Alamomin ciwon Basur

Daga BILKISU YUSUF ALI

Duk da basir ciwo ne da yake da alamomi da daman gaske amma akwai muhimmai da masana suka fi alaƙanta faruwarsu da ciwon basur.

Mutane na ɗaukar alamomi barkatai komai suka ji su ce basir ne wanda hakan ba dai-dai ba ne. Manyan nau’ukan cutukan Basir guda biyu kowanne yana da irin nasa alamonin wato basur na ciki da basir mai zubar jini ko tsiro.Yana daga alamomin basir:-
*Kumburin ciki
*Cushewar ciki
*Rashin narkewar abinci
*Bushewar fata
*Yawan zuwa banɗaki

A wani lokacin kuma a ɗauki tsahon lokaci ba a shiga banɗaki ba kuma in an shiga a yi bayan gida mai tauri.

Wani lokacin mutum kan yi bayan gida irin na dabbobi kamar duwatsu.

*Yana sa rama sosai
*Ciwon dubura
*Fitar baya

Basir kan haddasa ɗaukewar sha’awa ko ya hana sha’awar daga mace har namiji.

Basir kan sa mace ta bushe ya ɗauke mata ni’ima in an kusanceta sai dai ta ji zafi.

Yana haddasa rashin ƙarfin ɗa namiji sosai har in ya ta’azzara ya kai ga ma gabansa ya mutu.

Zubar jini bayan an gama bayan gida, wani lokacin kuma kawai sai jinin yake zuba ko ya ke naso a duburar.

Yana sa ƙaiƙayin dubura sau tari har takan tsage kamar an yanka da reza a wasu lokutan har da ƙuraje.

Basur kan sa ciwon kwakwalwa in ya yi ƙarfi za a ga kamar mutum na hauka.

Yana sa zafin ciki kamar me ciwon olsa.

Alamomin Basir yana da yawan gaske wanda ba a gane shi ko a sha magani sai an tuntuɓi masana don sau tari akan alaƙanta kowanne ciwo da basir don haka sai a je a yi maganin da bai dace da ciwo ba.

A mako na gaba za mu kawo hanyoyi da maganin da ya dace mai cutar basur ya sha in sha Allah.

Ga mai tambaya ko ƙarin bayani yana iya tuntuɓar wannan layin amma tes kawai ko ta WhatsApp 08039475191 ko a shafina na facebook Bilkisu Yusuf Ali

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *