29
Oct
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar NSCDC ta bayyana cewa, wani matashi ɗan shekara 22 mai suna Shuaib Idris ya kashe kansa a garin Gwanara da ke ƙaramar hukumar Baruten a Jihar Kwara saboda rashin ƙarfin iya saduwa da mata. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Babawale Afolabi ya sanya wa hannu, kuma aka miƙa wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Ilorin ranar Juma’a. Sanarwar ta ce, ɗaukacin al'ummar da ke zaune a ginin Ankara Wooro, da ke Gwanara, sun shiga cikin makoki a ranar 28 ga watan Oktoba, yayin da aka gano gawar Idris,…
