsaron da ya ke addabar ƙasar a matsayin 'babbar matsala' da ta fi ƙarfin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kuma ya ce ya kamata masu ruwa da tsaki su haɗa ƙarfi da ƙarfe, domin magance matsalar. Tsohon shugaban ya furta kalaman ne a ɗakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke Abeokuta a jihar Ogun, yayin da ya ke karɓar Dakta Ugochukwu Williams, ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar PDP da tawagarsa. Tsohon shugaban ya ce matsalar tsaron ta gagari gwamnatin Muhammadu Buhari. "Idan wani…
Read More
Matakan ƙasar Sin na daƙile COVID-19 sun tabbatar da gudanar wasannin Olympics ba lokacin hunturu na Beijing cikin aminci

Matakan ƙasar Sin na daƙile COVID-19 sun tabbatar da gudanar wasannin Olympics ba lokacin hunturu na Beijing cikin aminci

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a yau Juma’a cewa, ingantattun matakan kandagarki da dakile yaduwar COVID-19 da ƙasar Sin ta dauka, sun tabbatar da karbar baƙunci da gudanar wasannin Olympics na lokacin hunturu da irinsa na nakasassu na 2022, da aka yi a Beijing, cikin aminci ba tare da wata tangarɗa ba. Xi Jinping ya bayyana hakan ne yau, yayin wani taro don girmama waɗanda suka bada muhimmiyar gudunmawa ga gudanar wasannin 2 na Olympics na Beijing na lokacin hunturu na 2022 cikin nasara. A cewar shugaban, duk da mummunan tasirin COVID-19 da ake fuskanta…
Read More