Editor

9513 Posts
Asalin Fulani da shigarsu Ƙasar Hausa

Asalin Fulani da shigarsu Ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ci gaba da kawo muku tarihin manyan qabilun Nijeriya, yau ma Jaridar Manhaja za ta yi duba kan ƙabilar Fulani, wadda ɗaya ce daga cikin manyan ƙabilu mafi yawan jama'a a Nijeriya. Tushen Fulani:Fulani dai ƙabila ce da tarihi ke turke asalinta tun ƙarni na 15 daga wasu manyan ’yankuna biyu da ke ƙasashen Senegal da kuma Guinea Conakry, wato Futa Toro da kuma Futa Jalloh. Daga nan ne suka ci gaba da bazuwa cikin ƙasashen duniya musamman yammaci da kuma tsakiyar nahiyar Afirka domin nema wa dabbobinsu abinci da kuma ingantacciyar rayuwa. Ko da…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Sojoji sun daƙile yinƙurin hare-haren ISWAP

Da ɗumi-ɗumi: Sojoji sun daƙile yinƙurin hare-haren ISWAP

Sojojin Nijeriya na ƙasa da sama sun yi nasarar daƙile yinƙurin kai harin mayaƙan ISWAP da suka mamaye yankin Buni Yadi a jihar Yobe Duk da nasarar da sojojin suka samu a kan mayaƙan na ISWAP, tun farko sai da mayaƙan suka banka wa wani ofishin 'yan sanda wuta kafin daga bisani sojoji suka katse musu hanzari. Bayanan sojojin sun nuna mayaƙan sun tsere don neman mafaka sakamakon luguden wutar da suka sha a wajen sojojon. An ce an ga jiragen yaƙin sojojin sama ƙirar Super Tucano na shawagi a yankin tabkin Chadi tare da yin luguden wuta a kan…
Read More
WASIƘU: Illar cusa ƙiyayya a tsakanin jama’a (1)

WASIƘU: Illar cusa ƙiyayya a tsakanin jama’a (1)

*Cire Nijeriya daga cikin masu tauye ’yancin addini Assalamu alaikum, da fatan kowa muna lafiya, ameen. Mu sani cewa, kowane mutum da Allah ya yi, ya yi shi da irin nasa tunanin, kowa da yadda yake kallon abu idan ya zo masa, kamar yadda yake kuma kowa da irin nasa ra’ayin. Wasu ana iya kawar da su daga kan ra’ayinsa mummuna ko kyakkyawa, wasu kam ba yadda za a yi a iya kawar da su daga ra’ayin da suka ginu a kai. Irin wannan ra’ayi da fahimta da Allah ya yi kowa tasa daban, shi ne ya kamata a ce…
Read More
Zargin ɓata suna: Ɗan jarida ya maka jaridar Daily Trust, Gwamnatin Nasarawa da Yakubu Lamai a kotu

Zargin ɓata suna: Ɗan jarida ya maka jaridar Daily Trust, Gwamnatin Nasarawa da Yakubu Lamai a kotu

Daga WAKILINMU Tsohon ma'aikacin jaridar Daily Trust ya maka Daraktan Yaɗa Labarai ga Gwamnan Jihar Nasarawa, Mr. Yakubu Lamai, da jaridar Daily Trust da kuma Gwamnatin Jihar Nasarawa a gaban kuliya bisa zargin ɓata masa suna. Ibraheem Hamza Muhammad wanda tsohon wakilin jaridar Daily Trust ne a jihar Nasarawa, ya maka waɗanda yake zargin da ɓata masa suna a kotu ne ta hannun lauyansa, Barrister M. A. Danmama. Yayin zaman farko na sauraron shari'ar a Babbar Kotun Jihar Nasarawa mai zamanta a New Karu a ranar Talata, mai ƙarar ya yi iƙirarin cewa ya haɗa wani labari bayan kammala bincikensa…
Read More
Ya kamata matasa su himmantu wajen neman ilimi – Ƙungiyar masu motocin haya

Ya kamata matasa su himmantu wajen neman ilimi – Ƙungiyar masu motocin haya

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugaban ƙungiyar masu motocin haya da ɗaukar ma’aikata ta ƙasa wadda aka fi saninta da ‘Road Transport Employer of Nigeria’, Alhaji Musa Mohammed Mai Takobi Kano, kuma shugaban ƙungiya ta a birnin Legas, ya nemi matasan ƙasar nan da su zama masu ƙoƙarin neman ilimi tare da sana’o’in dogaro da kai domin kaucewa yawon gararanba a duk faɗin ƙasar nan. Alhaji Mai Takobi ya nemi hakan ne a birin Kano a lokacin da yake zantawa da waɗansu wakilan kafofin yaɗa labarai na ƙasa kuma yake bayyana masu abin da ya zama wajibi ga matasan ƙasar…
Read More
NURTW ta fara shirin rage cunkuso a Maraba

NURTW ta fara shirin rage cunkuso a Maraba

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ƙungiyar direbobin motocin sufuri ta ƙasa da aka fi sani da (NURTW) ta ce, ta ɗauki ƙwararan matakai don rage cunkosun ababen hawa da ake yawan fuskanta a garin Maraba da ke yankin ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa. Sakataren shirye-shirye na ƙungiyar a jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Gandu ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci mambobin ƙungiyar inda suka ƙaddamar da wani shiri na musamman don shawo kan lamarin. Shirin wadda suka yi wa lakabin ‘OPERATION PARK WELL’ a turance, an gudanar da shi ne a ƙarƙashin wani babban gada da…
Read More
Yadda ƙungiyoyin manoma suka tafka asarar kayan amfanin gona

Yadda ƙungiyoyin manoma suka tafka asarar kayan amfanin gona

Daga MUHAMMADU MUJITABA Ƙungiyoyin Manoman shekafa, dawa, masara da sauransu sun tafka sarar kayan amfanin gona mai ɗumbin yawa na billiyon naira da ba a tantance yawansa ba a wannan shekara sakamakon ƙarancin ruwa da aka samu a wasu wuraren na jihohin arewacin Nijiriya, wanda suka bayyana wa duniya domin dai sanar da hukumomin da sauran masu ruwa da tsaki domin ɗaukar mataki kamar yadda ya dace. Alhaji Samaila Abdullahi Wali shi ne shugaban masu sayar da kayan amfanin gona na zamani kuma ɗaya daga cikin ’yan ƙungiyar manoma da safarar kayan gona, ya ce, babu shakka a bana manoma…
Read More
Matafiya sun fusata sakamakon tsadar tikitin jirgin ƙasar Kaduna zuwa Abuja

Matafiya sun fusata sakamakon tsadar tikitin jirgin ƙasar Kaduna zuwa Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A safiyar yau talata ne aka ga fasinjoji a tashar jiragen ƙasa na Kaduna da ke Rigasa sun harziƙa kan yadda wasu mutane da ake zargin ba ma’aikatan Hukumar Jirgin Ƙasar ba ne na saran tikiti tare da sayarwa da tsada har sama da naira dubu goma. Wannan lamarin dai ya tilasta wa fasinjoji suka riqa sayen tikitin a kan farashin dubu goma wanda ya yi tsada ga talakawa a hannun ’yan kasuwar bayan-fage da ba a iya tantance ko su wane ne ba, kamar yadda wakilin Manhaja ya shaida. Tun a watan Janairu ne hukumar…
Read More
Yadda fursunoni 252 suka tsere daga kurkukun Jos bayan kai hari

Yadda fursunoni 252 suka tsere daga kurkukun Jos bayan kai hari

Daga HABU ƊAN SARKI Biyo bayan wani mummunan hari da wasu mahara da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba, suka kai babban gidan yarin Jos, dake ƙarƙashin Hukumar Kula da Gidajen Gyara Halinka ta Nijeriya, a ranar Lahadi da ta gabata 27 ga watan Nuwamba, an tabbatar da tserewar fursunoni 252, ciki har da waɗanda ake zaton an kai harin ne domin su. Babban Kwantirola mai kula da Cibiyar Gyara Halinka ta Jos, Samuel Aguda ya tabbatar da ɗan bindiga ɗaya ne daga cikin maharan da suka kai farmakin da muggan makamai aka kashe a cikin kurkukun…
Read More
Ko yau na bar shugabancin Jami’ar Nasarawa na kafa tarihi – Farfesa Sulaiman

Ko yau na bar shugabancin Jami’ar Nasarawa na kafa tarihi – Farfesa Sulaiman

Daga JOHN D. WADA a Lafiya A yayin da mahukuntan Babbar Jami’ar Jihar Nasarawa da Gwamnatin Jihar ke cigaba da murnar cikar jami’ar shekaru 20 da kafuwa, Wakilin Manhaja, John D. Wada, ya samu damar tattauna da shugaban Jami’ar Farfesa Suleiman Bala Mohammed inda ya bayyana nasarori da ƙalubale da jami’ar ke fuskanta kawo yanzu, da suka haɗa da shirin hura wisu wato 'whistle blowing policy' a Turance da ta kirkiro don gano tare da hukunta miyagun ɗalibai da malamanta, da batun ƙungiyoyin asiri da sauransu. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Manhaja: A kwanakin baya kun kafa wata doka ta…
Read More