Editor

9513 Posts
Jami’an tsaro a Sudan na ci gaba da gwabzawa da ma su ƙyamar mulkin Soja

Jami’an tsaro a Sudan na ci gaba da gwabzawa da ma su ƙyamar mulkin Soja

Jami'an tsaro a Ƙasar Sudan sun ci gaba da fesawa ma su zanga-zanga don nuna kyamar mulkin Soja, hayaƙi mai sa ƙ kwana ɗaya bawallayan da jami'an tsaron suka kashe mutane 15. Ma su boren da yawa suka ja daga hanyoyi da ke arewacin birnin Khartoum, kwana ɗaya bayan kisan mutane da aka samu yayin boren nuna adawa da mulkin soja. Babban Janar Abdel Fattah al-Burhan da ke riqe da shugabancin ƙasar tun watan Aprilu 2019 da aka kifar da Gwamnatin shugaba Omar al-Bashir, ya tsare shugabannin fararen hula inda ya ayyana dokar ta-ɓaci ranar 25 ga watan Oktoba. Matakin…
Read More
Amurka za ta wanke waɗanda aka ɗaure kan kisan Malcolm X

Amurka za ta wanke waɗanda aka ɗaure kan kisan Malcolm X

Hukumomin Amurka na shirin wanke wasu mutane biyu da aka samu da laifin kashe fitaccen mai kare haƙƙin Bil Adama Malcolm X a shekarar 1965 saboda abinda suka kira kuskure wajen yi musu shari’a. Ana sa ran yau Babban lauyan Manhattan, Cyrus Vance ya jagoranci taron manema labarai inda zai sanar da wanke mutanen biyu Muhammad A. Aziz da Khalil Islam. An ɗaure Aziz mai shekaru 83 ɗaurin rai da rai a shekarar 1966, amma kuma sai aka sake shi a shekarar 1985, yayin da aka saki Islam a shekarar 1987, ya kuma rasu a shekarar 2009. Vance ya ce…
Read More
Dokar hana ganin Fursunoni na ci gaba da aiki a Togo

Dokar hana ganin Fursunoni na ci gaba da aiki a Togo

Hukumomi a Ƙasar Togo sun haramtawa dangi da ‘yan'uwan fursunoni da ke gidajen yari a faɗin ƙasar kai duk wata ziyara don saduwa da fursunoni da ke zaman kaso. Watanni 18 kenan da aka kafa wannan doka don a yaƙi cutar Korona daga kama shiga gidajen yari. Mutane da yawa daga cikin dangi da ‘yan'uwan fursunoni da ke gidan kaso sun koka matuqa saboda wannan mataki da ke hana su ganin mutanensu. Ministan Sharia na ƙasar Pius Agbetomey, tun a bara ya sanar da cewa an hana kai ziyara gidajen yari da ke faɗin ƙasar har sai illamasha’a saboda annobar…
Read More
Gobara ta ƙone shaguna 41 a Kasuwar Kurmi da ke Kano

Gobara ta ƙone shaguna 41 a Kasuwar Kurmi da ke Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da ƙonewar shaguna 41 a ɓangaren ƴan Littafi da ke ƙasuwar kurmi a ƙaramar hukumar birni ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, wanda shi ne Jami'in Hulɗa da Jama'a na hukumar ne ya tabbatar da gobarar a sanarwar da ya fitar ga manema labarai a yau Litinin. Abdullahi ya ce hukumar ta ƙarɓi rahoton gobarar ne ta wayar salula daga wani Malam Bala Nasidi da misalin ƙarfe 10:58 cewa akwai gobara a ƴan littattafai kasuwar. "Muna karɓar rahoton, bamu yi ƙasa a gwiwa ba mu ka garzaya wajen…
Read More
Amurka da Chana za su warware zaren gabar da ke tsakaninsu

Amurka da Chana za su warware zaren gabar da ke tsakaninsu

Shugaba Joe Biden, wanda ke zantawa da takwaransa Xi Jinping, ya ce akwai buqatar Amurka da Chana su gindaya wa kansu wasu ƙa’idoji don ganin cewa ƙasashen biyu sun kauce wa faɗawa mummunan rikici a tsakaninsu. Saɓanin da ƙasashen biyu suka jima suna fama da shi ya samo asali ne daga batun kasuwanci zuwa na kare haƙƙin bil adama. A jawabinsa lokacin wannan tattaunawar wadda aka yi ta hoton bidiyo, shugaba Biden ya shaida wa takwaransa Jinping cewa, bai kamata gasa da lasashen biyu ke yi ta rikiɗe zuwa gagarumin rikici ba. Biden ya ce, tabbas akwai ɗimibin batutuwan da…
Read More
Ɗan Marigayi Gaddafi, zai tsaya takarar shugabancin Libya

Ɗan Marigayi Gaddafi, zai tsaya takarar shugabancin Libya

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Ƙasar Libya ta sanya ranar 24 ga watan Disamba mai gabatowa domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa karo na farko tun bayan mummunar tashin-tashina da tawaye na shekara da shekaru da ya yi sanadiyyar tunɓuke shugaba Mamman Gaddafi daga ƙaragar mulki a shekarata 2011. Seif Al-Islam an yi masa gani na farko tun bayan garƙame shi a maɓuya da dakarun yaƙin neman ‘yanci suka yi a garin Zintana ranar 19 ga watan Nuwamba ta shekarar 2011, kamar yadda kafar watsa labarai ta ‘Ammar El-Darwish/AP’ ta ruwaito. Seif Al-Islam Gaddafi ya yi rajistar tsayawa takarar…
Read More
Za mu haɗa kai da kamfanoni don samar wa ’yan kasuwa gurbi a Kano, cewar Sabon Shugaban Ƙungiyar Masu Saida Waya

Za mu haɗa kai da kamfanoni don samar wa ’yan kasuwa gurbi a Kano, cewar Sabon Shugaban Ƙungiyar Masu Saida Waya

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Injiniya Abubakar Usman Ahmad, sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar masu sana'ar sayar da wayoyi a kasuwar titin Berut, ya bayyana cewa za su yi ƙoƙari wajen kawo sauye-sauye masu nagarta don bunƙasa ci gaban masu sana'ar sayar da wayoyi a kasuwar. Ya ce Allah ne ya ƙudurta shi zai samu nasara a zaɓen da aka yi, ba domin ya fi kowa ba, sai dai haka Allah ya so, don haka abokan kawo canji da suka yi takara tare su zo su ba shi haɗin kai da goyon baya, don haɗa hannu domin kawo ci gaba a…
Read More
WASIƘU: Kira ga gwamnati kan ƙalubalen tsaro a Nijeriya

WASIƘU: Kira ga gwamnati kan ƙalubalen tsaro a Nijeriya

*Zaɓen Anambara: Darasi ga Arewa*Matasa mu kama sana’a Nijeriya dai wata babbar ƙasa ce a yammacin Afrika, wacce Allah ya albarkace ta da tarin ni'imomi da albarkatu masu yawa. Kama daga yawan jama'a da suka haura miliyan 200, da kuma ma'adinan ƙarƙashin ƙasa, na ruwa da na kan tudu, wanda ba kowacce ƙasa ce Allah ya bai wa wannan arzikin ba. Sai dai kuma ƙalubale iri iri da suka haɗa da rashin shugabanci nagari, cin hanci da rashawa, ƙabilanci da ɓangaranci, da kuma uwa uba matsalar taɓarɓarewar tsaro. Sai dai duk da ƙoƙarin da masu riƙe da madafun iko, ƙwararru…
Read More
Sai nan da 2025 za a kuɓutar da ‘yan Nijeriya miliyan 25 daga ƙangin talauci – Osinbajo

Sai nan da 2025 za a kuɓutar da ‘yan Nijeriya miliyan 25 daga ƙangin talauci – Osinbajo

Daga Amina Yusuf Ali Mataimakin Shugaban ƙasar Nijeriya, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, Nijeriya ta gama tanadinta tun daga wannan shekarar ta 2021 domin tabbatar da cewa an kuɓutar da 'yan Nijeriya mutum miliyan 25 daga ƙangin talauci sannan kuma za a kange wasu miliyan goma daga afkawa ƙangin talaucin. Osinbajo wanda Sakataren Gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha ya wakilta ne ya bayyana hakan a taron tattalin arziki wanda NiDCOM ta shirya. Inda ya ƙara da cewa, tallalin arzikin Nijeriya ya ƙara bunƙasa a yanzu. Sannan kuma sanadiyyar sabbin abokan hulɗar da Nijeriya ta ƙara samu sakamakon annobar Covid19, za…
Read More