Editor

9513 Posts
Jami’an tsaro sun hana ma’aikatan da ba a yi musu allurar rigakafi ba shiga sakatariyar Gwamnatin Tarayya a Abuja

Jami’an tsaro sun hana ma’aikatan da ba a yi musu allurar rigakafi ba shiga sakatariyar Gwamnatin Tarayya a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A halin yanzu an hana ma'aikatan gwamnati da sauran jama'ar da ba su da shaidar allurar rigakafin Korona na PCR daga shiga rukunin ginin gwamnati a Abuja. Sai dai ƙungiyar manyan ma’aikatan Nijeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta tsawaita wa’adin dokar hana ma’aikatan da ba su yi wa allurar rigakafi ba zuwa watan Maris na shekara mai zuwa, daga wa’adin yau na yin allurar dole ga ma’aikatan, matakin da Boss Mustapha ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa wanda kwamitin gudanarwa ya bayyana a matsayin abin da ba zai yiwu ba. Nijeriya a ranar Laraba kuma…
Read More
Zaɓen Anambra: Soludo ya sake samun nasara a kotu

Zaɓen Anambra: Soludo ya sake samun nasara a kotu

Daga BASHIR ISAH Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya tsallake siraɗin hana rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan Anambra ya zuwa watan Maris mai zuwa. Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Abuja ce ta yanke wannan hukunci a Larabar da ta gabata, inda ta ƙi bayyana zaɓen da Soludun ya lashe a matsayin mara inganci. Alƙalin kotun, Justice Taiwo Taiwo ya yi fatali da ƙarar da aka shigar a gabansa wanda aka nemi ya soke nasarar da Soludo ya samu a zaɓen da ya gabata bisa zargin miƙa wa hukumar zaɓe INEC bayanan ƙarya. Adindu Valentine da…
Read More
Sanata Barau ya raba wa ‘yan fim ɗin Hausa motoci da babura a Kano

Sanata Barau ya raba wa ‘yan fim ɗin Hausa motoci da babura a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, wato Sanata Barau I. Jibrin wanda aka fi sani da Maliya, ya yi taron bayar da tallafi ga ƙungiyoyin finafinan Hausa na Kannywood. Taron wanda ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata a ɗakin taro na Mina Event Center da ke cikin birnin Kano, ƙarƙashin jagorancin Comrade Isayaku Abubakar Balan da kuma jami'in shirye-shirye Honarabul Nasiru Yusuf Shuwaki, wanda shi ne shugaban Kano Progressive Media Network (KAPMEN). Tun da farko a jawabinsa, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar ya ce wannan tsari na Maigirma Sanata na…
Read More
’Yan APC shiyyar Arewa Maso Yamma sun karrama Gwamna Badaru

’Yan APC shiyyar Arewa Maso Yamma sun karrama Gwamna Badaru

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Ƙungiyar matasan jam'iyyar APC na arewacin Nijeriya sun karrama Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar saboda ƙoƙarinsa na cusa wa matasa ɗa'ar siyasa. An yibikin karramawar ne a ranar Asabar da ta gabata a filin Foke na Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhd Sunusi da misalin ƙarfe goma na dare. Bikin ya samu wakilcin matasa daga jihohin Zamfara, Kebbi, Kaduna, Katsina, Sakkwato, Kano da jihar Jigawa mai masaukin baƙi. Matasan sun shirya gagarimar liyafa ga Gwamna Badaru, har ma an yi yayyafin Naira ga matasan mawaƙa da suka baje basirarsu a wurin taron…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan sandan Kano sun garƙame ofishin lauyan Shekarau bayan kayar da Ganduje a kotu

Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan sandan Kano sun garƙame ofishin lauyan Shekarau bayan kayar da Ganduje a kotu

Daga WAKILINMU Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa, jami'an Ma'aikatar Filaye ta Jihar tare da haɗin gwiwar 'yan sanda sun garƙame ofishin lauyan Sanata Shekarau, Nureini Jimoh, SAN, da ke lamba 16c kan titin Murtala Mohammed. A Talatar da ta gabata lauya Jimoh ya wakilici ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau na APC inda suka samu nasara a kan ɓangaren Gwamna Abdullahi Ganduje. Lauyan Shakarau ya tabbatar wa jaridar Daily Nigerian da batun garƙame ofishin nasa, yana mai cewa shi da ma'aikatansa da sauran jama'ar da ke ginin lamarin ya shafa. "Maganar da nake yi, yanzu haka ina cikin ginin ne…
Read More
Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mutum 40 a Kano

Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mutum 40 a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Aƙalla mutane 40 wanda akasari mata da yara ne aka ruwaito sun rasa rayukansu a qauyen Badau da ke qaramar hukumar Bagwai a jihar Kano sakamakon wani hatsarin kwale-kwale. Wani wanda abun ya faru a gaban idonsa wanda kuma ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, hatsarin ya faru ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 6 na yamma. Ya bayyana cewa, kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar kogin yayin da yake jigilar fasinjoji zuwa garin Bagwai daga ƙauyen Badau. Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun mutu ne a cikin kogin saboda ba za su…
Read More
Kotu ga Gwamna Ganduje: Sai ka biya Sanusi Naira miliyan 10 bisa fatattakar sa daga Kano

Kotu ga Gwamna Ganduje: Sai ka biya Sanusi Naira miliyan 10 bisa fatattakar sa daga Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata da ta gabata, ta bayyana cewa korar Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi II, ko zuwa Jihar Nassarawa bayan an tsige shi daga sarautar Kano ya saɓa wa dokar ƙasa. Alƙalin kotun, Anwuli Chikere, a hukuncin da ya yi , ya bayyana cewa dokar kafa Masarautar Kano ta 2019 da gwamnatin jiha ta kafa ta kuma yi amfani da ita wajen korar Sarki Sanusi bayan ta tsige shi ta saɓa wa kundin tsarin mulki na 1999. Ya ce kundin tsarin mulkin ƙasar…
Read More
2023: Osinbajo ya nesanta kansa da buɗe ofishin yaƙin neman zaɓe

2023: Osinbajo ya nesanta kansa da buɗe ofishin yaƙin neman zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ofishin yaƙin neman zaɓe da wasu masoyan mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbanjo suka buɗe masa a Abuja. Wasu da suke ikirarin magoya bayan mataimakin shugaban Nijeriya ne sun buɗe ofishin tallata shi domin ya tsaya takarar shugabancin ƙasar a shekara ta 2023. Mutanen, waɗanda ke ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna The Progeressive Project, wato TPP a taƙaice, sun bayyana cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya cancanci shugabancin Nijeriya idan aka yi laakari da iliminsa da kuma ɗabiunsa. Sakatariyar magoya bayan mataimakin shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya tsaya takarar shuganbancin ƙasar a babban…
Read More
Su waye tsoffin gwamnonin masu son fafatawa a neman kujerar shugabancin APC

Su waye tsoffin gwamnonin masu son fafatawa a neman kujerar shugabancin APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tun bayan kammala zabukan shugabannin babbar jam'iyyar hammaya ta PDP a Nijeriya hankula suka karkata kan jam'iyya mai mulki, APC, domin ganin yaddaa za ta kaya.Hakan ba ya rasa nasaba da ƙurar da rikicin da ya ɓarke a wasu jihohi bayan zaɓukan da jam'iyyar ta APC ta gudanar kamar yadda aka gani a jihohi irin su Kano da Zamfara da Kwara da dai sauransu. Sai dai a yayin da jam'iyyar take fama da matsalolin da suka faru sakamakon zaɓen cikin gida, a gefe guda kuma tuni wasu manyan 'yan siyasa suka soma fafutikar ganin…
Read More
Babu abin da ya fi kasuwanci daɗi a wannan zamani – Dije Abdulƙadir

Babu abin da ya fi kasuwanci daɗi a wannan zamani – Dije Abdulƙadir

“Dole sai matasa sun cire girman kai da raina ƙaramar sana'a za a samu cigaba” Daga ABUBAKAR M TAHEER a Haɗejia Mai karatu, wannan tattaunawa ce ta musamman da Hajiya Dije Abdulƙadir, wacce ’yar kasuwa ce kuma mai fafutukar wayar da kan mata muhimmanci neman na kansu. A cikin zantawar, ta kawo yadda ta fara kasuwanci da ƙaramin jari har ta zama babbar 'yar kasuwa wadda take sana'arta a yanzu ta hanyar yanar gizo da dai sauran bayanai. A sha karatu lafiya: MANHAJA: za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu.DIJE ABDULƘADIR: Assalamu alaikum warahamatullahi wa baraka tuhu.…
Read More