Editor

9513 Posts
Yadda taron ƙaddamar da littafin ‘Wazirin Ilorin’ ya gudana

Yadda taron ƙaddamar da littafin ‘Wazirin Ilorin’ ya gudana

Daga AISHA ASAS A ranar Lahadin da ta gabata 14 ga Nuwamba, 2021 ne aka ƙaddamar da littafin Wazirin Ilorin, Sanata Dr. Olusola Abubakar Saraki, wato mahaifi ga tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya, wanda ƙungiyar Manyan Marubuta Tarihi da Harsunan Afrika, ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar Farfesa Khalid Abdullahi Zariya, ta shirya wa kafafen yaɗa labarai a Agura Otel, don jin ta bakin mawallafin littafin. Taron ƙaddamar da littafin wanda aka rubuta akan rayuwa, gwagwarmaya da faɗi-tashin da Marigayi Sanata Dr. Olusola Abubakar Saraki (Wazirin Ilorin) ya yi a fannin siyasa da gina al'umma tare da sauran ɓangarori da marubucin ya…
Read More
Alamomin ciwon Basur

Alamomin ciwon Basur

Daga BILKISU YUSUF ALI Duk da basir ciwo ne da yake da alamomi da daman gaske amma akwai muhimmai da masana suka fi alaƙanta faruwarsu da ciwon basur. Mutane na ɗaukar alamomi barkatai komai suka ji su ce basir ne wanda hakan ba dai-dai ba ne. Manyan nau'ukan cutukan Basir guda biyu kowanne yana da irin nasa alamonin wato basur na ciki da basir mai zubar jini ko tsiro.Yana daga alamomin basir:-*Kumburin ciki*Cushewar ciki*Rashin narkewar abinci*Bushewar fata*Yawan zuwa banɗaki A wani lokacin kuma a ɗauki tsahon lokaci ba a shiga banɗaki ba kuma in an shiga a yi bayan gida…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Jirgin saman Nijeriya zai soma aiki a Afrilun 2022

Da ɗumi-ɗumi: Jirgin saman Nijeriya zai soma aiki a Afrilun 2022

Daga BASHIR ISAH Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Hadi Sirika, ya bayyana cewa ana sa ran jirgin saman Nigeria Air zai soma aiki ya zuwa Afrilun 2022. Sirika ya bayyana haka ne sa'ilin da yake zantawa da wakilan jaridu a Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zaratarwa a ranar Laraba. Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, shi ne wanda ya jagoranci taron na ranar Laraba. A cewar Sirika, zirga-zirgar jirgin a cikin ƙasa zai kasance ne a ƙarƙashin kulawar wani kamfani inda gwamnati ke da hannun jari na kashi 5% a ciki. Ya ci gaba da cewa, 'yan…
Read More
Dalilin da ya sa Sanata Hanga ya ce Buhari ya juya masa baya

Dalilin da ya sa Sanata Hanga ya ce Buhari ya juya masa baya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wani ƙusan ɗan siyasa a Jihar Kano, Sanata Rufa’i Sani Hanga, ya bayyana cewa ya kashe sama da Naira miliyan 100 daga aljihunsa wajen ganin Buhari ya zama shugaban ƙasa, amma sai aka wayi gari Buhari bai yi da shi. Da yake jawabi a Kano, Hanga ya ce da daman waɗanda suka dafa wa Buhari ya samu ɗarewa kujerar shugabancin ƙasa, duk an wata musu ƙasa a ido. Yana mai cewa, yanzu Buhari ya zaɓi wasu ne daban suke kewaye da shi waɗanda ba su bai wa yaƙin neman zaɓensa gudunmawa ba kuma ba 'yan…
Read More
Hukumar Abuja ta yi alƙawarin kaurara tallafinta ga tsofaffin sojojin Nijeriya

Hukumar Abuja ta yi alƙawarin kaurara tallafinta ga tsofaffin sojojin Nijeriya

Daga AISHA ASAS Hukumar Birnin Tarayya Abuja ta yi alƙawarin mara wa bikin Ranar Tunawa da Sojoji na 2022 baya don tabbatar da bikin ya cimma nasara. Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello ne ya yi wannan alƙawari a lokacin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar tsofoffin sojojin Nijeriya a ofishinsa, tare da bada tabbacin FCTA za ta kaurara gudunmawarta don inganta walwalar tsofoffin sojoji da matan sojojin da suka rasa rayukansu a matsayin nuna godiya ga sadaukarwar da dakarun suka yi wa ƙasa. Sanarwar da sakataren labarai na FCTA, Anthony Ogunleye ya sa wa hannu, ta nuna akwai kyakkyawar alaƙa…
Read More
Asalin ƙabilar Ibo a Nijeriya

Asalin ƙabilar Ibo a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamar sauran ƙabilun Nijeriya, tarihin al'umar Ibo shi ma yana tattare da bayanai da zato da fahimta da ra'ayoyi iri daban-daban, har ma da jayayya a tsakanin masana tarihi, musamman ma game da asalin inda al'ummar ta Ibo ta samo tushenta, inda masana tarihi da dama suke ikirari cewa, al'ummar ta Ibo ta samo asalinta ne daga Isra'ila, don haka tana da dangantaka da Yahudawa. Kuma daga can ne Ibon suka fito, har suka iso wajen da suka samu mazauni na dindindin a yankin kudu maso gabashin Nijeriya. Harshen Igbo wani vangare ne na dangin harsunan…
Read More
Numfashin mutum (3)

Numfashin mutum (3)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu, assalam aliakum. Barkan mu da wannan lokaci kuma barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka na Jikin ɗan Adam, wanda ya ke kawo mu ku bayanai game da jikin bil adama, domin ku fa’idantu, ku san yadda jikinku ya ke aiki. Har yanzu dai muna magana ne akan yadda ɗan Adam ke numfasawa, da kuma abubuwan da ke faruwa yayin wannan numfashi. Ɗan Adam na fara numfashi ne yayin da aka Haife shi, baya daina har sai kwanansa ya ƙare. Yayin da ɗan Adam ke cikin mahaifiyarsa, ba ya…
Read More
Mace mai sana’a ta fi daraja a idon mijinta – Balaraba Abdullah

Mace mai sana’a ta fi daraja a idon mijinta – Balaraba Abdullah

“Ya kamata 'yan siyasa su taimaka wa mata wajen cikar burinsu” Daga UMAR AƘILU MAJERI  Hajiya Balaraba Abdullahi shahararriyar 'yar kasuwa ce da ta yi shihura wajen taimakawa mata da ƙananan yara, ita ce mace ta farko a Jihar Jigawa da ta zaɓi ta yi kasuwanci bayan ta kammala karatun ta na zamani. Ba ta sha'awar aikin gwamnati, amma Hajiya Balaraba ta yi fice a fagen siyasa har ta tava riƙe muƙamin shugabar jam'iyya ta mata wato 'women leader' ta jam'iyyar SDP a nan Jihar Jigawa. Yanzu haka Hajiya Balaraba ta kafa gidauniya domin taimaka wa marayu da koya wa mata…
Read More
Cire tallafin mai: ‘Yan Nijeriya milyan 40 za su riƙa samun na-mota N5,000 duk wata a 2022 – Minista Zainab

Cire tallafin mai: ‘Yan Nijeriya milyan 40 za su riƙa samun na-mota N5,000 duk wata a 2022 – Minista Zainab

Daga BASHIR ISAH 'Yan Nijeriya kimanin su miliyan 40 ne za su riƙa samun N5,000 duk wata a matsayin kuɗin mota daga aljihun Gwamnatin Tarayya don rage raɗaɗin cire tallafin mai baki ɗaya ya zuwa baɗi idan Allah Ya kai mu. Gwamnati ta bayyana haka ne ta bakin Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, a wajen ƙaddamar da shirin Bankin Duniya na 'Nigeria Development Update' (NDU) a ranar Talata. Idan dai za a iya tunawa, a baya gwamnati ta bayyana cewa ya zuwa watan Yuli na 2022, za ta cire tallafin mai baki ɗaya. Gwamnatin ta ce adadin waɗanda…
Read More
Boko Haram sun saki sabon bidiyon wasu mutum 4 da ke hannunsu

Boko Haram sun saki sabon bidiyon wasu mutum 4 da ke hannunsu

Daga WAKILINMU Mayaƙan Boko Haram sun saki wani bidiyo mai ɗauke da wasu mutum huɗu da suka kama daga sassan yankin Arewa-maso-gabas a Nijeriya. Waɗanda aka gani a cikin bidiyon mai tsayin minti 1 da sakan 40 sun haɗa da Imranu Mohammed Askira, mai gonar kaji, da wani ma'aikaci mai aiki tare da NDA waɗanda aka kama su tsakanin Buratai da Buni Yadi a ranar 21/11/2021. Sai kuma Zakariya Ajikime ma'aikacin UNICEF, wanda ya faɗa a hannun Boko Haram tsakanin Sabon gari da Wajoroko a ranar 3/10/2021. Shi kuwa Mohammed Askira ma'aikacin Bankin Premier Commercial a Maiduguri, ya faɗa a…
Read More