09
Apr
Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Rundunar sojin Nijeriya, ƙarƙashin tawagar 'Operation Safe Haven', ta musanta zargin da ake yi ma ta na rura wutar rashin tsaro a jihar Filato. Rundunar ta kuma bayyana cewa, adadin sojoji uku da jami’i guda ’yan bindiga sun kashe su a tsakanin watan Janairun bana zuwa, wanda hakan bai tsayar aikin wanzar da zaman lafiya a yankunan har zuwa yau. Gamayyar ƙungiyoyin matasan Filato da suka haɗa da Afizere, Amo, Anaguta, Atten, Bache, Irigwe, Berom, Buji, Chokobo, Jere, Kurama, Lemoro, Tarya da kuma matasa da mata na ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar, sun…
