13
Apr
"Aikin jin ƙai ko tallafa wa mabuƙata ba ruwansa da addini" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Sunan Hajiya Maryam Shehu Nabage da ake yi wa laƙabi da Uwar Marayu, ba ɓoyayye ba ne a cikin garin Jos da ma Jihar Filato bakiɗaya, saboda yadda ta yi fice wajen tallafa wa marayu, gajiyayyu, zawarawa da almajirai ƙarƙashin gidauniyarta ta Haske Support Foundation. Wakilin Manhaja Abba Abubakar Yakubu, ya ziyarci gidan ta dake Tudun Osi a unguwar Nasarawa Gwong, inda ya tarar da ita cikin tsakiyar aikin rabon kayan azumi da na ɗinkin sallah ga yara marayu. Ga yadda hirar su ta kasance:…
