Editor

9513 Posts
Yan sandan Zamfara sun ceto mutane 39 da aka yi garkuwa da su, sun kama 10 da ake zargi

Yan sandan Zamfara sun ceto mutane 39 da aka yi garkuwa da su, sun kama 10 da ake zargi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau. Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce a yau Litinin ta ceto mutane 39 da aka yi garkuwa da su ‘yan asalin kananan hukumomin Bungudu da Maru dake jihar. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ayuba N. Elkanah ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a yau Litinin. A cewarsa, an sace mutanen ne a watan Maris da farkon watan Afrilu na wannan shekara. Ya Kara da cewa, waɗanda abin ya shafa sun hada da, maza 8, mata 15 ciki har da uwa mai shayarwa da yara 16 waɗanda aka sace a ƙauyuka da wurare…
Read More
Zan ɗora daga inda Shugaba Buhari ya tsaya – Osinbanjo

Zan ɗora daga inda Shugaba Buhari ya tsaya – Osinbanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023. Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana tsayawa takarar ce a wani jawabi ta bidiyo da aka yaɗa ta talabijin, inda ya yi bayanin irin abubuwan da zai yi idan ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari. Ya ce yana neman tsayawa takarar ce domin inganta rayuwar 'yan ƙasar, yana mai cewa a matsayinsa na mataimakin shugaban ƙasa yana da ƙwarewar shugabancin Nijeriya. "A cikin shekara bakwai, na bauta wa gwamnati a matakai daban-daban, kuma bisa umarnin shugaban ƙasa, na wakilci…
Read More
2023: Osinbajo ya bi sahun masu kwaɗayin shugabancin Nijeriya

2023: Osinbajo ya bi sahun masu kwaɗayin shugabancin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana ƙudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa. Osibanjo ya bayyana ƙudirin nasa ne cikin wani taƙaitaccen bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Tiwita. Wannan na zuwa ne kwanaki 89 bayan da ubangidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shi ma ya bayyana aniyyarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin ƙasa. Sa'ilin da yake bayyana ƙudirin nasa, Osinbajo ya ce, "Tare da ƙanƙan da kai, a yau ina mai bayyana ƙudirina na neman ofishin shugaban ƙasar Tarayya Nijeriya a hukumance ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressive Congress (APC). "Idan…
Read More
Wasu magidanta kan rura wutar kishi tsakanin matansu

Wasu magidanta kan rura wutar kishi tsakanin matansu

Daga AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum. Sannun ku da jimirin bibiyar filinku na 'Zamantakewa'. Wanda yake zuwar muku kowanne mako daga jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja.   A wannan makon kuma,  mun zo muku da bayani a kan yadda magidanta ke kara assasa kishi a tsakanin matansu. A sha karatu lafiya.  Da farko dai na san da yawa magidanta za su jinjina kanun bayaninmu na wannan mako. Wasu ma ba za su gaskata cewa magidanci yana iya rura wutar kishi tsakanin matansa ba. Amma maganar gaskiya hakan tana faruwa. Magidanta da yawa da saninsu ko ba saninsu suna taimakawa…
Read More
PDP 2023: Baki ya zo ɗaya a tsakanin ‘yan takarar shugabancin Nijeriya

PDP 2023: Baki ya zo ɗaya a tsakanin ‘yan takarar shugabancin Nijeriya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike a ranar Laraba da ta gabata ne tare da sauran masu neman tsayawa takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP suka yi wata ganawar sirri a tsakanin su a gidan gwamnatin Ribas dake garin Fatakwal. Waɗanda suka halarci ganawar sun haɗa da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, takwaran sa na Jihar Sakkwato, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, da tsohon shugaban Majalisar Dattawa ta Nijeriya, Dokta Abubakar Bukola Saraki, da kuma tsohon shugaban bankin FSB International Bank, Dokta Mohammed Hayatu-Deen. Da yake yi wa manema larabai jawabi jin…
Read More
Gwamna Buni zai tallafa wa matasa 300,000 da kayan sana’a don dogaro da kai

Gwamna Buni zai tallafa wa matasa 300,000 da kayan sana’a don dogaro da kai

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sanar da ɗaukar matakin taimaka wa matasan jihar 300,000 da tallafin sana'o'i don samun abin dogaro da kai tare da yaƙi da talauci a jihar. Gwamna Buni ya bayyana hakan ne a lokacin da al'ummar jihar suka shirya masa gagarumar tarba a babban filin wasa na 27 August Stadium, domin taya shi murnar kammala babban taron jam'iyyar APC a matsayin sa na shugaban riqo kimanin shekaru biyu. A hannu guda kuma, Gwamna Buni ya sha alwashin tallafa wa matasa a faɗin jihar da Keke Napep don inganta rayuwar su…
Read More
An shawarci al’ummar Musulmi su ɗauki matakin kariya daga zafin rana saboda azumi

An shawarci al’ummar Musulmi su ɗauki matakin kariya daga zafin rana saboda azumi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Shugabar Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Unguwar Zoma ta Jihar Kano, Hajiya Mairo Sa'id Muhammad ta sharwarci al'umma akan ɗaukar matakan kariya akan yanayin tsananin zafi da ake fuskanta musamman a cikin watan Ramadan ɗin nan. Ta ce bisa yadda ake samun zafi da ƙwallewar rana a wannan lokaci ya kamata Musulmi su riƙa ɗaukar matakan samun sauƙi wajen gudanar da ibadunsu, musamman ta guje wa shiga rana, saboda tsananin zafi, sannan a lokacin buɗa baki a kauce wa soma amfani da ruwa mai sanyi. Ta ƙara da ce an fi buƙatar a samu ruwa…
Read More
Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta gargaɗi Musulmi da su guji ƙin yin azumin Ramadan da gangan

Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta gargaɗi Musulmi da su guji ƙin yin azumin Ramadan da gangan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta gargaɗi al’ummar Musulmi da su guji ƙin yin azumin watan Ramadan da gangan. A wani saƙon murya ta WhatsApp da ya aika wa manema labarai a Kano, kwamandan hukumar Hisbah na jihar, Haroun Ibn-Sina, ya ce hukumar ba za ta ƙyale duk wanda aka samu yana cin abinci da rana ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba. A cewarsa, hukumar Hisbah ba za ta naɗe hannunta tana ganin yadda matasa Musulmi ke keta hurumin addinin Musulunci a jihar ba, musamman a wannan wata mai alfarma, inda ake buqatar…
Read More
“Manajan Darakta na Bankin Manoma a Nijeriya ya biya ‘yan bindiga fansar Naira miliyan 100”

“Manajan Darakta na Bankin Manoma a Nijeriya ya biya ‘yan bindiga fansar Naira miliyan 100”

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ‘Yan bindigar da suka kai hari kan jirgin ƙasan dake zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna sun karɓi diyyar Naira miliyan 100 kafin sakin shugaban bankin kula da ayyukan noma a Nijeriya Alwan Hassan bayan ya kwashe kwanaki kusan 10 a hannunsu. Jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a yanar gizo ta ce saɓanin faifan bidiyon da ‘yan bindigar suka gabatar cewar sun saki Hassan ne saboda yawan shekarun sa da kuma azumin watan Ramadan, wata majiya kusa da iyalan sa ta tabbatar da cewar sai da suka karɓi maƙudan kuɗi kafin sakin sa. Jaridar…
Read More
Firaministan Sin ya jaddada aniyar haɗin gwiwa da ƙasashe masu magana da harshen Portugal

Firaministan Sin ya jaddada aniyar haɗin gwiwa da ƙasashe masu magana da harshen Portugal

CMG HAUSA Firaministan ƙasar Sin Li Keqiang, ya yi kiran a ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashe masu magana da harshen Portugal. Li ya yi wannan tsokaci ne a yayin da ya halarci bikin buɗe taron musamman na ministoci na dandalin haɗin gwiwar raya tattalin arziki da ciniki na ƙasar Sin da ƙasashe masu magana da harshen Portugal (PSCs), wacce aka fi sani da Forum Macao. Li ya ƙara da cewa, yawan ciniki a tsakanin ƙasar Sin da ƙasashe masu magana da harshen Portugal, ya zarce dalar Amurka biliyan 100 a shekaru biyar a jere, yayin da adadin ya kai dala…
Read More