Editor

9513 Posts
Shanghai: An yi wa sama da mutane miliyan 24 gwajin cutar COVID-19 a rana guda

Shanghai: An yi wa sama da mutane miliyan 24 gwajin cutar COVID-19 a rana guda

Daga CMG HAUSA A jiya Litinin, mahukuntan birnin Shanghai suka bayyana cewa, an kammala karɓar samfurin gwajin cutar COVID-19 daga al’ummar birnin su sama da miliyan 24, a wani mataki na daƙile bazuwar annobar, wadda ta sake ɓulla a sassan birnin. Wata sanarwa da aka fitar ta nuna cewa, an sanya birnin Shanghai cikin matakin kulle na wucin gadi, bayan da adadin masu harbuwa da cutar ta COVID-19 ya ƙaru matuƙa a ‘yan kwanakin baya bayan nan. Kaza lika, sanarwar ta ce a yanzu haka mahukuntan birnin na ci gaba da ayyukan gwaji, da killace masu ɗauke da cutar, tare…
Read More
Matsayar ƙasar Sin dangane da batun Ukraine, ta jaddada matsayinta na babbar ƙasar da ta san ya kamata

Matsayar ƙasar Sin dangane da batun Ukraine, ta jaddada matsayinta na babbar ƙasar da ta san ya kamata

Daga FA'IZA MUSTAPHA Ƙasar Sin ta sake jadadda matsayarta game da batun Ukraine da Rasha. Inda ta nanata cewa, bata neman cimma wani muradi na son kai a siyasar duniya dangane da batun, haka kuma, bata nuna halin ko in kula, bare kuma ta nemi kara rura wutar rikicin. Haƙiƙa, wannan ya sake fito da matsayin ƙasar Sin na babbar ƙasa da a kullum take kira da hawa teburin sulhu don tattaunawa da zummar samun maslaha, maimakon haddasa fito na fito. Ƙasar Sin ta bayyana haka ne ta bakin mamban majalisar gudanarwar ƙasar kuma ministan harkokin wajenta Wang Yi, yayin…
Read More
Za a kammala gadar da Sin ke ginawa a Habasha a farkon badi

Za a kammala gadar da Sin ke ginawa a Habasha a farkon badi

Daga CMG HAUSA Kamfanin gine-gine na CCCC (China Communications Construction Company) na ƙasar Sin, ya ce za a kammala ginin gadar kogin Abay ta Habasha, mai tsawon mita 380, zuwa rubu’in farko na shekarar 2023. Chen Li, manaja mai kula da aikin ginin gadar kogin Abay, ya ce ana sa ran za a kammala ginin wanda yanzu haka ya kai kaso 60, kafin rubu’in farko na baɗi. Kafar yada labarai ta ƙasar Habasha FBC, ta ruwaito Chen Li na cewa, gadar zata tanadi hanya mai fadi ga masu tafiyar kafa, baya ga ababen hawa. A nasa ɓangaren, Gebeyawe Belay, mataimakin…
Read More
Kotu ta yankewa Mubarak Bala zaman gidan yari na shekaru 24 saboda aikata laifin saɓo

Kotu ta yankewa Mubarak Bala zaman gidan yari na shekaru 24 saboda aikata laifin saɓo

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wata babbar kotu a Kano da ke arewacin Najeriya ta sake aike wa da Mubakar Bala zuwa gidan gyaran hali, saboda ci gaba da tsare rayuwarsa da kuma gazawar lauyoyinsa na gabatar wa kotun da cikakaken takardun da za su tabbatar mata cewar yana fama da rashin lafiya. An karanto wa Mubarak Bala caji 14 da ake tuhumarsa a kai na yin saɓo. Yayin zaman kotun, an karanto masa sakonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook, waɗanda ya yi kalaman batanci ga addinin Musulunci. Mubarak ya amsa dukkannin caji 14 da…
Read More
Jam’iyyar NNPP ta zaɓi sabbin shugabanninta na ƙasa

Jam’iyyar NNPP ta zaɓi sabbin shugabanninta na ƙasa

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Jerin sunayen waɗanda jam’iyyar NNPP ta zaɓa su 39 a matsayin shugabanninta a babban taronta na ƙasa da ya gudana ranar Laraba. 1- Farfesa Ahmed Rufa’i Alƙali (Gombe) – Shugaba 2-AVM John Chris Ifeimeji RTD (Anambra) – Mataimakin shugaba na kasa 3-Mr Dipo Olayoku (Ogun) – Babban Sakataren jam’iyyar 4-Sen Suleiman Hunkuyi (Kaduna) – Sakataren tsare-tsare 5-Dr Ahmed Ajuji (Adamawa) – Mataimakin babban Sakatare 6-Alhaji Sani malam (Bauchi) – Ma’aji 7-Prof. Ben Angwe (Benue) – Lauyan jam’iyyar 8-Chief Aneine clement (Rivers) Sakataren kudi 9-Maryam Yasin (Kwara) – Shugabar Mata 10-Muhammad Auwal (zamfara) – Shugaban Matasa…
Read More
Boko Haram sun kwantar da sojoji 11 a Kaduna

Boko Haram sun kwantar da sojoji 11 a Kaduna

Daga BASHIR ISAH Sahihan bayanan da suka riski Blueprint Manhaja a ranar Talata sun nuna mayaƙan Boko Haram sun kai mummunan hari Litinin da ta gabata a wani sansanin soja da ke yankin Polewire a Birnin Gwari, jihar Kaduna inda suka halaka sojoji 11 tare jikkata wasu 19. Haka nan, harin ya laƙume rayukan wasu 'yan bangan yankin su uku tare da raunata biyu daga cikinsu. Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, an shafe sama da sa'o'i uku ana ba-ta-kashi tsakanin 'yan bindigar da sojoji, inda a ƙarshe 'yan ta'addan suka ƙona motocin yaƙi guda uku mallakar sojojin Nijeriya. Bayanan…
Read More
Sharhin littafin ‘Duhun Damina’ na Maryamerh Abdul

Sharhin littafin ‘Duhun Damina’ na Maryamerh Abdul

Daga BAMAI ALHAJI DABUWA Sunan Marubuciya: Maryamerh AbdulShekarar Bugu: Babu.ISBN: 978-978-982-968-4.Mai Sharhi: Bamai Dabuwa.Lambar Waya: 07037852514. Gabatarwa/Abubuwan Burgewa:Littafin 'Duhun Damina' littafi ne da a ka yi amfani da wani irin salo mai kama da tafiyar kura. Shi ne littafin da ya kawo zunzurutun kuɗi sama da miliyan guda a ranar da a ka ƙaddamar da shi. Littafin ya taɓo wata matsala da kusan kowa ke tsoron taɓawa saboda gudun tambayar kai ta ya aka yi ka sani? Wasu kuma hankalinsu bai kai wajen ba, musamman iyaye, amma kuma rayuwar 'ya'yansu ce dumu-dumu a ciki. Littafi ne da kowanne uba/uwa ya…
Read More
Matan da ba su samu mijin aure ba (1)

Matan da ba su samu mijin aure ba (1)

Daga AISHA ASAS Daga lokacin da mace ta balaga, za ka ji ana mata addu’ar samun mijin aure. Yawaitar wannan furuci tsakanin dangi kan yi tasiri ga wasu yaran wajen tsaya wa da samarin da ke neman aurensu. A ganinsu ba abinda ya fi dace wa da su da ya wuce samun mijin aure. Ba wai na ce hakan laifi ba ne, sai dai a inda gizo ke saqa shine, lokacin da yarinyar ta kasa samun mijin aure. Matsin lambar da yarinya ke samu a lokacin da ta kawo ƙarfi daga baki da fuskokin mutane na ɗaya daga cikin dalilan…
Read More
Dubban likitoci ne suka garzaya Shanghai don taimaka wa birnin wajen yaƙi da COVID-19

Dubban likitoci ne suka garzaya Shanghai don taimaka wa birnin wajen yaƙi da COVID-19

Daga CMG HAUSA Rahotanni daga ƙasar Sin na cewa, kimanin likitoci 10,000 a duk faɗin ƙasar ne, suka garzaya zuwa Shanghai, cibiyar kasuwanci ta ƙasar, domin taimakawa cibiyar wajen daƙile yaɗuwar annobar COVID-19. Jiya Lahadi, dubun dubatan likitoci ne, suka isa birnin Shanghai mai yawan jama'a miliyan 25 ta cikin jiragen ƙasa masu saurin tafiya, wadanda suka taso daga yankunan Tianjin da Hubei da Shandong da Jiangxi. Hukumar lafiya ta birnin Shanghai ta bayyana cewa, tun da farko akwai tawagogin likitocin da suka fito daga lardunan Zhejiang da Jiangsu da Anhui da ke kusa, da suka riga suka isa birnin…
Read More
Sheikh Nuru Khalid zai soma limanci a wani sabon masallacin Abuja

Sheikh Nuru Khalid zai soma limanci a wani sabon masallacin Abuja

Daga BASHIR ISAH Fitaccen malamin nan na Abuja da ya rasa matsayinsa na limamin masallacin rukunin gidajen 'yan majalisar tarayya da ke Apo, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya ce an naɗa shi babban limamin sabon masallacin Juma'a da aka buɗe a bayan rukunin gidajen CBN da ke Abuja. Sheikh Khalid ya bayyana sabon naɗin nasa ne yayin zantawarsa da jaridar Vanguard ranar Litinin a Abuja, yana mai cewa Juma'a mai zuwa, 8 ga Afrilu zai soma jagorancin Sallar Juma'a a sabon Masallacin. Kwamitin Masallacin Apo ya tsige Sheikh Khalid daga limanci ne saboda huɗubar da ya yi a kan matsalar…
Read More