Editor

9513 Posts
Bankin raya ƙasar Sin ya yi matuƙar taimaka wa ci gaban makamashi mai tsafta a rubu’in farkon bana

Bankin raya ƙasar Sin ya yi matuƙar taimaka wa ci gaban makamashi mai tsafta a rubu’in farkon bana

Daga CMG HAUSA Bankin raya ƙasar Sin (CDB), ya ninka kuɗaɗen tallafawa ayyukan samar da makamashi mai tsafta a rubu’in farko na wannan shekarar da muke ciki. A cewar bankin na CDB, ya fidda rancen kuɗi da yawansa ya kai kuɗin Sin RMB yuan biliyan 109, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 17.12, domin tallafawa ci gaban makamashi mai tsafta, da sauya fasalin samar da makamashin da aka saba amfani da su zuwa hanyar kaucewa gurɓata muhalli. A cikin rubu’in farko na wannan shekara, an samar da rancen kuɗi da ya kai jimillar yuan biliyan 76.5 domin gudanar da ayyukan bunƙasa samar…
Read More
An gudanar da taron tattaunawa kan al’adun Sin da Afirka karo na farko

An gudanar da taron tattaunawa kan al’adun Sin da Afirka karo na farko

Daga CMG HAUSA A jiya ne, aka gudanar da taron tattaunawa kan al’adun Sin da Afirka karo na farko mai taken “sa kaimi ga raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a sabon zamani ta hanyar mu’amalar al’adun juna”, wanda kwalejin ilmin zamantakewar al’umma ta Sin, da kwalejin nazarin Afirka na ƙasar Sin, da kuma ofishin ƙungiyar AU dake kasar Sin suka ɗauki nauyin shiryawa. A wajen taron, babban sakataren kwalejin ilmin zamantakewar al’umma na ƙasar Sin Zhao Qi, ya yi nuni da cewa, an gudanar da taron tattaunawar cikin nasara, wanda ya kasance sabon dandalin yin mu’amalar…
Read More
Tasirin azumi a jikin ɗan adam

Tasirin azumi a jikin ɗan adam

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAH 'Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka da ilmintarwa, da ke kawo muku bayanai game da duniyar jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, ku san yadda jikinku ke aiki.  Barkanmu da wannan lokaci na azumin watan Ramadan; fatan Allah ya karɓi ibadunmu, Aameen.  Kusan duk lokacin da watan azumin Ramadan ya kewayo, ina sadaukar da rubutuna na wannan watan ga bayanai na yadda azumi ke taka rawa a jikin ɗan Adam. To, wannan shekarar ma, Allah ya sake kawo mu!…
Read More
Rikicin Smith da Chris: Oscar Award sun dakatar da Smith shekaru 10

Rikicin Smith da Chris: Oscar Award sun dakatar da Smith shekaru 10

Daga AISHA ASAS Hukuncin da mahukunta suka sha alwashin ɗauka kan jarumi Will Smith game da labta wa Chris Rock mari a bainar jama'a, a ranar bikin karramawa na Oscar Award ya bayyana, inda ƙungiyar ta haramta wa Smith halartar taro irin wannan da ma takwarorinsa na tsawon shekaru goma. A ranar Juma'ar nan da ta gabata ne, masu alhakin shirya gagarumin bikin bayyar da kyauta na Oscar wato Academy of Motion Pictures Arts and Sciences suka bayyana abin da Smith ya aikata a matsayin abin da ba a lamunta da shi ba, kuma ba zai tafi ba tare da…
Read More
Sufuri: Gwamna Buni ya ƙaddamar da sabbin motocin bas 20 a Yobe

Sufuri: Gwamna Buni ya ƙaddamar da sabbin motocin bas 20 a Yobe

Daga MUHAMMAD EL-AMEEN a Damaturu  Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni a ranar Talata ya ƙaddamar da sabbin motoci ƙirar Toyota Hiace masu kujeru 18 guda 20 ga hukumar kula zirga-zurga tare da hukumar kiyaye haɗurra ta YOROTA a jihar. A jawabin Gwamna Buni a lokacin ƙaddamar da motocin ƙirar bus Damaturu, ya ce taron yar manuniya ce dangane da ƙoƙarin da gwamnatin sa ta tsayu dashi wajen inganta harkokin zirga-zurga don jin daɗin al'ummar jihar Yobe. Bugu da ƙari kuma ya ƙara da cewa, ”Wannan mataki ne wanda zai ƙara tabbatar da inganta harkokin zirga-zurga tare da lafiyar…
Read More
‘Yan daba sun kai hari gidan rediyon Ibadan

‘Yan daba sun kai hari gidan rediyon Ibadan

Daga WAKILINMU ‘Yan daba sun kai hari a wani gidan rediyon da ke Ibadan mai suna Fresh FM, yayin da tashar ke tsaka da gabatar da wani shiri na kai tsaye a safiyar yau Lahadi. Bayanai sun nuna ‘yan daban sun kai hari tashar ne inda suka sace wasu muhimman kayayyakin aiki da suka haɗa da kwamfutoci, wayoyi da wasu kayayyaki mallakar ma’aikatan gidan rediyon. Ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan rediyon ya shaida wa jaridar Punch cewa, da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar wannan Lahadin ɓarayin suka antayo musu. Ya ƙara da cewa, babu hasarar rai kuma babu wanda ya…
Read More
Manufar kamfaninmu ita ce tsamo matasa daga ƙangin talauci – Kwamred Alkamatu

Manufar kamfaninmu ita ce tsamo matasa daga ƙangin talauci – Kwamred Alkamatu

Kamfanin Alkamatu Kamfani ne da ya yi fice a jahar Kano, wajen samar wa da al'umma mafita don dogaro da kai. Sannan suna samar wa da mutane bashi daga bankuna tare da tallafin kuɗaɗe don cigaba da kasuwanci don tsayawa da ƙafafunsu. Wakilin Blueprint Manhaja a Kano, Babangida S. Gora, ya samu tattaunawa da Shugaban kamfanin na Alkamatu Brainbox Solutions, Kwamred Alkamatu Hussain Abdulƙadir. Ga yadda tattaunawar ta kasance.  MANHAJA: Da farko za mu so mu ji da wa mu ke tare.ALKAMATU: Ni Sunana Alkamatu Hussaini Abdulƙadir, Kuma ni ne shugaban wannan kamfani na Alkamatu BrainBox Solutions. Mene ne manufarka…
Read More
Boko Haram sun kashe kwamandojin ISWAP 10 a yankin Tafkin Chadi

Boko Haram sun kashe kwamandojin ISWAP 10 a yankin Tafkin Chadi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Aƙalla mayaƙan ISWAP goma, duk da manyan kwamandojinsu suka rasa rayukansu yayin artabu da abokan hamayyarsu a ta'addancin, Jama'at Ahl as-Sunnah lid- Da'awah wa'l- Jihad, wani nau'in Boko Haram na Arewa maso gabashin tafkin Chadi suka kai musu farmaki.  Zagazola Makama, fitaccen mai bibiyar lamurran ƙungiyoyin ta'addancin ne ya bayyana hakan. Kamar yadda ya ce, 'yan Boko Haram na Buduma sun yi luguden wuta ga ISWAP, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mayaƙan da dama a bakin tafkin dake tsakanin iyakar kogin Kaduna da Kandahar na Jamhuriyar Nijar.  An jefa mayaƙa da dama cikin ruwan,…
Read More
Harin jirgin ƙasa: ’Yan bindiga na barazanar kashe fansinjojin da suka sace

Harin jirgin ƙasa: ’Yan bindiga na barazanar kashe fansinjojin da suka sace

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan bindigan da suka dasa bam a hanyar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, su ka yi awon-gaba da bayin Allah su na barazanar cewa za su kashe mutanen da ke hannunsu.  Jaridar Daily Nigerian ta fitar da faifan bidiyon 'yan bindigar da suka yi garkuwa da Manajan Darakta na Bankin Manoma a Nijeriya, Alwan Hassan, ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu 2022, inda aka ji cewa waɗannan ‘yan ta’addan su na gargaɗin gwamnatin tarayya a lokacin da suka ce za su saki Alwan Hassan ya koma ga iyalansa. A wani gajeren faifen bidiyo da…
Read More
Lambar NIN: Waɗanda aka rufe layukansu su yi tururuwa ofisoshin kamfanonin sadarwa

Lambar NIN: Waɗanda aka rufe layukansu su yi tururuwa ofisoshin kamfanonin sadarwa

Daga AMINA YUSUF ALI Wasu masu amfani da layukan sadarwa sun shiga tsaka mai wuya a ranar Larabar da ta gabata bayan da suka wayi gari kamfanonin sadarwa suka rufe musu layukan waya. Wato aka hana su kiran waya gabaɗaya. Hakan ya biyo bayan umarnin gwamnatin Tarayya na a rufe layin dukkan wanda bai yi rajistar  shaidar ɗan ƙasa (NIN) a layin nasa ba. A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Gwamnatin Tarayya ta ba da umarni ga dukkan kamfanonin sadarwa da su tilasta wa 'yan Nijeriya yin katin shaidar ɗan ƙasa da kuma yin rajistar wayarsu da…
Read More