Editor

9513 Posts
Ko layin wayar Starlink zai iya gogawa da MTN, Airtel da Glo?

Ko layin wayar Starlink zai iya gogawa da MTN, Airtel da Glo?

Daga AMINA YUSUF ALI Ko shin sabon layin sadarwa na Starlink zai iya goga kafaɗa da kamfanonin sadarwa na MTN da Glo a Nijeriya? Wannan ita ce tambayar da akasarin masu bibiyar al'amuran yau da kullum suke yi kenan.  Shi dai wannan sabon layin waya mai suna Starlink mallakin kamfanin wannan biloniyan ba'amurken ne, Elon Musk wanda alƙaluma suka tabbatar da cewa ya fi kowa ƙarfin arziki a Duniya. A yanzu haka rahotanni sun tabbatar da cewa Elon Musk yana da ƙudurin kamfanin zai shigo ƙasar Nijeriya da ƙarfinsa ya kafa sansanin kasuwanci a Nijeriya a shekara mai zuwa domin…
Read More
Buhari ya hana jiragen attajirai 91 tashi sakamakon gaza biyan haraji

Buhari ya hana jiragen attajirai 91 tashi sakamakon gaza biyan haraji

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ta bayar da umarni ga hukumar Kwastan da su dakatar da wasu jirage 91 masu zaman kansu, mallakin wasu masu ƙumbar susa a ƙasar nan. A kan rashin biyan haraji sama da Naira biliyan 30.  Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ranar 7 ga watan Yunin shekarar nan, hukumar kwastan ɗin ta fara aikin tantance jiragen saman masu zaman kansu inda ta nemi masu mallakin jirage masu zaman kansu da su garzayo ofishin hukumar domin tantancewa tare da satifiket ɗin jirgin saman, da lasisinsa…
Read More
Litar mai ta tada kowa daga barci

Litar mai ta tada kowa daga barci

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Kama daga mai minshari zuwa kwanta shiru har wanda ya yi likimo a cikin talakawan Nijeriya ya yi zumbur ya farka musamman a makon jiya don labarin da ya shafi litar man fetur. Matuƙar aka taso da maganar man fetur, to a na nufin kayan masarufi koma duk abin da a ke sarrafawa a gida ciki kuwa har da tattasai da tumatur da albasa. Me ya sa talakawa ba za su farka ba tun da ko gabanin babban labari kan shirin karin farashin man fetur su na kokawa na tashin farashin kayan abinci sanadiyyar fakewa da…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Ɗaya daga cikin malaman da suka yi muƙabala da Sheikh Abduljabbar Kabara ya rasu

Da ɗumi-ɗumi: Ɗaya daga cikin malaman da suka yi muƙabala da Sheikh Abduljabbar Kabara ya rasu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Guda daga cikin malaman da suka yi muƙabala da Malam Abduljabbar Kabara, Malam Mas’ud Mas’ud Hotoro ya rasu. Rahotanni da MANHAJA ta samu sun nuna cewa Malam Mas’ud ya rasu ne a daren ranar Larabar da ta gabata sakamakon haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya Idan za a iya tunawa dai malamin na ɗaya daga cikin mutum huɗun da suka yi muƙabala da Sheikh Abduljabbar Kabara a kwanakin baya. Kazalika, Malamin shi ne wanda ya wakilci ɓangaren Ƙadiriyya yayin zaman muƙabalar. Rahotannin sun bayyana cewa an yi wa Malamin jana’aiza…
Read More
Marubuta mutane ne masu wuyar sha’ani – Zaharadden Kallah

Marubuta mutane ne masu wuyar sha’ani – Zaharadden Kallah

“Dole marubuci ya zama makaranci” Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Idan ana maganar rubutu da ƙungiyoyin marubuta, musamman shahararriyar ƙungiyar nan ta marubutan Nijeriya, wato 'Association of Nigerian Authors' (ANA), to tabbas za a sa sunan baƙonmu na yau. Wannan ba kowa ba ne sai Zaharadden Ibrahim Kallah, domin kuwa ya shekara 25 a harkar rubutu, jajirtacce ne kuma mai matuqar ƙwazo, wanda da ƙoƙarinsa ne ƙungiyar ANA reshen Jihar Kano ta kafu. Wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, ya zanta da shi. Don haka ku biyu mu don jin yadda hirar za ta kasance: Manhaja: Za mu so jin…
Read More
Hanyoyin magance ciwon basur

Hanyoyin magance ciwon basur

Daga ABILKISU YUSUF ALI Yadda ciwon basir ya ke da hanyoyi da yawan gaske da ke haifar da shi sannan yake da alamomi da ke nuna alamunsa haka kuma hanyoyin magance shi yake da yawan gaske. Akwai basir da ba ya buƙatar shan magani ana iya magance shi ne da ɗabi’a, wato yanayin rayuwa ta yau da kullum ko kuma abin da ake ci. Sannan akwai basir da na lokaci ne in wannan yanayin ya wuce da dama ana samun waraka. Misali, mai ciki, Basir kan dami mai juna biyu wanda nauyin ɗa ne ke janyo shi, irin wannan basur…
Read More
Google ya haramta tallata bayanan siyasa a shafukansa a Philippine

Google ya haramta tallata bayanan siyasa a shafukansa a Philippine

Daga BASHIR ISAH Kamfanin Google ya bayyana cewa, ba zai lamunci tallata bayanan siyasa ba a shafukansa. Rashin amincewar kamfanin na da nasaba da babban zaɓen ƙasar Philippine da za a gudanar shekara mai zuwa. Da yake ƙarin haske game da yaɗa bayanan siyasa a shafukansa kamfanin Google ya ce, “Dangane da zaɓaɓɓukan Philippine na 2022, ba a yarda a yaɗa bayanan siyasar ƙasar ba kama daga ranar 8 ga Fabrairu zuwa 9 Mayu, 2022. “Tallar siyasa talla ce da ke tallata jam'iyya ko ɗan takara ko akasin haka don neman jagorancin al'umma." Ma'aikatar Zaɓe ta Philippine ta ce, 8…
Read More
Gwamnatin Legas ta yi watsi da rahoton kashe masu zanga-zangar EndSARS tara a Lekki

Gwamnatin Legas ta yi watsi da rahoton kashe masu zanga-zangar EndSARS tara a Lekki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin jihar Legas ta fitar da farar takardarta kan rahoton da kwamitin bincike kan zanga-zangar EndSARS ya gabatar ma ta wanda ya binciki lamarin da ya faru a ƙofar Lekki a ranar 20 ga Oktoba, 2020. Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, a safiyar ranar Talata yayin ganawa da manema labarai, ya yi alƙawarin cewa za a fitar da farar takarda a ranar Talata. Sai dai gwamnan ya yi watsi da rahoton kwamitin na cewa mutum tara kawai aka kashe a ƙofar karɓar haraji lokacin da sojoji da ‘yan sanda suka harbe masu zanga-zangar lumana. Sanwo-Olu ya bayyana…
Read More