Editor

9513 Posts
HOTUNA: An yi jana’izar Janar Dzarma da wasu dakaru 7

HOTUNA: An yi jana’izar Janar Dzarma da wasu dakaru 7

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa sadaukarwar da dakarun suka nuna a halin rayuwarsu. Yayin da Gwamnan Adamawa, Umaru Ahmadu Fintiri ya sanya wa wata hanya a Yola sunan Marigayi Zurkushu don ci gaba da raya sunan. Sanarwar da Daraktan sashen hulɗa da jama'a na sojojin Nijeriya, Brigadier General Onyema Nwachukwu ya fitar, ta nuna Buhari ya halarci jana'izar da aka gudanar a Yola a Juma'ar da ta gabata a bisa wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha. Kazalika, sanarwar ta nuna Gwamna Fintiri ya bai wa iyalan Marigayi Brig Gen Dzarma Zurkushu tallafin kuɗi Naira miliyan 10, da kuma…
Read More
Yadda nacina ya kai ni ga nasara a gasar Hikayata, inji Zulaihat Alhassan

Yadda nacina ya kai ni ga nasara a gasar Hikayata, inji Zulaihat Alhassan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zulaihat Alhassan ita ce wadda ta zo ta uku a gasar Hikayata ta BBC Hausa ta shekarar 2021, wadda aka yi bikin karrama gwarazan jiya a Abuja, babban birnin tarayya. Zulaihat ta kasance ta uku ne da labarin ta mai suna 'Ramat' wanda babban jigon sa yake ishara da gaskiya da riƙon amana, sai kuma ƙaramin jigon sa da ke bayar da labari akan fyaɗe. Gwarzuwar ta uku ta kuma samu kyautar dala 500 tare da kambun karramawa. Zulaihat Alhassan haifaffiyar garin Kaduna a yankin Maƙera da ke Kakuri cikin ƙaramar hukumar Kaduna ta…
Read More
Gwamna Badaru zai samar wa gwarazan ‘Hikayata’ aiki

Gwamna Badaru zai samar wa gwarazan ‘Hikayata’ aiki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya ce zai samar wa gwarazan gasar Hikiyata ta BBC Hausa aikin yi da zarar sun kammala karatun su. Gwamna Badaru ya faɗi hakan ne a wajen taron karrama waɗanda suka lashe gasar ta bana, wanda ya gudana a ɗakin taro na Ladi Kwali da ke Sheraton Otel a Abuja. Badaru ya bayyana cewa yana da alfarma a wajen gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai, don haka zai roƙe shi da ya ɗauki Aisha Musa Dalil da ta zo ta ɗaya a gasar da kuma Zulaihat Alhassan, wadda…
Read More
Saraki ya halarci ɗaurin suren ɗiyar Sheikh Bala Lau

Saraki ya halarci ɗaurin suren ɗiyar Sheikh Bala Lau

Daga NASIRU S. GWANGWAZO A yau Juma'a ne tsohon Shugaban majalisar dattawan Nijeriya kuma tsohon gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya halarci ɗaurin auren diyar shugaban kungiyar Izala ta Nijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau. Auren wanda aka ɗaura a babban masallacin Juma'a na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi dake unguwar Malali a Jihar Kaduna ya samu halartar manyan mutane da malamai daga sassan Nijeriya. Wazirin na Ilorin ya shaidi auren wanda aka kulla tsakanin amarya Rufaida Bala Lau da angonta Tijjani Abdullahi Gabba. A wani saƙon taya murna da ya ɗora a shafinsa na Facebook, Dakta Saraki ya yi…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Aisha Musa Dalil ta zama gwarzuwar gasar ‘Hikayata’

Da ɗumi-ɗumi: Aisha Musa Dalil ta zama gwarzuwar gasar ‘Hikayata’

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Aisha Musa Dalil, ita ce ta zo ta farko a gasar Hikayata ta BBC Hausa ta shekarar 2021, haifaffiyar Jihar Kaduna, wanda ta yi karatun firamare da sakandare duk a jihar Kaduna, sannan yanzu haka tana karatu a Jami'ar Umaru Musa YarAdua da ke Katsina, inda take karantar harsunan Ingilishi da Faransanci a fannin kimiyyar harshe. Aisha Musa Dalil ta shiga gasar Hikayata ta BBC Hausa da labarinta mai taken 'Haƙƙina', wanda jigonsa ya karkata kacokan akan fyaɗe kamar yadda ta bayyana a tattaunawar da ta yi da jaridar Manhaja kafin bayar da kyaututtuka,…
Read More
Sabon harin Filato ya laƙume rayuka 10 da gidaje 30

Sabon harin Filato ya laƙume rayuka 10 da gidaje 30

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga yankin ƙaramar hukumar Bassa a jihar Filato, sun nuna cewa aƙalla mutane 10 sun mutu sannan an ƙona gidaje sama 30 sakamakon wani sabon hari da aka kai da sanyin safiyar Juma'a a ƙauyen Te’egbe da ke yankin. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Ubah Ogaba, ya tabbatar da aukuwar harin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, inda ya ce wasu da ba a kai ga sanin ko su wane ne ba sun kai hari a ƙauyen Te’egbe da ke yankin ƙaramar hukumar Bassa a jihar. Ya ce mutum 10 sun…
Read More
‘Yan sandan Zamfara sun kama wata mata bisa zargin ba wa ‘yan bindiga harsashi

‘Yan sandan Zamfara sun kama wata mata bisa zargin ba wa ‘yan bindiga harsashi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sashen Tactical Operatives tare da haɗin gwiwar FIB/STS ƙarƙashin jagorancin DSP Hussaini Gimba, sun kama wata mata mai suna Fatima Lawali ‘yar shekara 30 da ta amsa laifin yin safarar harsasai ga ‘yan bindiga a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba N. Elkana ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Juma’a. A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne a unguwar Gada Biyu da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bunguɗu a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Ya ce, “A ranar 25 ga Oktoba,…
Read More
Tsadar abinci: Gwamnatin Nijar za ta fara sayar wa da talakawa kayan abinci da kanta

Tsadar abinci: Gwamnatin Nijar za ta fara sayar wa da talakawa kayan abinci da kanta

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da 'yan ƙasar Nijeriya suke kokawa da matsananciyar tsadar abinci wanda ya jefa su a ƙangin rayuwa, ita kuma ƙasar Nijar ta karɓe ragamar sayar da abinci daga hannun magadan gari domin fara sayar da shi a farashi mai rahusa ga talakawan ƙasar, wadanda ke shan wahala wajen samun wadataccen abincin. Tuni wannan matakin ya haddasa cece-kuce a faɗin ƙasar, inda wasu ke lale marhabin da tsarin, wasu kuma suke adawa. Gwamnatin Nijar ta karɓe ragamar sayar da abinci daga hannun magadan gari domin fara sayar da shi a farashi mai rahusa ga talakawan…
Read More
Takun saƙa tsakanin kwamitin maƙabarta da ‘yan kasuwar Kwanar tifa a jihar Kano

Takun saƙa tsakanin kwamitin maƙabarta da ‘yan kasuwar Kwanar tifa a jihar Kano

Daga MUKHTAR YAKUBU A yanzu haka dai wata Sabuwar rigima ta ɓullo a tsakanin 'yan kwamitin Maƙabartar Tudun Murtala dake jihar Kano da kuma masu gudanar da harkokin kasuwancinsu a jikin maƙabartar. Wannan rigima kuwa ta samo asali ne a satin da ya gabata inda gobara ta tashi a cikin maƙabartar da tsakiyar rana wadda kuma har zuwa wannan lokacin ba a samu musabbabin tashinta ba. Sai dai wasu na ɗora alhakin tashin nata a kan masu gudanar da kasuwancin su a wajen. Hakan ya sa Kwamitin Unguwar Tudun Murtala suka buƙaci masu gudanar da kasuwanci a jikin maƙabartar da…
Read More