Editor

9513 Posts
Ku amsa waɗannan tambayoyi kafin ku yanke hukuncin rabuwa

Ku amsa waɗannan tambayoyi kafin ku yanke hukuncin rabuwa

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da haɗuwa a wannan makon! Sannunku da jimirin karatun jaridar Manhaja! A wannan makon za mu yi magana a kan yadda wasu lokuta a rayuwar aure da zaman yake yin zafi ya ƙi daɗi. Har ma su yanke shawarar su rabu da juna. Ko ɗaya ya dinga riyawa a zuciyarsa ba mafita illa ya rabu da ita ko ita ta dinga tunanin idan ba ta rabu da shi ba ba ta da sauran wani 'yanci. Eh haka ne, akwai wasu lokuta na rayuwar aure da suke zuwa ku ji sam ba kwa jin daɗin zaman.…
Read More
‘Yan sanda sun bindige gawurtaccen ɗan bindiga, Yellow Magaji a otel

‘Yan sanda sun bindige gawurtaccen ɗan bindiga, Yellow Magaji a otel

Daga BASHIR ISAH Bayanan 'yan sandan jihar Kaduna sun nuna 'yan sandan jihar sun samu nasarar sheƙe gawurtaccen ɗan bindigar nan Yellow Magaji da ya addabi babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya faɗa a ranar Asabar cewa, an kashe Yellow Magaji ne a ranar 24 ga Nuwamban 2021. A cewarsa, sakamakon bayanan sirri da suka samu ne ya sanya 'yan sandan Kaduna tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro na musamman na tarayya bisa unarnin Kwamishinan 'Yan sanda CP Mudassiru Abdullahi suka yi dirar mikiya a masaukin baƙi…
Read More
An rutsa mahara a cikin kurkukun Jos

An rutsa mahara a cikin kurkukun Jos

Daga BASHIR ISAH A yammacin jiya Lahadi 'yan bindiga suka kai hari gidan yarin garin Jos a Jihar Filato inda aka ce 'yan bindigar sun maƙale a cikin gidan yarin sun rasa mafita sakamakon ƙawanyar da jami'an tsaro suka yi musu. Mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yari na ƙasa, CC Francis Enobore, shi ne ya bayyana haka a Abuja ran Lahadi da daddare. Sanarwar da ta fito ta hannunsa ta ce, "Gungun 'yan bindiga sun kai wa gidan gyaran hali na Jos, jihar Filato hari ɗauke da muggan makamai. "An ce maharan sun dira gidan yarin ne…
Read More
Rasuwar Sani Buhari Daura babban rashi ne ga Nijeriya – Shugaba Buhari

Rasuwar Sani Buhari Daura babban rashi ne ga Nijeriya – Shugaba Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwar nan mazaunin Kano, Alhaji Sani Buhari Daura, a matsayin babban rashi ba ga jihar Katsina da Kano kaɗai ba, amma ga ƙasa bakiɗaya musamman ma idan aka yi la'akari da irin tasirin da yake da shi ga tattalin arzikin ƙasa. Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu a ranar Lahadi. Yana mai bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin daɗaɗɗun jiga-jigan 'yan kasuwa a Nijeriya waɗanda suka bada gudunmawarsu gaya wajen cigaban tattalin arzikim…
Read More
Matasa ya kamata su jagoranci Nijeriya kasancewarsu ƙashin bayan al’umma – Abba Sa’ad

Matasa ya kamata su jagoranci Nijeriya kasancewarsu ƙashin bayan al’umma – Abba Sa’ad

Daga ABUBAKAR M. TAHIR a Haɗeja Haƙiƙa ya zama wajibi mutane su dawo hayyacinsu su gwada bai wa matasa ƙuri'un su, domin samar da ci gaba ga al'umma. Abba Bin Sa'ad Haɗeja shi ne ya yi wannan kira a lolacin da yake tattaunawa da wakilin Manhaja a Haɗeja, inda ya bayyana cewa ya kamata matasa su zama jagororin ƙasar nan domin samun ci gaba mai ma'ana. "Musamman idan ka duba halin ƙunci da ake ciki a wannan ƙasa, ga kuma halin rashin tsaro wanda duk wani ɗan Nijeriya babba da yaro ya san da wannan matsala. Kamata a ce matasa…
Read More
Kare ya zama babban attajiri a Ƙasar Jamus

Kare ya zama babban attajiri a Ƙasar Jamus

Wani kare a ƙasar Jamus mai suna Gunther VI ya zama babban attajiri bayan an damƙa ma sa gadonsa na biliyoyin Daloli. An yi kiyasin cewa, karen ya zama mamallakin Dala miliyan 500, kimanin Naira biliyan 205,420,000,000 kenan, kuma yana rayuwa a wani katafaren gida, kamar yadda rahoto ya tabbatar. Gunther VI na ɗaya daga cikin zuri'ar Gunther III wanda ya taki sa'a ya gaji ɗumbin arziki daga uban gidansa, Karlotta Liebenstein, wanda ya mutu a 1992. Kakan kare Gunther VI ya gaji dukiyar ne shekaru 30 da suka gabata bayan ya cika burin uban gidan nasa, kamar yadda Business…
Read More
Yadda kwalliya ta biya kuɗin sabulu a shirin bunƙasa noma a Kano

Yadda kwalliya ta biya kuɗin sabulu a shirin bunƙasa noma a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwalliya ta biya kuɗin sabulu a katafaren shirin nan na bunƙasa noma da kiwo na Jihar Kano, wanda aka yi wa laƙabi da KSDP, wanda shiri ne da yake samun tallafi daga Bankin Addinin Musulunci dake Ƙasar Saudi Arabiya. Shirin na samar da hanyoyin da za a bunƙasa yawan abincin da ake nomawa a Jihar Kano ƙarƙashin ƙungiyar Sasakawa. A wannan mako ne ƙungiyar ta gayyaci ‘yan jaridu domin nuna musu irin ayyukan da suka yi a wannan shekara da muke bankwana da ita. Da fari an bai wa ƙungiyar ta Sasakawa damar koyar…
Read More
Sani Buhari Daura ya kwanta dama

Sani Buhari Daura ya kwanta dama

Daga WAKILINMU Allah Ya yi wa hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Sani Buhari Daura (Walin Daura) rasuwa. Ɗan marigayin Abdulrasheed Daura ne ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa ga jaridar Daily Nigerian, yana mai cewa marigayin ya rasu ne da safiyar Lahadi a can ƙasar Dubai. A halin rayuwarsa, Marigayi Daura shi ne shugaban kamfanoni da dama da ya kafa, da suka haɗa da kamfanin Bayajidda Nigerian Limited da Standard Construction Limited da Buhari Properties and Development Company da kuma kamfanin nan na Katsina Oil Mill. Kamfaninsa na Standard Construction Limited shi ne ya gina fitaccen ginin nan da ake kira…
Read More
Farfesa Khalid ya ja kunnen malamai a Kebbi

Farfesa Khalid ya ja kunnen malamai a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Shugaban hukumar ilmin bai ɗaya ta jihar Kebbi (SUPEB), Farfesa Suleman Khalid ya ja kunnen ma'aikata musamman malamai kan tsare aiki. Ya yi wannan bayani ne jiya Alhamis da ya ke zantawa da wakilinmu a garin Augie a cikin wani rangadi da ya ke na ganewa idonsa yadda aikin koyarwa a makarantun firamare ke tafiya a faɗin jihar. Farfesa Suleman Khalid ya ce ya ziyarci yankunan Yola da Gobirawa, inda ya tabbatar wa malamai da cewa gwamnatin jihar Kebbi tana nan tana tsare-tsaren tabbatar da bai wa kowane malami haƙƙinsa, saboda haka ya kamata kowa…
Read More
Ya sayar da ɗansa, ya yi wa mahaifiyar ɗan ƙaryar ya mutu

Ya sayar da ɗansa, ya yi wa mahaifiyar ɗan ƙaryar ya mutu

Rundunar ’yan sanda a jihar Abia, ta kama wani ɗan shekara 40, Appolos Ndubuisi, bisa zargin sayar da ɗansa na miji kan kuɗi naira 350,000, bayan ya yaudari mahaifiyarsa da cewar ya mutu a lokacin haihuwa. An tattaro cewa, Ndubuisi ya haɗa kai da wata Rose Godwin Chinweikpe, wacce ke da wajen karɓar haihuwa a garin Owoahia-Afor da ke yankin Obingwa, wajen sayar da jinjirin. Rahotanni sun ce, matar Ndubuisi, Deborah Onukaogu ce ta haifi jinjirin wanda ya kasance bakwaini. Da ta ke jawabi ga manema labarai a Umuahia, kwamishinar ’yan sandan jihar Abia, Janet Agbede, ta ce, Omukaogu ta…
Read More