Editor

9513 Posts
Yadda wasu likitoci suka sa wa mutum ƙodar alade

Yadda wasu likitoci suka sa wa mutum ƙodar alade

A karon farko wani ƙwararre a fannin tiyata a Amurka mai suna, Dakta Robert Montgomery ya ce, sun samu nasarar dasa wa wani mutum ƙodar alade, inda suke fatan hakan zai taimaka wajen kawo karshen ƙarancin taimakon ƙoda da ake samu a wannan lokaci. Ƙwaƙwalwar mutumin da aka sanya wa kodar tuni ta daina aiki, inda yake ci gaba da rayuwa da taimakon na’ura, lamarin da ya sa mutum ne da ƙwaƙwalwarsa ta daina aiki, lamarin da ya sa aka cire tsammani da shi. Ita dai ƙodar da aka yi amfani da ita, ta wani alade ne da aka jirkita…
Read More
Ba za mu yarda da ƙarin farashin man fetur ba – Ƙungiyar Ƙwadago

Ba za mu yarda da ƙarin farashin man fetur ba – Ƙungiyar Ƙwadago

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa, NLC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi watsi da shirin qara farashin man fetur a Nijeriya. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Ayuba Wabba ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata.  A cewar sa, Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPC,  Mele Kyari, ya sanar da cewa farashin man fetur zai iya yin tashin gwauron zabi har Naira 340 daga watan Fabrairun 2022. Amma da ya ke mayar da martani…
Read More
Kannywood: Mafari da makoma

Kannywood: Mafari da makoma

Daga AL'MUSTAPHA ADAM MUHAMMAD Wasan kwaikwayo wani al’amari ne mai daɗɗaɗen tarihi a rayuwar ɗan Adam. Ya samo asali ne shekaru aru-aru da suka wuce a daulolin Girkawa da Rumawa tun ɗaruruwan shekarun da suka shuɗe. Tun a wancan lakacin akan yi amfani da wasan kwaikwayo ne don nishaɗantarwa da zaburar da rundunonin sojojinsu da suka yi nasara a yaƙe-yaƙen su a wancan zamani. Haka zalika akan yi wasannin kwaikwayo don faranta wa masu mulki rai su samu cikakken muwalati da nishaɗi. A irin waɗannan lokuta ne makaɗa, masu iya bada hikayoyi, maraya da mutanen fadla masu barkwanci kan sheƙe…
Read More
Zamfara: An kulle gidan mai da na burodi bisa Zargin alaƙa da ‘yan bindiga

Zamfara: An kulle gidan mai da na burodi bisa Zargin alaƙa da ‘yan bindiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwamitin bibiya na Jihar Zamfara ya bi bi umarnin Gwamna Bello Matawalle kan matsalar rashin tsaro, ya bada umarnin rufe gidan mai da gidan burodi a ƙananan hukumomin Gusau da Tsafe a jihar. Shugaban kwamitin, Abubakar Dauran ne ya bayar da wannan umarni jim kaɗan bayan jami’an tsaro sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da bayar da burodi da fetur ga ‘yan bindiga. Dauran, kuma mai bai wa Matawalle shawara kan harkokin tsaro, ya ce za a rufe gidan man da ke garin Tsafe a ƙaramar hukumar Tsafe, bisa zargin sayar da…
Read More
Buhari ya cancanci yabo bisa magance rikicin manoma da makiyaya – Garba Shehu

Buhari ya cancanci yabo bisa magance rikicin manoma da makiyaya – Garba Shehu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Muhammad Buhari kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa, shugaban ya cancanci yabo bisa ƙoƙarin da ya yi na magance rikicin manoma da makiyaya a ƙasar nan. Shehu ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a a lokacin da yake gabatar da wata takarda mai taken ‘Labaran ƙarya: ƙalubalen sarrafa bayanai’ a wajen bikin cika shekara 10 da kafa Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), da ke jihar Katsina. Ya ƙara da cewa, “tabbas gwamnatin Buhari ce kawai gwamnatin Nijeriya da ta samar da hanyar da za ta…
Read More
‘Yar Jamhuriyar Nijar ta farko da ta yi nasara a gasar Hikayata

‘Yar Jamhuriyar Nijar ta farko da ta yi nasara a gasar Hikayata

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An haifi Nana Aicha Hamissou Abdoulaye a ranar 27 ga watan Yuli, 1994 a unguwar Sabon Gari da ke garin Maraɗi. Ta fara karatun boko a shekarar 2000, ta yi digirinta na farko a fannin muhalli. Yanzu haka kuma tana cigaba da karatun digiri na biyu a fannin rabe-raben rayuwa da Muhalli a jami'ar Abubakar Ibrahim da ke Maraɗi a Ƙasar Nijar. Nana Aicha Hamissou Abdoulaue ta samu ilimin addini mai zurfi, inda ta sauke Alƙur'ani Maigirma a watan Disamba, 2013. Mahaifin Nana Aicha ta rasa mahaifinta a shekarun da suka gabata, inda yanzu…
Read More
Za mu dakatar da rufe layukan sadarwa Talata mai zuwa – Matawalle

Za mu dakatar da rufe layukan sadarwa Talata mai zuwa – Matawalle

Daga Sanusi Muhammad, Gusau Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya yi alƙawarin buɗe hanyoyin sadarwa a sauran ƙananan hukumomi 13 na jihar a ranar Talata mai zuwa. Matawalle ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin jam’iyyar APC na jihar a ranar Asabar. A cewarsa, rahotannin da gwamnatin sa ta samu sun nuna cewa an rage matsalar rashin tsaro zuwa mafi ƙaranci. "Mun samu rahoton leƙen asiri cewa an kawar da barazanar 'yan bindiga fiye da kimai don haka za mu sake buɗe hanyoyin sadarwa tsakanin Litinin ko Talata", inji Matawalle. Ya kuma yi kira…
Read More
Ƙarin kuɗin mai: Cikin ’yan Nijeriya ya ɗuri ruwa

Ƙarin kuɗin mai: Cikin ’yan Nijeriya ya ɗuri ruwa

*Fetur na iya tashi zuwa Naira 340 lita guda – Shugaban NNPC*Za mu ba da tallafin sufurin Naira 5,000 duk wata, inji gwamnati*Babu tanadi a kasafin 2022 – Majalisar Dattawa*Matakin zai haifar da cin hanci da rashawa – Masu ruwa da tsaki*Yadda NNPC ke kashe Naira tiriliyan 1.8 akan tallafi duk shekara Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Cikin mafi yawan ’yan Nijeriya ya ɗuri ruwa kan makomarsu muddin cire tallafin man fetur bakiɗaya ya kankama nan da watanni. Tun bayan samun sanarwar daga Gwamnatin Tarayya da ke tabbatar da cewa, a watannin farko na shekarar 2022 za a cire…
Read More
Yadda tsadar rayuwa ke janyo lalacewar tarbiyya

Yadda tsadar rayuwa ke janyo lalacewar tarbiyya

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Da fatan mun same ku lafiya, a wannan mako. Yau za mu yi magana a kan tsadar rayuwa da muke fuskanta ta ko'ina. Ita ma ta ba da gudunmowar taɓarɓarewar tarbiyya. Saboda sai da akwai arziki kowa ke iya rayuwa cikin farin ciki. Yanzu abin da za a ci ma nema yake ya gagari mutane. Talaka na ganin rayuwa! Kana so ka yi abu ba dama, saboda rashin kuɗi. Kafin goma ta shigo maka hannu, wallahi Naira ɗari ta fita daga hannun ka. Ba a ma ta sauran abubuwa kowa ta abin da zai ci yake…
Read More
Yadda al’adar gaisuwa ke ƙarfafa zumunci

Yadda al’adar gaisuwa ke ƙarfafa zumunci

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Gaisuwa, musabaha ko kuma sallama wata halayyar ɗan Adam ce wadda ya kan yi ta hanyar yin amfani da wasu kalmomi ko wata inkiya, da sauti ko da gaɓar jiki, da nufin marabtar baƙo ko sada zumunci da girmamawa. Akwai yanayin gaisuwa iri-iri da ƙabilu ko addinai, da zamantakewa kan sa su rungumi wata halayya ta gaisuwa da nufin mutunta juna. A wajen wasu al'ummar akan bambanta irin gaisuwar da ake yi wa babban mutum, basarake, ko talaka. Mace ko namiji, yaro ko babba. Wasu na gaisuwa ne a tsaye, tare da haɗa kafaɗar hagu da…
Read More