12
Apr
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Blueprint Manhaja ta yi nazari tare da tattaro bayanai daga masana dangane da labarin rikicin Maitatsine, inda za ta riqa kawo muku labarin sanka-sanka har na tsawon wasu makonni. Maƙasudin rikicin maitatsine ya faru ne a ranar 11/12/1980, wato kusan a ce ya faru ne a unguwar Malafa, Malafa unguwa ce daga gabas, ta yi iyaka da unguwar Fagge wacce ta ke da mashahuran mutane masu Arziki, malamai da ’yan kasuwa da sauransu, misali a ɓangaren masu arziki akwai irinsu Alhaji Garba A.D. Inuwa, da Alhaji Sama’ila maiguza. A ɓangaren Malamai kuma, akwai irinsu Malam Umar…
