Gwamna Badaru zai samar wa gwarazan ‘Hikayata’ aiki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya ce zai samar wa gwarazan gasar Hikiyata ta BBC Hausa aikin yi da zarar sun kammala karatun su.

Gwamna Badaru ya faɗi hakan ne a wajen taron karrama waɗanda suka lashe gasar ta bana, wanda ya gudana a ɗakin taro na Ladi Kwali da ke Sheraton Otel a Abuja.

Badaru ya bayyana cewa yana da alfarma a wajen gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai, don haka zai roƙe shi da ya ɗauki Aisha Musa Dalil da ta zo ta ɗaya a gasar da kuma Zulaihat Alhassan, wadda ta kasance ta uku aiki gwamnati a jihar sa da zarar sun kammala karatun su. Haka zalika ya ce idan kuma Aisha Musa Dalil a Adamawa take buƙata, to can ma gwamnan yana da alfarma.

Haka kuma ga wadda ta kasance ta biyu a gasar, wato Nana Aicha Hamissou Abdoulaye daga Jamhuriya Nijar, Gwamna Badaru Abubakar ya ce zai sanar da Shugaba Bazoum, don shi ma suna da kyakkyawar alaƙa da shi, inji gwamnan.

Da qarshe Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya bayyana irin wannan ƙwazo na matasan ‘yan matan a matsayin wani tubali da zai kawo gyara a Nijeriya, musamman lokacin da ake cikin wani yanayi na matsalar tsaro da kuma taɓarɓarewar tarbiyya.

Gasar ta bana dai ita ce gasar da mafi ƙarancin shekaru suka lashe tun lokacin da BBC Hausa ta fara shirya wa mata gasar, inda ‘yar shekara 18 daga jihar Kaduna ta yi zarra.

Haka kuma a wannan shekarar an bayyana cewa mata daga ƙasashen Ghana, Kamaru, Nijar da Sudan duk sun fafata a gasar. Haka kuma Hausawa mazauna ƙasar Saudiyya da Italiya su ma sun wasa alƙaluman su a gasar.