Editor

9513 Posts
Buhari ya nuna alhininsa kan rasuwar Janar Wushishi

Buhari ya nuna alhininsa kan rasuwar Janar Wushishi

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shiga cikin jerin 'yan ƙasa da ke ci gaba da nuna alhininsu dangane da rasuwar tsohon Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya, Janar Mohammed Inuwa Wushishi, tare da bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya. Buhari ya ce gudunmawar da marigayin ya bayar ga cigaban ƙasa a halin rayuwarsu abu ne mara misaltuwa. Sanarwar da ta fito ta hannu mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu a jiya Lahadi, ta nuna Buhari ya ce, “Janar Wushishi ya yi aiki mai tsafta a matsyinsa na soja kuma muna alfahari da…
Read More
Amarya a Zamfara ta nemi saki mako guda da tarewarta saboda girman mazakutar mijinta

Amarya a Zamfara ta nemi saki mako guda da tarewarta saboda girman mazakutar mijinta

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wata mata mai suna Aisha Dannupuwa da ta yi aure mako ɗaya da ya gabata a Jihar Zamfara, ta roƙi kotun shari’ar Musulunci da ta raba aurenta. Matar da ke zaune a yankin Samaru cikin ƙaramar hukumar Gusau ta jihar ta ce, dalilin da ya sa ta buƙaci a raba auren na ta shi ne saboda girman mazakutar mijinta. Da ta ke ba da labarin abin da ya faru, ta bayyana cewa, jima'i da mijinta a daren aurensu na farko ya yi matuƙar tada ma ta da hankali. Aisha Dannupuwa, ta ce, “lokacin da ya…
Read More
Tinubu ya gana da Sanata Shekarau a asirce

Tinubu ya gana da Sanata Shekarau a asirce

Daga BASHIR ISAH Jagoran APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi baƙuncin tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau inda suka yi ganawar sirri. Kafin ganawar tasu, sai da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da takwaransa Abubakar Badaru na Jigawa suka ziyarci Kano inda suka nuna goyon bayansu ga ɓangaren Shekarau na jam'iyyar APC ƙarƙashin shugabancin Ahmadu Haruna Zago (Ɗanzago). Sai dai babu wani cikakken bayania kan abin da Shekarau da Tinubu suka tattauna yayin ganawar tasu, amma rashin ganin Ganduje a wajen ganawar ya haifar da tambayoyi da dama masu neman jawabi. Rikicin APC a Kano ya…
Read More
Nijeriya za ta ƙaddamar da shirin zaman kotu na zamani ‘Virtual’ – Malami

Nijeriya za ta ƙaddamar da shirin zaman kotu na zamani ‘Virtual’ – Malami

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya bayyana cewa, an shirya tsaf don ƙaddamar da shirin shari’o’in kotun ƙoli na zamani ‘Virtual’ a cibiyoyin gyaran hali na Nijeriya. Malami ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Dakta Umar Gwandu, mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ya fitar ranar Juma’a a Abuja.Ya ce, shirin zai fara aiki ne daga cibiyar gyaran hali na Kuje da ke Abuja a ranar 6 ga watan Disamba. “Waɗanda ake sa ran a wajen taron sun haɗa da Ministan Harkokin Cikin Gida,…
Read More
Harin ISWAP a Maiduguri ya yi sanadiyar jin raunin yarinya ‘yar watanni

Harin ISWAP a Maiduguri ya yi sanadiyar jin raunin yarinya ‘yar watanni

Daga AISHA ASAS Rundunar 'yan sanda ta Jihar Barno ta tabbatar da jin raunin yarinya 'yar watanni shida da haihuwa a sanadiyar harin da ƙungiyar 'yan ta'adda ta ISWAP ta kai a Maiduguri ta hanyar jefo bama-bamai har biyar. Kwamishinan 'yan sanda Abdul Umar, ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN cewar, maharan sun harbo bama-bamai ne daga wajen filin jirgin sama na Ngomari, wanda ke bayan jami'ar Barno. Ya ƙara da cewa, harin na su ya sauka a wurare ma-banbanta, hakan ne ya sa ba a samu hasarar rayuka ko kuma manyan raunuka ba. Kwamishinan ya ce,…
Read More
Ngozi Iweala ta shiga jerin fitattun mata 25 na duniya

Ngozi Iweala ta shiga jerin fitattun mata 25 na duniya

Daga AISHA ASAS Haifaffiyar Nijeriya, kuma 'yar ƙabilar Ibo, Ngozi Okonjo-Iweala, ta cira tuta a jerin matan Nijeriya ta hanyar zama ɗaya daga cikin fitattun mata 25 da suka yi suna tare da taka wata muhimmiyar rawa a duniya. Fitacciyar Jaridar kasuwanci ta duniya ce ta bayyana hakan wato 'Financial Times'. Okonjo-Iweala wadda ta kasance babbar darakta ta Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya, ta zama ta farko a jerin sunaye 25 na fitattun mata masu faɗa a ji a duniya, duk da cewa jaridar ta 'Financial Times' ta bayyana cewar, ba sun fitar da jerin sunayen ne bisa fifiko ba. FT…
Read More
Mawaƙan Annabi suna rayuwa ne a gaɓa mai haɗari, inji Mahmoud Nagudu

Mawaƙan Annabi suna rayuwa ne a gaɓa mai haɗari, inji Mahmoud Nagudu

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Mahmoud Isma’il Ibrahim, wanda aka fi sani da Mahmoud Nagudu, fitaccen mawaƙi ne a fagen yabon Manzon Allah (SAW) tun yana ƙaramin yaro, sai dai ya yi fice ne a fagen waƙoƙin fim a shekarun baya. Amma dai yanzu ya daɗe ba a jin ɗuriyarsa a fagen waƙoƙin Nanaye, sai na yabon Manzon Allah kaɗai. Kasancewarsa mai ilimi a fagen yabon, ya sa Wakilin Manhaja a Kano, Mukhtar Yakubu, ya nemi tattaunawa da shi a kan abubuwan da yabon ya ƙunsa a fage na ilimin musamman ganin yadda a ke tafiyar da tsarin kara-zube a…
Read More
Sanata Yahaya ya raba kaya a makarantun sakandare a mazaɓarsa

Sanata Yahaya ya raba kaya a makarantun sakandare a mazaɓarsa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi A cikin shirinsa na tallafa wa ɓangaren ilmi, Sanata mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi ya raba kaya a makarantun sakandare huɗu da ke mazabarsa da suka haɗa da makarantar maza ta Kanta Unity College Argungu da makarantun mata na Augie, Argungu da kuma Ɗakingari. Kayan dai sun haɗa da katifu 396, zannuwan gado 396 da filallu 396, inda kowace makaranta ta samu 99 daga cikin kayan, sauran sun haɗa da manyan tukwanen girki 60 cokula farantin cin abinci dozin ashirin-ashirin,…
Read More
FOMWAN ta buƙaci reshenta na Bauchi ya kafa manyan makarantu

FOMWAN ta buƙaci reshenta na Bauchi ya kafa manyan makarantu

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Ƙungiyar Mata Musulmi Ta Nijeriya (FOMWAN) ta buƙaci reshen ta na jihar Bauchi ya kakkafa manyan makarantun koyar da ilimi a cikin jiha domin bunƙasa cigaban ilimin mata da matasa. Kamar yadda Amirar ƙungiyar ta ƙasa, Rafi’at Idowu Sanni ta ce, ire-iren waɗannan manyan makarantu kamar Jami’ar Koyon Haɗa Magunguna ko Kwalejin FOMWAN kan likitancin ungozomanci (HealthTechnology) da Cibiyar fasahar Sadarwa (ICT), da makamantansu. Amira ta qasa ta ƙungiyar FOMWAN tana jawabi ne a yayin buɗe gangami akan ilimi na kwanaki biyu da reshen qungiyar na jihar Bauchi ta shirya mai taken “Cimma Muradun…
Read More
Kwastam sun kama tabar wiwi ta kimanin Naira miliyan 18 a Katsina

Kwastam sun kama tabar wiwi ta kimanin Naira miliyan 18 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Kwastam reshen jihar Katsina ta kama tabar wiwi wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan sha takwas da dubu ɗari ɗaya a watan da ya gabata na Nuwamba. Muƙaddashin Shugaban hukumar reshen jihar Katsina, Ɗalhatu Wada Chedi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da hukumar ta kira don sanar da jama'a nasarar da ta samu a yaqi da hana shigowa da haramtattun kayayyaki a Nijeriya. Wada Chedi ya bayyana cewar an kama wasu mutane biyu ne ɗauke da tabar ta wiwi ƙunshi 230 a lokacin da suke ƙoƙarin shigowa da ita cikin…
Read More