07
Apr
Daga CMG HAUSA Kwanan baya, kwamitin wasannin Olympic na ƙasa da ƙasa ya aike da wasiƙa zuwa babban rukunin rediyo da talabijin na ƙasar Sin wato CMG a takaice, inda ya nuna yabo da godiya ga nasarar da ya samu, wajen watsa shirye-shirye kai tsaye, yayin wasannin Olympics na lokacin hunturu da aka shirya a birnin Beijing, da kuma yadda yake yada wasannin Olympic na ƙasa da ƙasa yadda ya kamata. A matsayinsa na gidan rediyo da talabijin na ƙasa mai masaukin baki, kuma abokin haɗin kai na kwamitin wasannin Olympic na ƙasa da ƙasa, a aikin watsa shirye-shirye kai…
