Editor

9513 Posts
Taron PDP: Muna da damar daidaita Nijeriya – Atiku

Taron PDP: Muna da damar daidaita Nijeriya – Atiku

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a Abuja ya buƙaci ɗaukacin 'yan Nijeriya da su yi amfani da damar da jam’iyyar PDP ta bayar wajen daidaita Nijeriya da ceto ƙasar daga halin da ta ke ciki. Atiku ya ba da wannan cajin ne ga wakilai da jami'an jam'iyyar a babban taron jam'iyyar PDP na 2021. A cewarsa, akwai bambance-bambance da dama, amma 'yan Nijeriya za su iya cimma komai idan suka ajiye saɓanin da ke tsakaninsu a gefe. Ya ƙara da cewa, taron wata dama ce ta yanke…
Read More
Me ya sa Jonathan ya zille wa babban taron PDP?

Me ya sa Jonathan ya zille wa babban taron PDP?

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Mista Goodluck Ebele Jonathan, wanda ɗa ne ga jam'iyyar adawa ta PDP, ana zargin shi da zille wa babban taron da jam'iyyar ta gudanar a jiya Asabar a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Ranar Juma'a kwana ɗaya kafin babban taron na jam'iyyar PDP, Jonathan ya bayyana cewa zai bar Abuja zuwa Nairobi, Ƙasar Kenya domin halartar taron Ƙungiyar Haɗin Kan Afrika akan bunƙasa zaman lafiya, tsaro da kuma cigaban yankin. Sai dai kuma, wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar PDP sun yi amannar cewa Jonathan ya ƙirƙiri tafiyar ne kawai a daidai…
Read More
Jami’ar Nasarawa ta rantsar da sabbin ɗalibai 6,323

Jami’ar Nasarawa ta rantsar da sabbin ɗalibai 6,323

Daga BASHIR ISAH Mataimakin shugaban Jami'ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK), Farfesa Suleiman Bala Mohammed, ya yi kira ga sabbin ɗaliban da suka samu gurbin karatu a jami'ar da su kasance masu ɗa'a a kowane lokaci saboda a cewarsa, jami'ar ba za ta lamunci kowane nau'i na rashin ɗa'a ba. Farfesa Suleiman ya wannan kira ne a wajen bikin rantsar da sabbin ɗalibai su 6,323 na shekarar karatu 2020/2021 da jami'ar ta shirya ta kuma gudanar a dandalin taron yaye ɗalibai a Juma'ar da ta gabata. Jagoran ya kuma gargaɗi ɗaliban da su ƙaurace wa mu'amala da ƙungiyoyin asiri…
Read More
Ƙasungumin mai safarar hodar Ibilis na duniya ya shiga hannu a Colombia

Ƙasungumin mai safarar hodar Ibilis na duniya ya shiga hannu a Colombia

Jami’an tsaron Colombia sun samu nasarar cafke ƙasungumin mai fataucin muggan wayoyi mafi shahara da aka fi sani da Otoneil, wanda suka daɗe suna farautarsa, la’akari da cewar a halin yanzu shi ke kan gaba wajen safarar hodar iblis a duniya. Hukumomin tsaro sun ce an kama Otoniel da asalin sunansa shi ne Dairo Antonio Usuga, a kusa da ɗaya daga cikin manyan ofisoshinsa a yankin Necocli, dake kusa da kan iyaka da Panama. Sojoji aƙalla 500 tare da jirage masu saukar ungulu 22 gami da taimakon hukumomin tsaron Ingila da Amurka ne suka kai samamen da ya basu nasarar…
Read More
Sanatocin Brazil sun nemi kotu ta dakatar da Bolsonaro daga kafafen zumunta

Sanatocin Brazil sun nemi kotu ta dakatar da Bolsonaro daga kafafen zumunta

Wani kwamitin Majalisar Dattijan Brazil dake bincike kan matakan da gwamnatin ƙasar ta ɗauka wajen yaƙi da annobar Korona, ya buƙaci kotun ƙolin ƙasar da babban mai gabatar da ƙara, da su rufe shafukan shugaba Jair Bolsonaro na kafofin sadarwar zamani, saboda samunsa da laifin yin ƙarya wajen alaƙanta rigakafin Koronar da kuma kamuwa da cutar Sida. Cikin buƙatar da suka mika ‘Yan majalisar Dattijan sun buƙaci kotun ƙoli da ta dakatar da shugaba Bolsonaro daga amfani da kafofin sadarwar zamanin da suka haɗa da 'YouTube' da 'Twitter' da 'Facebook' da kuma 'Instagram', bayan da bincike ya bankaɗo cewar shugaban…
Read More
Amurka ta dakatar da kamfanonin Chana

Amurka ta dakatar da kamfanonin Chana

Amurka ta dakatar da kamfanonin sarrafa wayoyi da sauran harkokin sadarwa na Chana da ke aiki a ƙasar, lamarin da ake ganin ba ya rasa nasaba da rikicin kasuwanci da gwada ƙarfin tattalin arziki a tsakanin ƙasashen biyu. A cewar hukumomin Amurkan, sun yanke wannan shawara ce saboda ƙara inganta tsaro a Amurka musamman a rumbunan adana bayananta da ke fuskantar barazana daga Chana. Amurka dai ta bai wa Hukumar Kula da Sadarwar Chana umarnin tabbatar da ficewar duk wasu kamfanonin da ke da alaƙa da samar da wayoyyi ko sadarwa da ke Amurkan cikin kwanaki 60, abin da ya…
Read More
Chana ta ɓullo da sabon tsarin rage hayaƙi mai guba

Chana ta ɓullo da sabon tsarin rage hayaƙi mai guba

Ƙasar Chana ta duƙufa wajen rage fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli ta hanyar inganta makamashi mai sabantuwa na zamani nan da shekara ta 2030 kamar yadda Majalisar Ministocin ƙasar ta sanar. Sabon matakin tamkar nanata ƙudirin da Chana ke son cimma ne na daidaita ƙarfin iska da na rana zuwa gigawat 1,200 nan da shekaru 10 masu zuwa domin gina ƙarin cibiyoyin samar da wutar lantarki da nukiliya. Waɗannan bayanai da Chana ta fitar na zuwa ne kwanaki ƙalilan gabanin fara babban taron sauyin yanayi a birnin Glasgow da aka shirya domin ƙarfafa wa ƙasashen duniya gwiwa wajen yaƙi…
Read More
Duniyar marubutan Hausa ta girgiza bisa rasuwar Marubuci Bello M. Bello

Duniyar marubutan Hausa ta girgiza bisa rasuwar Marubuci Bello M. Bello

Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano Fitaccen matashin marubucin littattafai da fina-finan Hausa, kuma jarumi a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, wato Bello M. Bello ya koma ga Mahaliccinsa a daren Talatar da ta gabata (26, 10, 2021). Marigayi Bello M. Bello ya rasu ne a dalilin ciwon ciki da ya kama shi jim ka]an bayan ya yi sallar Magriba, kuma nan take, ya ce ga garinku nan. Ya rasu a gidansa dake cikin garin Ringim ɗin jahar Jigawa, kuma an yi jana'izarsa a washegari ranar Laraba 27, 10, 2021 da misalin ƙarfe takwas na safe. Marigayi Bello M. Bello,…
Read More
Coca-Cola da Pepsi sun fi gurɓata muhalli a Duniya – Bincike

Coca-Cola da Pepsi sun fi gurɓata muhalli a Duniya – Bincike

Wani rahoton ƙwararru ya bayyana kamfanin lemun kwalba na Coca-Cola a matsayin wanda ya fi gurɓata muhalli a duniya, inda takwaransa na Pepsi ke biye da shi. Rahoto ya gano cewa, robobin da waɗannan kamfanoni ke zuba lemunsu a ciki, sun karaɗe sassa da dama na duniya a matsayin shara. A yayin tattara alƙaluman binciken, sama da mutane 11,000 suka sadaukar da kansu a ƙasashen duniya 45 wajen aikin tsaftace gaɓar tekuna tare da kwashe tarin sharar robobin da waɗannan kamfanoni ke samarwa. Wasu bayanai na cewa, an tattara sharar robobi sama da 330,000 bayan an yi amfani da su…
Read More
Fusatattun jama’ar gari sun sheƙe ɗan leƙen asirin ’yan bindiga a Kaduna

Fusatattun jama’ar gari sun sheƙe ɗan leƙen asirin ’yan bindiga a Kaduna

Daga WAKILINMU Wasu fusatattun mutane sun kashe wani mutum da matarsa da ɗansa a unguwar Zangon Aya da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna bisa zargin bada bayanai ga ’yan bindiga. Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin. Samuel Aruwan, kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna, ya bayyana a ranar Talata cewa, hukumomin tsaro sun kai rahoton kisan ga gwamnatin jihar. Rahoton ya ce, an kashe Abdullahi Mohammed Gobirawa da matarsa Binta Abdullahi da ɗansa Hassan Abdullahi…
Read More