26
Nov
Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai majalisar dattawan Nijeriya tana gab da tabbatar da ƙudirin samar da hukumar da za ta dinga tafiyarwa da kuma kula da hada-hadar gidaje da filaye. A ƙoƙarinta na ceto dubban 'yan Nijeriya da suke faɗawa komar mazambata a koyaushe. An shigar da wannan ƙuduri ne domin kawo saiti a harkar hada-hadar gidaje da filayen wacce sam ba saiti a cikinta. Wacce hakan ya sa wasu ɓata-garin ke amfani da damar don turmusa hancin wasu 'yan Nijeriya. Shi dai wannan ƙuduri wanda Sanata Aliyu Wamakko (APC, Sokoto) ya ɗauki nauyi a yanzu haka…
