Editor

9513 Posts
Buhari ne zai bayyana matsaya ta ƙarshe kan makomar Abba Kyari – Dingyaɗi

Buhari ne zai bayyana matsaya ta ƙarshe kan makomar Abba Kyari – Dingyaɗi

Daga SANI AHMAD GIWA Ministan Lamuran 'Yan Sandan Nijeriya, Muhammad Maigari Dingyaɗi ya ce sun kammala bincikensu kuma tuni sun miƙa shawarwari da suka bayar ga hukumomin da ya kamata. Ministan ya ce Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne zai yanke matsaya ta ƙarshe kan matakin da za a ɗauka a kan DCP Abba Kyari, da wata kotun ƙasar Amurka ta buƙaci a kamo mata shi, bisa tuhumarsa da alaƙa da Hushpuppi. A wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels, Dingyaɗi ya ce gwamnatin Nijeriya na buƙatar ganin an yi duk abin da ya kamata akan…
Read More
Ganduje ya ƙi amincewa da buƙatar shugaban KARATO na neman yin murabus

Ganduje ya ƙi amincewa da buƙatar shugaban KARATO na neman yin murabus

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Muƙaddashin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, ya ƙi karɓar takardar ajiye aiki da shugaban Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) Baffa Babba Ɗan-agundi ya miƙa a ranar Litinin don yin murabus. Bayanan da Blueprint Manhaja ta kalato sun nuna Ɗan-agundi ya miƙa takardar ajiye aiki ga muƙaddashin gwamna don ba shi damar ajiye aikinsa amma sai Gwamnan Jihar, Umar Ganduje wanda ya tafi hutu can Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya bada umarnin kada muƙaddashin nasa ya karɓi takardar. Sa'ilin da yake yi wa jaridar Solacebase ƙarin haske kan batun, Baffa Babba…
Read More
Al’ummar Musulmi a Xinjiang sun fara azumin watan Ramadan

Al’ummar Musulmi a Xinjiang sun fara azumin watan Ramadan

Daga CMG HAUSA Tun daga jiya Lahadi 3 ga watan nan, al’ummar musulmi a birnin Urumqi na jihar Xinjiang ta ƙasar Sin sun fara ibadar azumin watan Ramadan na bana. A cibiyar birnin Urumqi, akwai wani babban masallaci da ake kira White Mosque, mai tarihin kusan shekaru 100, inda musulmai su kan taru don yin salloli, da karatun Alƙur’ani mai tsarki, da gudanar da sauran wasu ibadu. A babbar kasuwar ƙasa da ƙasa mai suna Xinjiang International Grand Bazaar dake Urumqi, ana sayar da abubuwa masu sigar musamman ta wurin. A gaban shagunan sayar da kayan kade-kade, masu shagunan kan…
Read More
Iran: Amurka ba ta damu da ƙasashen Musulmi ba

Iran: Amurka ba ta damu da ƙasashen Musulmi ba

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi, ya ce ko kaɗan Amurka ba ta damu da halin da ƙasashen musulmi ke ciki ba, maimakon haka, burin ta shi ne cimma muradun ƙashin kai da tabbatar da danniya. Shugaba Raisi ya bayyana hakan ne, yayin zantawarsa ta wayar tarho da takwaransa na Iraƙi Barham Salih a jiya Lahadi. Ya ce ƙasarsa ta tallafawa Iraƙi, a fannin wanzar da hadin kan ƙasa, da samun ‘yancin kai, da tsaro, da tabbatar da gurbin ta a matakan ƙasa da ƙasa da na shiyya, kuma tsaron Iraƙi na da matuƙar tasiri ga tsaron shiyyar…
Read More
Waɗanne matakai ƙasar Sin ta ɗauka don tabbatar da tsaro a cikin gidanta?

Waɗanne matakai ƙasar Sin ta ɗauka don tabbatar da tsaro a cikin gidanta?

Daga CMG HAUSA Harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wani jirgin ƙasan fasinjoji a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, babban birnin Najeriya a kwanaki baya, ya girgiza al’ummar duniya sosai. Lamarin da ya fusata ‘yan ƙasar, inda wasu abokaina ke ta tattauna matakan da suka dace a dauka don daƙile ayyukan ‘yan fashi a Najeriya. A ganina, wataƙila za a iya duba wasu matakan da ƙasar Sin ta taba ɗauka don tabbatar da tsaro a cikin gidanta. Kamfanin ba da shawara na ƙasar Amurka Gallup ya gabatar da wani rahoto dangane da ayyukan shari’a na ƙasashe…
Read More
An yi jana’izar shugaban majalisar malamai na JIBWIS reshen Nasarawa

An yi jana’izar shugaban majalisar malamai na JIBWIS reshen Nasarawa

A yau Litinin aka yi jana'izar Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, HQ/Jos reshen jihar Nasarawa, Ustaz Surajo Alhaji Sabo Keffi tare da mutum biyun da Allah Ya karɓi rayuwarsu a wani hadarin mota da ya rutsa da su a jiya Lahadi, wato Asst National Org. Sectatry, Malam Adam Damaturu da kuma matar Al-Hafiz Idris Isa Nasarawa. An yi jana'izar ne a garin Fataskum, Jihar Yobe a ƙarƙarshin jagorancin Sheikh Sani Yahaya Jingir. Yayin sallar janazar Marigayan sun rasu ne a kan hanyarsu ta zuwa wajen Tafsirin Ramadan. Da fatan Allah ya sa Aljanna ta kasance makomarsu.
Read More
An sake ɗage shari’ar Kanu Nnamdi zuwa 10 ga Nuwamba

An sake ɗage shari’ar Kanu Nnamdi zuwa 10 ga Nuwamba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Kotun Tarayya a birnin Abuja ta ƙi amincewa da buqatar da lauyoyin Nnamdi Kanu suka gabatar na maida shi gidan gyara hali dake yankin Kuje a Abuja. An yi ta ce-ce-ku-ce dangane da makomar Kanu wanda aka daɗe ba a ji ɗuriyarsa ba tun bayan watan Yuli. Lauyoyin da ke kare Kanu, sun yi ta kira da a fito da shugaban ƙungiyar ta IPOB wanda hukumomi suka gaza gabatar da shi a gaban Mai Shari’a Binta Nyako a zama na ƙarshe da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli. Baya ga qin…
Read More
’Yan bindiga sanye da hijabi sun hallaka ɗan sanda a Katsina

’Yan bindiga sanye da hijabi sun hallaka ɗan sanda a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Da rana tsaka wasu mutane akan babur da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun kashe wani jami'in ɗan sanda a ƙauyen Biyu na Ƙaramar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina yayin da ɗan sandan da sauran abokan aikinsa ke gudanar da aikin su a wani shinge na binciken ababen hawa. Sun yi vadda kama a yayin da ɗaya daga cikin su na sanye da babbar riga ɗaya kuma ya saka hijabi. Isar su wurin ke da wuya suka buɗe wa jami'in ɗan sandan wuta suka kuma kashe shi nan take suka kuma gudu da bindigar…
Read More
Gidauniyar IDDEF ta yi taron yaye yaran da ta yi wa kaciya

Gidauniyar IDDEF ta yi taron yaye yaran da ta yi wa kaciya

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Gidauniyar tallafa wa Musulmi da mabuƙata ta duniya (IDDEF), ta yi wani taron yaye yaran da ta yi musu kaciya su kimanin 450 bayan sun warke daga kaciyar da aka yi musu. Taron wanda aka gudanar da shi a Ofishin Gidauniyar dake gidan Ladi Haladu a Kan titin Zaria a Kano ya samu halartar manyan mutane, cikin su har da Shugaban Gidauniyar na duniya Sheikh Muhammad Turan wanda ya zo daga ƙasar Turkiyya domin halartar taron. Tun da farko da ya ke Jawabi a wajen, babban mai kula da gudanarwar Gidauniyar a Nijeriya, Malam Askiya…
Read More
Yadda harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ya rikita Nijeriya

Yadda harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ya rikita Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIDA a Abuja A cikin 'yan kwanakin nan Jihar Kaduna na fuskantar matsanancin kai hare-hare daga 'yan fashin daji, inda suka addabi wasu yankunan jihar. 'Yan bindigar sun fito da sabon salon kai hare-hare a tashar jirgin sama da kuma hanyar titin jirgin ƙasa, kamar yadda 'yan bindigar suka kai wa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna cikin satin nan. Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane takwas, yayin da mutane 26 suka samu raunika, wasu kuma aka neme su sama ko ƙasa babu labari, a harin jirgin ƙasan mai ɗauke da fasinjoji kusan 1000 a daren…
Read More