Me ke wahalar da Ganduje a kotu?

*Cikin shari’u huɗu an kayar da shi uku
*Shin ko dai tsiyar nasara sai za shi gida ne?

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A cikin shari’u guda huɗu mafi shahara da Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi a gaban kotuna, sau ɗaya kawai ya yi nasara, inda ya sha kayi a guda uku.

Shari’ar da ya yi nasara ita ce wacce ya kara da ɗan takarar PDP a zaɓen 2019, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-gida), amma dukkan ukun da suka biyo bayan wannan shine ya kai ƙasa. Sauran shari’un uku su ne, na rikicin gwamnan da Mawallafin jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, da rikicin siyasar cikin gida na Jam’iyyar APC tsakaninsa da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, da kuma wacce ya fafata da Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi II. Duka bai ji da daɗi ba. To, amma shin bayan tiya akwai wata caca?

Ko kuwa irin abin nan da a ke cewa, tsiyar Nasara sai za shi gida ne? A yayin da Manhaja ta tuntuvi ƙwararren lauya mazaunin Kano kuma mai bibiyar harkokin siyasar jihar, Barista Nazir Adam, ya ce, a shari’ar Gwamna Ganduje da Jaafar Jaafar babu wanda ya yi nasara kuma babu wanda aka kayar, domi n mai ƙara ne ya janye ƙararsa. Wannan ne dalilin da ya sa kotu ta nemi gwamnan da ya biya wanda ya ke ƙara Naira 800,000, saboda ɓata masa lokaci da ya yi. Don haka sai a jira a ga hukuncin da kotun Abuja za ta yi kan shari’ar tunda gwamnan can ya je ya shigar da sabuwar ƙara bayan janye ta kotun Kano.

Tun bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Kano da aka gwabza tsakanin ɗan takarar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, wanda ake yi wa laƙabi da Abba Gida-gida a shekarar 2019, sai gwamnan ya dinga fuskantar ƙalubalen shari’a a gaban kotu akan nasarar sa daga ɓangaren jam’iyyar adawa, inda jam’iyyar ta ke yin ƙorafin INEC ba ta gudanar da zaɓen cikin mutunta dokoki da kundin tsarin mulkin ƙasar ba.

Duk da cewa, ko a wancan lokacin mutane da dama, musamman masu fashin baƙi akan al’amuran siyasar Nijeriya, su ma su na ganin kamar an yi amfani da ƙarfin mulki tare da amfani da jami’an tsaro ne wajen yin ƙarfafa a zaɓen gwamnan na Jihar Kano.

Kafin nan kuma, sai batun bidyon karvar daloli da jaridar Daily Nigerian ta wallafa a shafinta a watan Oktobar 2018, da ke nuna Gwamna Ganduje na karɓar bandiran kuɗi a matsayin cin hanci da yawansu ya kai Dala miliyan biyar, a cewar jaridar, amma fa gwamnatin jihar ta ce bidiyon na bogi ne. Lamarin ya sa Ganduje ya garzaya kotu, don a bi ma sa kadi kan zargin ɓata ma sa suna da mawallafin jaridar, Jaafar Jaafar, ya yi. 

Wannan bidiyo da ake zargin an nuno Ganduje yana soke Daloli a aljihun babbar rigarsa da jaridar ta ce wani ɗan kwangila ne ya yi amfani da biro da agogon hannu wajen naɗar hotunan bidiyon, ya ja ra’ayin al’ummar Nijeriya ciki har da manyan ’yan siyasa wajen bayyana ra’ayinsu gami da caccakar Gandujen, inda wasu kuma har yanzu suke kwaikwayon hoton bidiyon a matsayin raha ko shaguɓe ko shaƙiyanci ga Gwamna Ganduje ɗin. 

Ƙalubale da barazanar da mawallafin Jaridar Daily Nigerian ya ce yana fuskanta, ciki har da barazanar kisa, ta tilasta shi tattara iyalansa da shi kansa, don barin ƙasar, inda ya gudu zuwa Birnin London, bayan ɗan lafawar shari’arsa da Ganduje, kafin daga bisani gwamnan ya sake shigar da sabuwar ƙara gaban kotu a Abuja.

A haka dai gwamnatin Ganduje ta riƙa rarrafawa cikin tarkon shari’a da shan suka daga wajen magoya bayan ɗan takarar Jam’iyyar PDP har ta kai ga a ƙarshe ya samu nasara akan Abba Kabir Yusuf a Kotun Ɗaukaka Ƙara, lamarin da ya shammaci wasu da suke kallon zaɓen a matsayin mafi munin zaɓe (inji wani ɗan siyasa) da aka gudanar daga ƙarshe, wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta yi wa laƙabi da ‘Inconclusive’, wato zaɓen da bai kammalu ba.

Tun waccan nasara da Gwamna Ganduje ya samu a kotu, sai kuma ana nan wata sabuwar varaka ta kunno tsakanin Masarautar Kano da kuma Fadar Gwamnatin Kano, inda ake kallon kallo tsakanin ɓangaren gwamnati da kuma Masarautar Kano, ƙarƙashin Mai Martaba Sarkin Kano 14, Malam Muhammadu Sanu II, inda gwamnatin Kano ke zargin Muhammasu Sanusi da yi ma ta katsalandan akan al’amuran gudanar da mulki da kuma bayyana Sarki Sanusi a matsayin sarkin da bai da biyayya ga umarnin ofishin gwamna da sauran hukumomin gwamnati, ciki har da rashin halartar tarukan da gwamnati ke gayyatar sa ba tare da bayar da ƙwaƙƙwarar hujja ba.

Da kuma wasu zarge-zargen da ake ganin su ma su na daga cikin musabbabin ruruwar wutar da ta tashi tsakanin ɓangaren masarauta da kuma gwamnati sun haɗa da siyasa, sukar manufofin gwamnati da kuma abinda ake ganin ba ta shafi sarkin ba amma yana tsoma baki cikin suka da kakkausar magana ga gwamnatin Ganduje.

Wasu su na ganin waɗancan matsaloli ne suka sa Gwamnatin Jihar Kano ta ƙirƙiro da qarin masarautu huɗu a faɗin jihar, domin rage wa Sarki Sanusi ƙarfi, inda gwamnan ya ƙirƙiro da masarautar Gaya, Ƙaraye, Bichi da kuma Rano.

Da wutar rikicin ta kasa cinyewa bayan ƙirƙirar waɗancan masarautu ne, sai Gwamna Ganduje ya bada sanarwar tsige Sarki Sanusi ranar 9 ga Maris, 2020, yayin da kuma gwamnatin jihar ta shiga terere da sarkin bayan da ta kore shi jihar, zuwa ƙauyen Loko da ke Jihar Nasarawa, bayan wasu ‘yan kwanaki sarkin ya tafi Jihar Ikko don yin zaman sa can. Lamarin da ya sa Sarki Sanusi ya shigar da qara a kotu kan zargin cin mutuncin sa da kuma karyar tsarin kundin mulkin Nijeriya na 1999.

Hausawa dai suna wani irin salon magana da suke cewa ‘mai haƙuri mijin mai nasara’. To a haka dai shari’o’in biyu suka kama tafiya, inda daga ƙarshe Jaafar ya yi nasara akan gwamnan bayan da ya janye ta, yayin da kuma kotu ta umarci Ganduje ya biya kamfanin jaridar da mawallafinta tarar kuɗin vata lokaci da ya yi musu akan shari’ar har zunzurutun kuɗi Naira 800,000, wanda Jaafar ya bayyana makonni biyun da suka gabata cewa kuɗin sun shiga asusun ajiyarsa lakadan ba ajalan ba, har ma ya kasafta kuɗaɗen ga mabuƙata ɗalibai da marasa lafiya a Jihar Kano.
 
Haka batun ya ke a ɓangaren shari’ar Sarki Sanusi da gwamnatin Jihar Kano da wasu manyan jami’an Nijeriya, inda wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talatar da ta gabata, ta bayyana cewa korar Sarkin Kano 14 zuwa Jihar Nassarawa bayan an tsige shi daga sarautar Kano ya saɓa wa dokar ƙasa.

Alqalin kotun, Anwuli Chikere, a hukuncin da ya yi, ya bayyana cewa dokar kafa Masarautar Kano ta 2019 da gwamnatin jiha ta kafa ta kuma yi amfani da ita wajen korar Sarki Sanusi bayan ta tsige shi ta saɓa wa kundin tsarin mulki na 1999. Ya ce, kundin tsarin mulkin ƙasar shi ne a gaba kuma duk wata doka da a ka ƙirƙire ta ba a doron kudin ba, to ba abar karɓa ba ce. Alƙalin ya ƙara da cewa tsohon sarkin na Kano yana da ‘yancin da zai zauna a ko’ina a faɗin ƙasar nan har da ma Jihar Kano.

Kamfanin Daillancin Labara na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, bayan da aka tsige sarkin a ranar 9 ga Maris, 2020, sai ya kai ƙarar Babban Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa da Babban Daraktan Hukumar DSS na Ƙasa da kuma Gwamnatin Jihar Kano tun a ranar 12 ga Maris, 2020 inda ya ke ƙalubalantarsu kan cewa an tsare shi ba bisa haƙƙinsa ba. Haka kuma a cikin waɗanda ya kai ƙarar har da Antoni Janar na jihar da na ƙasa.

Saboda haka alƙalin ya umarci masu ƙara na 1 da na 2 da 3 su biya Sarkin Naira miliyan 10 da kuma ba shi haƙuri ta kafafen yaɗa labarai.

Da ya ke martani a kan wannan hukuncin, Antoni Janar na Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Mohammed Lawan, ya bayyana cewa, sun ji hukuncin kuma za su yi nazari a kai.

Da ya ke ganawa da manema labarai, Lawan ya ce, gwamnatin jiha ta yi daidai da ta tsige Sarki Sanusi, saboda ya sa ƙafa ya rushe al’adar Masarautar Kano.

Makamantan irin wannan tirka-tirka da shiga kotu sun dabaibaye gwamnatin Ganduje har a vangaren siyasar jam’iyyar jihar, inda a rikicin na kwanan nan, ya shafi rikicin cikin gida na jam’iyyar APC a Kano, inda ta dare gida biyu, ɓangaren tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da kuma ɓangaren Abdullahi Ganduje ne wanda kowane ɓangare ya gudanar da zaven shugaban jam’iyyar APC a jihar, lamarin da ya sa ɓanɓaren Shekarau ruga wa gaban kotu, don warware matsalar da tabbatar da Alhaji Haruna Ahmad Ɗanzago a matsayin halastacce kuma zaɓaɓɓen shugaban APC a jihar.

Kamar waɗancan shari’un na baya, wannan ma Ganduje bai yi nasara ba, domin a Litinin xin makon nan Babbar Kotun Abuja ta amince da zaven shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Kano vangaren Malam Ibrahim Shekarau, wanda ke qarqashin jagorancin Xanzago, yayin da ta yi watsi da vangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Alqalin kotun xaukaka qara da ke Abuja Hamza Mu’azu ya yanke hukuncin amincewa da vangaren tsohon gwamnan sakamakon qarar da ya shigar, inda yake qalubalantar halarcin vangaren gwamnan mai ci wanda aka zavi Alhaji Abdullahi Abbas.

Wannan ya biyo bayan tarurrukan jam’iyyar guda biyu da aka yi a birnin Kano a ranar 16 ga watan Oktoba,wanda Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Shekarau suka jagoranta a wurare daban-daban.

Kafin hukuncin kotun, kwamitin kula da ƙararrakin zaɓe na jam’iyyar APC ya amince da ɓangaren Gwamna Ganduje wanda aka zaɓi Abdullahi Abbas, yayin da ɓangaren Malam Shekarau ya ruga kotu domin neman haƙƙin su.

Wani lauya mai zaman kansa da ke zaune a Kaduna, Barista El-Zubair Abubakar, ya ce, “dole ne kotu ta amshe kujerar ɓangaren Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje, saboda ba su saka Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ba a lokacin gudanar da zaɓen, amma vangaren Shekarau INEC tana wajen,” inji shi.

A ɓangaren siyasar sa kuwa, Barista El-Zubair ya ce, “duk da ba san alƙibalar da ya dosa ba a siyasa, amma ya nuna ƙara yana goyon bayan Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari, to siyasar sa za samu gagarumin rauni duba da kayen da yake sha a gaban kotu.” Shin me ya sa Ganduje ke shan kayi a duk shari’o’in da ake yi da shi? 

Masu nazari da fashin baƙi suna ganin hakan ba ya rasa nasaba da salon siyasarsa, kamar yadda wani mazaunin Kano kuma ɗan siyasa da ya nemi a sakaya sunan sa ya bayyana wa Manhaja, ya ce “kashi 70 cikin ɗari na talakawan Jihar Kano ba sa tare da Ganduje, ba shi suka zaɓa ba, kujerar ta sa ma kamar fashinta aka yi,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, “haka ɓangaren manyan ‘yan siyasa masu mutunci a Jihar Kano, su ma ya vata da su, ba ya tuntuvar su don neman shawarwari a matsayin su na ƙwararrun ‘yan siyasa.”

Idan haka ne kuwa, to wace kujerar siyasa Ganduje zai nema nan gaba, har ya yi wani tasiri na a-zo-a-gani a Jihar Kano duba da yadda waɗancan matsaloli suka ƙara fito da wasu sirrika a siyasar sa. Shin ƙwararan hujjoji ne gwamnan bai da su kafin zaman kotu ko kuwa nasara ce bai samu? Lokaci ne kawai zai tabbatar da wannan iƙirari.