05
Dec
Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Najeriya na fuskantar ƙarancin ruwan sha, wanda hakan ya biyo bayan bincike da masana a harkar ruwa suka gabatar. Kamar yadda binciken ya nuna matuqar gwamnatocin ba su ɗauki mataki kan matsalar ba jama'a za su fuskantar ƙalubale mai tarin yawa ta fuskar samun ruwan sha. Waɗannan bayanai sun fito ne a wani taron kwanaki uku da hukumar samar da ruwan sha ta ƙasa ta shirya a jahar Jigawa da nufin samar da bakin zaren. Wani masani akan harkar ruwan sha, Ambasada Rabiu Dagari wadda shine Babban Darakta a Hukumar hulɗa da ƙasashen waje,…
