Editor

9513 Posts
Yadda wani matashi ya sanya kansa a kasuwa

Yadda wani matashi ya sanya kansa a kasuwa

Daga WAKILINMU Wani matashi mai shekara 26 ya sa kansa inda yake neman wanda zai saye shi a Kano. Matashin mai suna Aliyu Na Idris, wanda ɗan asalin Jihar Kaduna ne, yana yawo ne a kan tituna a Kano, ɗauke da kwali da aka rubuta ‘wannan mutumin na sayarwa ne a kan Naira miliyan 20.’ Shi dai Aliyu, wanda ya shafe kimanin kwana biyar yana yawon neman wanda zai saye shi a garin Kano, ya shaida wa manema labarai cewa shi dai a da tela ne, matsin rayuwa ce ta sa yake son sayar da kansa miliyan N20, kuma da…
Read More
An gano mutumin da ya fi kowa tsayin hanci a duniya

An gano mutumin da ya fi kowa tsayin hanci a duniya

Bincike ya sa an gano mutumin da ya fi duka mutanen duniya tsawon hanci, wanda tsawon hancinsa ya kai inci uku da rabi. Shekara 10 ke nan bayan mutumin mai suna Mehmet Ozyurek mai shekara 71 ɗan ƙasar Turkiyya ya fara shiga Kundin Tarihi na Guinness a matsayin wanda ya fi kowa tsawon hanci a shekarar 2010. An fara tabbatar da tsayin hancin Mehmet ne bayan da ya bayyana a shirin wani gidan talabiji na ƙasar Italiya, inda aka gwada tsayin karan hancinsa, inda ya kai kusan santimita 8.8, kamar yadda jaridar The Mirror ta rawaito. Jaridar The Mirror ta…
Read More
Me ya sa Ado Gidan Dabino ya ke mamaye kyautar jarumin jarumai?

Me ya sa Ado Gidan Dabino ya ke mamaye kyautar jarumin jarumai?

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) ba baƙo ba ne a masana'antar Kannywood da kasuwar adabi, domin su ne suka yanke wa Kannywood cibiya. Ya fara da dirama (wasan daɓe) ne tun a shekarar 1984, wato shekaru 37 da suka gabata. A zantawarsa da Wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji yadda Ado Ahmad Gidan Dabino ya lashe kyautar jarumin jarumai har sau uku a shekara ɗaya kuma da fim ɗaya a fim ɗin ɗaya, wato Juyin Sarauta’. Ko a watan Nuwambar da ya gabata (2020), Malam Gidan Dabino (MON) ya samu nasarar lashe…
Read More
Ku zo mu haɗa hannu mu ceci Nijeriya, cewar PDP ga ‘yan Nijeriya

Ku zo mu haɗa hannu mu ceci Nijeriya, cewar PDP ga ‘yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Adamawa kuma shugaban kwamitin shirya babban taron jam'iyyar PDP, Ahmadu Fintiri, ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su zo su haɗa hannu da jam'iyyarsu don karɓe mulkin ƙasa da kuma gyara wa ƙasar zama. Fintiri ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabin maraba da dalaget da jami'an jam'iyya wajen babban taron PDP na 2021 ranar Asabar a Abuja. Yana mai cewa, babban taron nasu shi ne mataki na farko na shirin ceto Nijeriya da jam'iyyarsu ta yi. Ya ce, “Za mu karɓe ƙasarmu kamar yadda muka saba. Ya kamata mu ceto…
Read More
Masu garkuwa sun fito da sabuwar dabarar sanya kayan makaranta don yin garkuwa da ɗalibai

Masu garkuwa sun fito da sabuwar dabarar sanya kayan makaranta don yin garkuwa da ɗalibai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Oyo a ranar Juma'a ta shelanta cewar masu garkuwa da mutane sun fara shigar burtu, suna saka kayan makaranta domin sace ɗalibai a Ibadan, babban birnin jihar. Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da aka raba wa masu ruwa da tsaki a ranar 27 ga Oktoba, 2021, wacce ta fito daga Ofishin Sakataren Dindindin na Ma'aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Jihar Oyo. Takardar wadda aka tura wa Shugabannin Hukumar Ilimi Matakin Farko (SUBEB) da TESCOM da kuma Babban Sakatare na Hukumar BOTAVED, daraktoci da kuma masu sanya ido a harkokin…
Read More
Nijeriya na buƙatar ‘yan sandan jihohi – Obasanjo

Nijeriya na buƙatar ‘yan sandan jihohi – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya yi kira ga gwamnati da ta ƙirƙiro da 'yan sandan jiha a Nijeriya. Obasanjo ya ce Nijeriya na buƙatar 'yan sandan jiha domin magance ƙalubalen tsaron da ke addabar ƙasar. Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa mai taken "Haƙƙin da ke kan al'umma wajen gina ƙasa', a wajen murnar cikar Kulub ɗin Island da ke Legas shekara 78 a ranar Juma'a. Tsohon shugaban ƙasar ya ce wuraren da ba su fama da tashe-tashen hankula ne kawai ke da tabbaci da…
Read More
Ya dace a ƙarfafa gwiwar masu aikin alheri?

Ya dace a ƙarfafa gwiwar masu aikin alheri?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Masu hikimar magana na cewa, yaba kyauta tukwici. Ma'ana, idan har ka ji daɗin kyautatawar da aka yi maka, ko wani alheri da aka aiko maka to, yana da kyau ka bai wa wanda ya aikata ko ya yi sanadin sada ka da wannan alheri, wani abin tukwici ko wata kyauta da shi ma zai ji daɗi. Yabawa ko da ta fatar baki ce tana da daɗi kuma tana ƙara ƙarfafa gwiwar wanda aka yi wa, don ya sake dagewa ya yi aikin da ya dace wanda kuma zai jawo masa yabo. Hatta a koyarwar addini…
Read More
Shirin kai hari: Yadda `yan bindiga suka gargarɗi sojoji da su bar ƙauyen Miango

Shirin kai hari: Yadda `yan bindiga suka gargarɗi sojoji da su bar ƙauyen Miango

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsagerun 'yan bindiga sun shaida wa Sojojin Nijeriya da ke aikin samar da tsaro a ƙauyen Miango da ke cikin Ƙaramar Hukumar Bassa, Jihar Filato, cewa su bar yankin domin za su sake kai wani hari kan 'yan ƙauyen. Kwanan nan ne dai aka girke sojoji yankin bayan rahoton wani hari da 'yan bindiga suka kai a kauyen na Miango. Rundunar soji wadda ke aiki ƙarƙashin Rundunar Safe Haven, a watanni biyu da suka gabata ta ce ta yi ƙoƙarin dakatar da maharan ga afka wa 'yan ƙauyen. Wasu shaidun gani da ido waɗanda…
Read More
Da alamu matar Cristiano Ronaldo ta harbu

Da alamu matar Cristiano Ronaldo ta harbu

Fostin ɗin da ɗan wasa Cristiano Ronaldo ya wallafa a shafinsa na Instagram na cewa matarsa ta samu 'juna biyu. Wannan shi ne fostin na farko da wani ɗan wasa a duniya ya samu mabiya (Likes) mutum miliyan 27 da dubu ɗari ɗaya, kuma yana ci gaba da ƙaruwa ahalin yanzu ashafin Instagram. Ba a iya ƙwallon ƙafa ba, a kowane irin wasa a duniya babu wani ɗan wasa da ya taɓa samun yawan mabiya da suka kai na waɗanda suka bibiyi fostin ɗin na Cristiano Ronaldo wanda ya wallafa a jiya tare da shi da matarsa Georgina.
Read More
Gargaɗin Buhari: Ku daina min bambaɗancin tazarce

Gargaɗin Buhari: Ku daina min bambaɗancin tazarce

Daga SANI AHMAD GIWA Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gargaɗi masu yekuwar kamfen ɗin tazarcensa bayan 2023 da su daina kuma su shiga taitayin su, domin babu haka a tsarin sa. ”Da Alƙur’ani na yi rantsuwa kuma shekara huɗu sau biyu duka sai da na yi rantsuwa cewa iya shekarun da zan yi kenan, saboda haka kada wani ya bijiro da abinda ba shi cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan. Ba zan lamunce wa duk wanda ya bijiro da haka ba.” A cikin takardar wadda Kakakin Fadar Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana cewa Shugaba…
Read More